Yadda India ta sauya harshen Turanci

Suna nan a ciki, to amma ba kasafai ake lura da su ba. Kalmomin da suka zama wani bangare na turancin da ake yi yau da kullum;

Loot da nirvana da pyjamas da shampoo da shawl da bungalow da jungle da pundit da thug.

Menene asali da hanyoyin wadannan kalmomi na India.

Ta yaya kuma da wana lokaci suka yi wannan tattaki, suka shiga harshen Birtaniya sannan suka kutsa kamus din turanci na Oxford, da ke fada mana dangantakar Birtaniya da India?

Tun kafin mulkin mallakar Birtaniya a Indiya, kafin kamfanin East Indiya ya mallaki yankinsa na farko a India a 1615, kalmominKudancin Asiya daga harsunan da suka hada da Hindi da Urdu da Malayalam da kuma Tamil, sun yi

kutse a cikin harsuna na waje.

Wani fitaccen littafin kamus ya tattara bayanan tarihin asalin kalmomin Indiya na turanci, wadanda wasu masu sha'awar harkokin India suka wallafa.

Wadannan mutane su ne Henry Yule da Arthur C Burnell, kuma sunan littafin shi ne, Hobson-Jobson: The Definitive Glossary of British India, wanda aka wallafa a 1886.

Sha'irin nan ko mawaki Daljit Nagra ya bayyana littafin da cewa, ''ba wani kamus ba ne mai tsari na a-zo-a-gani illa dai kawai littafi ne na abubuwan da suka kunshi tarihin lokacin mulkin mallaka na India. Kamar wani baturen

Ingila na daban a tsarin kamus din kalmomi.''

Editan sabon littafin na yanzu, wanda aka wallafa kwanan nan ya bayyana yawan kalmomin da suke nan tun kafin mulkin mallaka na Birtaniya.

''Ginger da pepper da Indigo sun shiga harshen turanci ne ta hanyoyin da na kakanni; inda suka nuna alakar kasuwanci ta da tsakanin Indiya da Girkawa da kuma Rumawa kuma daga nan suka samu shiga ta harshen Girka da

Latin zuwa cikin Ingilishi.'' Inji Kate Teltscher.

''kalmar Ginger ta samo asali ne daga harshen Malayalam wanda ake yi a jihar kudancin Indiya ta Kerala ta biyo ta harshen Girka da Latin ta ratso ta harshen Faransanci na da da kuma Turanci na da, kuma daga nan ne kalmar

da itacen suka zama abubuwa na duniya baki daya.

A karni na 15 ne aka shigar da itacen yankin Karebiya da Afrika, daga nan su ma suka fara samar da shi kuma ya zama ya watsu a duniya.''

Tun lokacin da kasuwanci tsakanin kasashe ko dauloli ya fadada ta hanyar mulkin mallakar Turawa da suka yi wa yankunan Kudanci da Kudu maso Gabashin Asiya kutse ko shigar kalmomin Indiya a cikin Turanci ya kankama.

Da yawa daga cikinsu sun shigo ne ta hanyar Turawan Portugal.

''Tun a lokacin karni na 16 ne turawan Portugal suka kama Goa, kuma kalmomin mango da curry sun zo mana ne ta hanyar turawan Portugal.

Da farko kalmar mongo ta shigo turancin Portugal ne da sunan mangai da harshen Malayalam da Tamil sannan ta kare da wasalin 'o' a turancin Ingilishi.'' In ji Kate.

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES

Kalmar bungalow ta samo asali ne daga harshen Indiya inda ake kiranta 'banga'(CREDIT ALAMY1)

To sai dai kuma kwararar kalmomin kasashen Kudancin Asiya zuwa harshen Ingilishi ba a ko da yaushe suke biyo hanyar al'adar da aka saba gani ba ta Gabas zuwa Yamma, kamar yadda Teltscher ta nuna inda ta yi misali da kalmar 'ayah'.

Ta ce, '' kalmar 'ayah' kalma ce da san tana nufinmai reno a Indiya ko mai aikin gida kamar yadda wasu daga cikin dangina da suke Delhi suke amfani da ita a yau.''

ta kara bayani da cewa, '' Ayah ta samo asali ne daga turancin Portugal, inda take nufin ma'aikaciyar jinya ko matar da aka dauka aikin koyar da yara, kuma da haka mutanen Portugal da suke Indiya suke amfani da ita, wanda ta

haka ne su kuma mutanen Indiya suka dauki kalmar.

Daga Indiyancin ne kuma wannan kalma ta shiga Ingilishi''

Kamus na Hobson-Jobson ya bayyana wata irin tafiya ta daban da kalmar 'chilli', wadda sananniyar kalma ce, a Ingilishin Indiya da ke nufin barkono, ta yi.

Kamar yadda marubuta littafin Yule da Burnell suka bayyana a kamus din inda suka ce, '' akwai dan shakku kadan cewa wannan suna an samo shi daga kasar Chile da ke Latin Amurka lokacin da aka kai shukar tsibiran Indiya

daga nan kuma aka kai ta Indiyan.''

Kalmomin Indiya da Urdu da Tamil da Malayalam da na turancin Portugal da kuma Ingilishi sunyi yawo a duniya a karni na 16 da 17, wanda hakan ya nuna yadda harsuna suke sauyawa kamar yadda al'ada take samuwa ta kuma sauya su ma mutane suke sabawa da yanayin wurin da suka samu kansu.

Kalmomi uku da suka bayyana wannan misali su ne shawl da cashmer da patchouli, wadanda suka yi tafiya tare daga Indiya zuwa harshen Ingilishi na karni na 18.

''Cashmere kalma ce da muke dangantawa da wul (wool a turanci) kuma ta samo asali ne daga Kashmir kuma akuyoyin Kashmir ne suke samar da wul din.

Wannan kalma tana da kusanci da 'shawl' wadda ita kuma kalma ce da ta samo asali daga harshen mutanen Iran na Pasha kuma ta shiga Indiya ta hanyar harshen Urdu da Indiyanci daga nan kuma ta shiga Ingilishi,'' kamar yadda Telscher ta yi bayani.

Hakkin mallakar hoto AP

Ma'aikatan kamfanin East India su ne suka mayar da shawl Birtaniya Shawl ya shigo Ingila ne a karni na 18 da 19 saboda mayafi ne da mata masu hali suke jin dadinsa.

Idan kina da dan uwa da yake aiki a kamfanin East India sai ki sa ya aiko miki da shawl mai kyau.

Patchouli yana da dangantaka da shawl, saboda ana amfani da turaren domin maganin warin ruma a lokacin da ake safarar shawl daga Indiya zuwa Birtaniya.Saboda haka shi ma ya yi suna a Birtaniyan.'' kamar yadda ta kara bayani.

Telscher ta ce, ''to sai dai shi kuma Patchouli bai yi karko ba domin, yayin da karni na 19 ya shigo sai patchouli ya zama abu ne da ke dangantawa da batattun mata na Faransa da kuma karuwai.

Daga nan ne sai patchouli ya zama daga turaren masu matsayi zuwa na gama-gari kuma zuwa shekarun 1960 sai ake danganta shi da matasa 'yan bana-bakwai.''

Marubuci Nikesh Shukla haifaffen Landan wand ke zaune a Bristol, yana ganin gagarumar gudunmawar da Indiya ta bai wa turancin Ingilishi alama ce ta cudanni-in-cude-ka na daula.

''A sakamakon mulkin mallaka ne Birtaniya ta dauki al'adar mutanen da ta mulka kuma ya yi tasiri sosai saboda mulkin mallaka yana bin hanya biyu ne.

Ka duba abubuwan da ke cikin ala'adar Birtaniya da suka samo asali daga kasashen da ta rena, wadanda Birtaniyan ke cewa nata ne kamar tea( shayi) kuma harshe na daga irin wadannan abubuwa shi ma,'' inji marubucin.

Shukla, wanda littafinsa na kwanan nan mai suna Meatspace ya yi nazari kan hanyoyin sada zumunta da muhawara na intanet da wayoyin komai-da-ruwanka yana ganin daula ta bunkasa turancin Ingilishi kamar yadda fasaha take yi a yanzu.

Ya ce, ''hanya daya da zaka gane haka ita ce, yadda wadannan kalmomin Indiya su ka yi wa turanci katsa-landan saboda babu su a turancin, misali 'veranda da pyjamas', ya ce.

Marubucin ya kara da cea,'' a yau kalmomi irin su wifi da inaternet da Google da email da selfie sun zama kalmomi na duniya, babu wasu kalmomi a madadinsu a don haka sun yi wa turancin Ingilishi da sauran harsuna na duniya kutse.

Shafukan sada zumunta da muhawara suma sun sauya yadda muke magana, misali kalmar 'like' ta turanci yanzu ta sauya daga ma'anarta haka kalmar 'following' ko 'lol'.

Sabon abin da yake dagulawa turanci lissafi yanzu shi ne ci gaban fasaha, amma na ji dadin yadda daula ta kasance babbar abar da ta dagulawa turancin Ingilishi lissafi ta hanyar cusawa Birtaniya al'adu da harsuna da yawa,'' Ya kara da cewa.

Kalmar Indiya ta Ingilishi wadda Shukla ya fi so, wato 'blighty' tana nuna yadda harshe yake saurin sauyawa.

Da farko turawan Birtaniya ne da ke Indiya suke amfani da ita inda suke nufin Birtaniya kamar a 'good ol' Blighty'.

To amma kalma ce da ta samo asali daga harshen Urdu wadda suke cewa 'vilayati' wadda ke nufin dan kasar waje ko Bature.

Daga nan aka sauya mata ma'ana ta zama turawan Birtaniya na amfani da ita a ma'anar girmamawa a bainar jama'a har a karshe ta zama ta turancin Ingilishi.'' Inji Shukla.

Tasirin harshen Indiya a turancin Ingilishi ya nuna yadda harshe yake tafiya a ko da yaushe, kuma hakan ya nuna muhimmanci da amfanin tsoffin yankunan mulkin mallaka wajen samar da sabuwar duniyar yau.

Telscher ya ce,'' abin ban sha'awa ne ka kalli yadda kalmomi suke, za ka ga yadda wannan amo na kalmomi da ba a yi tsammani ba da kuma hanyar da suka bi da alakar da ta samu atsakani.''