Wuraren da dole a sa lakataye da wadanda ba a sa wa

Hakkin mallakar hoto PA

Sanya lakataye abu ne da yake al'ada a yanayin sa tufafi na bature, wannan ya sa za ka ga idan mutum bai sa shi ba idan ya sa kwat sai abin ya zama banbarakwai.

Watakila wannan shi ya sa wasu wurare suke tilasta wa duk wanda zai shige su ya zama yana sanye da shi a kan kwat dinsa a Birtaniya

Sai dai duk yadda wannan dan zirin kyalle yake da muhimmanci a al'adar sanya tufafin bature wasu wuraren sun haramta sa shi.

Wasu rahotanni sun nuna cewa an hana direban motar tsere Lewis Hamilton shiga benen manyan baki na filin wasa na Wimbledon da ke Ingila wanda ake kira Royal Box, saboda ba ya sanye da lakataye. To ina masu rajin sai an sa lakataye ? Tambayar da Gareth Rubin yayi ke nan.

Mataimakin editan mujallar maza ta GQ Bill Prince, ya ce, ba laifin Hamilton ba ne, bai san dokokin wurin ba ne. Ya ce, ''lakataye shi ne cikammakin adon mutum kamar yadda al'ada take. To amma yadda al'ada ta sauya ake sa

kaya yadda aka ga dama, hakan ya sauya tsarin sa tufafi wanda hakan ke jawowa wanda yake son sanya wa rudadi. Saboda haka ka'idoji sun kawar da duk wani shakku suka kuma tabbatar da tsari.''

Patrick Murphy kuwa ya ce ba wai magana ce tabbatr da tsari ba kawai, idan ka yi ado da kwat ba ka sa lakataye ba abin zai zama ba tsari. Ya kara da cewa, ''idan ka tambaye ni kan wanda ya sa kwat bai sa lakataye ba zan ce maka, ai wannan bai gama sa tufafinsa ba.''

Wasu mutanen suna ganin sanya wannan dan zirin kyalle a wuyan mutum wani abu ne na da ya zama tsohon yayi, amma kuma akwai wuraren da sai lalle mutum ya sa lakatayen kafin a barshi ya shiga wurin.

Sai dai kuma akwai wuraren da su kuma suka hana mutane sanya lakatayen din ko mutum yana son sa wa ko baya so.

Ga wurare biyar da dole sai ka sa lakataye:

1.Otal din Ritz na Landan. Idan har kana son ka je wannan otal wanda wuri ne da masu hali da 'yan jinin sarauta da masu yawan bude idanu ke zuwa , kana bukatar ka sa lakataye. Kamar yadda Jackie McDevitt na Otal din ya

ce: '' Ginin da ya ke bangaren wurin shakatawa na Palm Court, gini ne mai ban sha'awa irin na zamanin Sarki Louis na 16 na Faransa kuma bakinmu suna sha'awar su sanya tufafi masu kyau domin su dace da wurin.''

2. P&O Cruise: Dole ne mutum ya sa kwat da lakataye a lokacin liyafa a wannan wurin wanda kamfani ne da ke daukar masu zuwa hutu zuwa fitattun wurare na shakatawa a sassan duniya. Kamfanin yana Carnival House ne da ke Southampton, a Ingila.

3. Makaranta: Dole ne mutum ya sa lakataye idan yana makarantar 'ya'yan masu hali a Birtaniya.

4. Sashen 'yan jarida na Majalisar Wakilai ta Birtaniya: An tsara yadda 'yan jarida maza za su sa tufafinsu a wannan wuri ya zamanto ya nuna girmamawa da mutunta majalisar a don haka dole ne namiji ya sa lakataye idan yana wurin.

5. Filin wasan kwallon kirket na Marylebone: Duk mazan da za su je kallo a wannan fili a ranar da ake karawa tsakanin kungiyoyi dole ne su sa lakataye kafin a bar su su zauna a benen da manyan baki suke. Sai dai manyan

Hakkin mallakar hoto Getty

bakin da suke sanye da tufafi na kasar wato jesi ko kumamasu kayan sarki, to su wadannan ba dole ba ne.

Wuraren da ba a sa lakataye:

1. Kamfanin Richard Branson. Idan kana aiki a wani daga cikin kamfanonin Richard Branson, hamshakin dan kasuwar nan na Birtaniya mai kamfanin sufurin jirgin sama na Virgin, to ka da ma ka fara sa lakataye sai dai idan kana

son wata rana kawai ka gan shi ya zo ya kama lakataye na naka ya yanke da almakashi.

Ya taba rubutawa cewa, ''na tabbata ana amfani da su ne saboda bayan an rika tilasta wa shugabannin wuraren aiki sanya su, shi ne su ma suke son su yada al'adar zuwa 'yan baya.''

2. Likitoci. Idan likita ne kai ba ka sa lakataye a lokacin da kake aiki, domin an dauke shi tamkar wani abu ne da kwayoyin cuta ke taruwa a jikinsa. Kamar yadda dokokin kula da lafiya na Birtaniya suka nuna lakataye abu ne da

mutum yake sa wa kusan kullum, amma kuma ba kasafai yake wanke shi ba. Kuma ga shi ba wani amfani da yake yi wajen yi wa maras lafiya magani kuma an lura matattara ce ta kwayoyin cuta.

3. 'Yan sanda. Za a ga kamar 'yan sanda suna sanye da lakataye to amma a zahiri ba shi ba ne. A birtaniya 'yan sanda ba sa amfani da lakataye a kayansu domin hadari ne a wurinsu musamman idan rikici ya hada su da wani mai laifi, domin zai iya shake su.

4. Wurin shakatawa na masu zaman kansu. Wurin shakatawa kamar otal da makamancinsa na wasu mutane daban da ba kowa ba ne yake zuwa ba sai su kadai da kuma wanda suka gayyata. Irn wadannan wurare da ake kira

a turance, 'Soho House', suna da tsarin sanya tufafinsu, inda ba sa sa lakataye domin sun dauka wani salon kaya ne na da, su kuma suna nuna cewa su wurinsu ba wuri ba ne shakatawa na mutane masu ra'ayin da.

5. Masana'anta. Duk wata masana'anta da take da na'urori da za su iya cafkar kayan mutum, ba a sa lakataye. A Birtaniya dokokin irin wadannan wurare ba wai sun ambaci lakataye ba ne karara amma duk wata tufa ko kaya da

mutum zai sa da ba ta kama jiki ba, wadda na'ura za ta iya kama wa abu ne da aka hana sa wa.

Hakkin mallakar hoto PA

A da za ka ga an yi wurin rataye lakataye a kowana babban titi da tashoshi da filin jirgin sama, to amma tun da har firaministocin jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya (kwanzabatib) suka fara tafiya ba lakataye kasan cewa

wannan al'ada ta shekarun 1980 ta Birtaniya ta kau.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Five places that still demand ties, and five that ban them