Sauraren maganar biri

Hakkin mallakar hoto ALAMY

kamannin mutum da biri abu ne da ya dade yana kayatar da masana kimiyya.Duk da haka Mary Colwell kamar yadda ta rubuta abu ne mai ban sha'awa.

Charlotte Uhlenbroek masaniya a kan dabbobi ta ce, ''idan ka kalli idanuwan biri, za ka ga dabba mai basira da ta san kanta kai ma ta kura ma ido tana kuma nazari a kanka.''

Uhlenbroek, wadda ta yi shekaru tana nazartar rayuwar birrai a muhallinsu, ta kara da cewa,'' Sau da yawa ina mamakin yadda birrai suke daukarmu idan suka kalle mu.''

Birrai da mutane suna da kama sosai kusan a ce abu ne mai wuya a iya cewa ga abin da ya raba mu da halitta mafi kusanci da mu a bayan kasa.

''Babu wata dabba da ke ba wa mai kallonta sha'awa kamar yadda wadannan 'yan kananan halittu da ke da alaka da dan adam.'' Kamar yadda R L Garner ya rubuta a 1896.

A gaskiya ma garner yana daya daga cikin mutanen da suka yi kokarin gano banbancin da ke tsakanin mutane da birrai ta hanyar zama ya rayuwa da birrai a Afrika ta Yamma.

Mai binciken ya lura da kamannin halittun na siffa da mu'amullarsu da yanayinsu na murna ko bakin ciki da kuma yadda suke kula da 'ya'yansu.

A duk wannan bincike na shi, abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda birran ke magana da junansu. Da alamu suna magana da junansu to amma abin shi ne me suke cewa kuma me ya sa?

''Karan da wadannan birrai suke yi ya kunshi duk wasu abubuwa na harshe ko yare.'' Inji Garner kamar yadda ya rubuta

''Mai magana ko yin karan yana sane da ma'anar karan da yake yi, kuma yana yin sa ne da nufin aikawa da wani sako zuwa wajen wanda yake yi wa;

Ba shakka yana magana ne da wani idan ka ji yayi karan kuma za ka ga yana kallon wanda yake yi wa maganar idan ya yi.

Zai rage amo ko karan muryar domin ya dace da yanayin da yake amfani da shi, domin ya san amfanin kara ko sauti a matsayin wata hanya ta sadarwar tunani.

Wadannan da sauran dalilai sun nuna cewa sautin da birrai ke yi ba komai ba ne illa magana ta sosai kamar yadda dan adam ke yi''

Hakkin mallakar hoto SCIENCE PHOTO LIBRARY

A ranar 1 ga watan Yuni na 1698 sanannen masanin halittar jikin dan adam din nan na lokacin Edward Tyson ya gabatar da gawar wani dan karamin gwaggon biri da ya fede.

Shi dai gwaggon birin an kawo shi Ingila ne daga Angola, wanda ya kamu da cuta bayan wata biyu da kai shi Ingilan, sakamakon ciwon da ya ji a mukamukinsa lokacion da ya fadi a cikin jirgin ruwan da aka dauko shi daga Afrika.

Masanin ya rubuta bayanan abubuwan da ya gano a jikin halittar gwaggon birin a littafinsa mai suna Orang-Outang, sive Homo Slvestris.

Daga gwaje-gwaje da bayanan da ya bayar na tsoka da kashin birin, abin sosa zuciya shi ne bayanin da ya yi na yadda ma'aikatan jirgin ruwan suka kula da dan birin.

Sun sa mi shi kaya kamar na mutum suka rika ba shi abinci da ya rika ci a tebur kamar yadda sauran mutane ke yi, har da kwantar da shi a gado ''.

Wanna dabba ce da ta ba ma'aikatan jirgin sha'awa kamar mutum. Su ma kamar mu sun dauki wannan halitta da ke da kusanci da dan-adam suka yi tunanin muhimmancin kasancewarsu na mutane.

Wani abu mafi ban sha'awa daga cikin abubuwan da masanin ya gano shi ne yadda jijiyoyin furta sauti na birin su ke.

Tyson ya gano bambancin da ke tsakanin makogaron birin da namu(mutane) dan kadan ne.

Ya ce, ''wannan ai kamar yadda na mutum yake. To me ya sa ba ya magana?

Wata amasa da ake bayarwa akan wannan tambaya ita ce, idan birrai suka yi magana kamarmu to za mu bautar da su, saboda haka ne suke shiru a cikin mutane .

Yadda muke daukar birrai abu ne da ya samo asali tsawon lokaci wanda kuma yake da alaka da falsafa da addini da kuma kimiyya.

Hakkin mallakar hoto SCIENCE PHOTO LIBRARY

A karni na 17 katangar da ke tsakanin kimiyya da hikaya da kuma addini 'yar siririya ce.Dabba ba kawai wata halitta ba ce da za a ba da bayani a kanta ba, wata halitta ce kawai da tke karin haske a kan yadda duniyarmu ta ke da kuma yadda wurin da muke a duniyar.

A fahimtar Tyson, abin da ya sa birrai ba sa magana kamar mutane, shi ne saboda su ba halittu ba ne masu tunani kamar mutum.

Erica Fudge na Jami'ar Strathclyde, ya ce, ''mutane suna da bambanci da dabbobi saboda muna da abin da ake kira tunani, wanda abu ne da ba za ka taba samu a jiki ba, abu ne da ruhi, saboda haka kasancewar biri yana da makogaro kamar na mutum hakan kadai ba zai ba shi damar magana kamar mutum ba, kuma rashin maganar tasa shi ya kara tabbatar da matsayin mutum a matsayin halitta mai tunani.''

To sai dai kuma a wurin masana kimiyya na yau,dalilin da aka bayar na ruhi da dan-adam yake da shi wanda ya sa yake magana wadda sauran halittu ko dabbobi ba sa yi kamar biri, ba abu ne da za su yarda da shi ba, to amma duk

da haka muna da kuduri daya ne, na gano kusanci da kamanninmu da birrai.

Saboda haka ne muka karkata wajen harshe ko magana domin samo wadannan amsoshi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

R L Garner, shi ne na farko da ya yi kokarin koya wa biri magana sai dai nasarar da ya samu ba ta taka kara ta karya ba.

Sauran binciken da aka gudanar sun nuna cewa nau'in biri daban daban kama daga tsula da gwaggon biri da sauransu suna iya sadarwa a tsakaninsu amma ba ta hanya iri daya ba.

Shekaru 70 da suka wuce an yi kokarin koyar da birrai yadda za su rika magana da Turanci, ta hanyar hada biri sabuwar haihuwa da jariri shi ma sabuwar haihuwa aka rene su tare a gida daya.

A lokacin da suka kai shekara uku, dan birin ya fi na mutum karfin yin abubuwa,amma kuma ba ya iya furta kalmomi sosai, yayin da shi kuma dan mutum ya iya furta kalmomi da yawa.

Daga nan ne aka gano cewa a zahiri baki da makogaron biri ba za su iya yin sauti ba kamar yadda mu mutane muke yi da namu.

Wannan ya bude wani sabon babi na bincike a fagen koyar da magana irin ta kurame.

A karnin da ya wuce an samu sauyi a dangantakarmu da birrai kan yadda muke daukarsu daga namun daji zuwa dabbobin da ke da basira da kuma suke iya sadarwa.

Har yanzu yadda birrai ke magana da junansu abu ne da har yanzu ba a iya ganowa ba, amma har yanzu ba mu gaji da yadda muke kokarin sanin yadda muke da kusanci da su ba.

Idan kana son karan wannana a harshen Ingilishi latsa nan Listening to the language of apes