Sauyin halitta : Me ya sa idanuwanka suke a gaba?

Hakkin mallakar hoto Getty

Me ya sa idanuwanmu ba a gefen kanmu suke ba? Jason Goldman ya duba dalilin hakan. Ka yi tattaki zuwa gidan namun daji, idan ka lura da kyau, za ka iya ganin yawancin dabbobin sun kasu kashi biyu.

Akwai wadanda idanuwansu suke a gefen kansu, kamar su kaji da shanu da dawakai da jakin dawa.

Sannan kuma akwai wadanda idanuwansu suke a fuskarsu, kusa da kusa, kamar birrai da damisa da mujiya da kura.

Haka su ma dukkanin mutanen da suke ziyarar gidan idanuwansu kamar na wannan rukunin na dabbobi suke wato a gaba ba gefe ba. To wai me ya sa haka?

Idan ana maganar inda ido yake a jikin dabba ko mutum ne to akwai tsarin taimakekeniya ko hada karfi da karfe wuri daya.

Idanuwan da suke fuska idan suka kalli gaba kowanne siffar da ya kalla za ta tafi wajen dayan ne, ma'ana za su yi musayar hoton da kowanne ya dauko, su mika wa kwakwalwa, wanda wannan shi ke sa mutum ya san zurfin da yake gabansa.

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

Dabbobin da idanuwansu suke gefe ba lalle su samu wannan damar ba ta sanin zurfin da ke gabansu, to amma su kuma a nasu bangaren suna da damar ganin fadin fili sosai maimakon zurfin. Kunkuru idanuwansa suna gefe ne amma kuma yana iya gani ko sarrafa siffar abin da ya gani kamar idonsa yana gaba ne.

Inda halittar ido take a jikin dabba watakila ta kasance ne saboda dalilai da dama a wurin dabbobin.

Kunkurun da yake da ido a gefe kuma yake iya amfani da idon kamar dabbar da take da ido a fuskarta, ana ganin yana da wannan tsari ne watakila saboda idan ya mayar da kansa ciki ya boye, idanuwan nasa za su iya ganin haske ne kawai daga gaba kamar a ce idon a gaba yake.

To amma yaya halittar mutum ita kuma take da idonta a gaba wato a fuska? Akwai bayanai da dama da ake ganin suka sa hakan.

A shekarar 1922 wani masanin kimiyya dan Birtaniya, mai suna Edward Treacher Collins ya rubuta cewa, nau'in halittar mutanen farko suna bukatar idanuwan da za su ba su damar tsalle daga wannan reshen bishiya zuwa

wancan ba tare da sun fadi ba su kuma kama abinci da hannunsu su tura a baki.

A yanayin da nau'in halittar mutanen farko(halittar da masana ke kwatantawa da biri da suke cewa daga ita ne halittar ta juye ta zama mutum a yau) yake inda suke rayuwa a kan bishiyoyi domin kaucewa dabbobin da za su iya

cinye su, suna bukatar yanayin idanuwan da za su iya rayuwa a kan bishiyoyi har suma su iya kama sauran kwari ko halittu da suke ci, masanin yana ganin wannan shi ya sa sauyin halittar ya fi dacewa da su idanuwansu su kasance a fuska ta yadda za su iya sanin zurfin wuri da kyau

Hakkin mallakar hoto Reuters

Idanuwan kaji ko wasu tsuntsayen suna gefe ne domin hakan ya ba su damar sanin fadin filin da suke ta yadda za su kauce wa halittun da suke kama su su ci.

Duk da dai cewa an sake nazari da sabunta dalilan da masani Collins ya bayar na dalilan da ya sa halittun da suka juye suka zama mutum a yau suke da idanuwansu a gaba, wanda ya ce saboda suna rayuwa ne a kan bishiya ta

yadda za su iya tsalle daga wanna reshe zuwa wancan , kuma su kama halittun da suke ci, tare da kiyayewa da zurfi ko nisan da ke tsakaninsu da kasa ta yadda za su kauce wa halittun da su kuma suke cinsu, duk da haka an ci gaba da dogara da wannan bayani.

Saboda ko ba komai idan aka yi la'akari da hadarin da yake tattare da kuskurewa ko fadowar wadancan halittu da masana ke cewa su ne asalin mutum daga kan bishiya wadda kasanta halittu ne manya-manya irin su kada da makamantansu na wancan zamani abu ne da za su yi gudun ya same su, inji wani masanin Christopher Tyler wanda ya yi nasa rubutun a 1991.

Matsalar dalilai ko nazarin da Collins ya yi ita ce, da dama daga cikin dabbobin da suke rayuwa a kan bishiya idanuwansu suna gefe ne misali kurege.

Saboda haka ne a 2005 wani masanin, Matt Cartmill, ya kawo wani dalilin inda ya ce, shi yana ganin halittun da suke kama wasu halittun su cinye a matsayin abincinsu, suna da idanuwansu ne inda za su fi ganin wadanda suke kamawa da kyau kawai.

Cartmill yana ganin bayanansa su ne suka fi inganci saboda sun kara bayar da haske a kan wasu sauye sauye da nau'in halittar dan adam ta farko ta samu.

Misali wadancan halittun na farko suna farauta ne ta amfani da ido ba jin kanshi ba, saboda haka ne masanin yake ganin jin kanshinsu ya ragu ko kuma shi ya sa ba sa jin kanshi kamar yadda suke gani.

Saboda hakan ne ma filin da ke tsakanin hancinsu da kwakwalwa ya kasance kadan saboda iaduwa sun cika wurin inji shi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Dabbobin da suke kama wasu su ci kamar wannan damusar suna da idanuwansu a gaba ne domin samun saukin gano dabbokin da za su kama su ci.

Wani masanin John Allman, shi kuma ya dora ne a kan dalilan da Cartmill ya bayar ne inda ya fadada su.

Ya ce to ai ba duka dabbobin da suke kama wasu dabbobin su cinye ba ne suke da idanuwansu a gaba.

Shi yana ganin dabbobin da suke da idanuwa a fuska wadanda suke farauta da dare ne kamar su mujiya da kyanwa da damusa saboda sun fi zure wa haske ba kamar masu idanuwa a gefe ba.

A don haka ne yake ganin halittun da suka juye suka zama mutane a yau su ma a lokacinsu suka fi farauta da dare, wannan ya sa idanuwansu har ma da na jikokinsu zuwa mutane kamar yadda suke a yau suke da idanuwa a fuska.

Hakkin mallakar hoto AP

Wani masanin Mark Changizi, shi kuma yana ganin kamar yadda ya bayar da bayani a wata mujalla ta kimiyya Journal of Theoretical Biology a 2008, ya ce, ido a gaba ya ba wa kakanninmu dama su rika ganin tsakanin tarin ganyayyaki da rassan bishiyoyin kungurmin dajin da suke ciki a lokacin da kyau.

Ya bayar da wani misali inda ya ce, idan ka tayar da dan yatsanka daya a gaban idonka kuma ka kura wa wani abu da ke can nesa ido za ka ga yatsan naka kamar ya zama biyu kuma kana iya hangen abin da ke can gaba ta

cikin yatsan naka, wanna zai sa ka ga kamar kana iya ganin hatta cikin halittar abu kamar yadda na'ura za ta iya dauka, wadda ake cewa mai gani har hanji.

Duk da wadannan dalilai na bincike da masanan suka bayar har yanzu ba za a iya cewa an kawo karshen muhara a kan dalilin da ya sa muke da idanuwanmu a fuska maimakon a gefen kanmu ba, domin kowace hujja ko bayani yana da karfinsa da kuma gazawarsa.

To amma dai ko idanuwanmu sun kasance ne a gaba domin mu iya ganin tsakanin rassan bishiya ko farautar wata dabba ko mu iya ganin tsakanin ganyayyaki, abu daya da yake tabbas shi ne, abu ne da ya ke da alaka da rayuwa a kan bishiya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Turanci latsa nan Evolution : Why do your eyes face forwards?