Lokacin barci na tasiri sosai a wasanni

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lokacin tashi daga barci ne sirrin nasarar Real Madrid?

Masu bincike sun ce yanayin yadda jikinmu yake amfani da lokacin yin abubuwansa yana da tasiri sosai a kan kokarinmu a wasanni, wanda hakan zai iya sauya damar da mutum yake da ita ta cin lambar zinariya a wasannin Olympics.

Masanan na Jami'ar Birmingham, sun nuna cewa lokacin kokari ko akasin hakan a wasannin da mutane ke yi, ya bambanta da kashi 26 cikin dari a duk rana. Binciken nasu ya nuna cewa mutanen da suke tashi daga barci da wuri, sun fi kokari a wasanni a daidai lokacin cin abincin rana.

Su kuma wadanda ba sa tashi da wuri wato wadanda ke dadewa ba su kwanta da daddare ba sun fi kwazo a wasanni da yamma.

Masanan sun ce binciken zai iya ma bayyana abin da ya sa kungiyoyin kwallon kafa na kasar Spaniya suka fi yin nasara a wasannin Kofin Turai.

Agogon cikin jikin mutum kamar yadda masu binciken suka kira shi, shi ke tafiyar da komai a jikin, daga yanayin da mutum yake na farkawa ko lokacin da ba barci yake ba zuwa hadarin bugun zuciya a kullum.

Ana ganin wasu fannoni na kokarin mutum ko kuzarinsa a wasanni sun fi tasiri da farko farkon rana, to amma wani nazari da aka sa a mujallar kimiyya ta Current Biology, ya nuna cewa yanayin barcin kowana dan wasa yana da muhimmin tasiri.

Masu binciken sun tattara 'yan wasan kwallon gora mata 20, inda suka bukace su, su yi 'yan guje-guje daban-daban na minti 20, a takaitattun lokuta.

'Yan wasan sun yi hakan a lokuta shida daban-daban a rana, tsakanin karfe 7:00 na safe da karfe 10:00 na dare.

Jumullar sakamakon da aka tattara ta nuna an fi samun kyakkyawan sakamako ko kuma 'yan wasan sun fi kokari a wuraren karfe hudu zuwa biyar na yamma.

To amma kuma masana kimiyyar daga nan sai suka sake kasa 'yan wasan gida uku, da wadanda suke tashi daga barci da wuri da wadanda ba sa tashi da wuri da kuma wadanda suke tsakiya.

Daga nan kuma sai aka ga bambancin da ke tsakanin wanda ya fi kokari da wanda bai yi kokari ba kashi 26 ne cikin dari, daga nan kuma sai lissafin ya sake fadadawa:

Masu tashi da wuri sun fi kokari a 12:00 na rana sannan 'yan tsakiya sun fi kokari 'yan lokuta kafin 4:00 na yamma, su kuma wadanda ba sa tashi da wuri da sukan shafe dare kafin su kwanta sun fi kokari kafin 8:00 na dare.

Jagoran binciken Dakta Roland Brandstaetter ya gaya wa BBC cewa: 'yan wasa da masu ba su horo za su amfana sosai idan suka san lokacin da mutum ya fi kokari da kuma lokacin da ba shi da kokari.''

Masanin, ya kara da cewa bambancin kashi daya cikin dari na kokari ko kwazo a wasa zai iya kawo bambanci tsakanin na hudu da wanda ya zo na daya, ya samu lambar zinariya a wasannin Olympics da dama.

Amfani:

Agogon cikin jikin mutum (kamar yadda masanan ke cewa) ko kuma lokacin aikin jikin mutum abu ne da za a iya sake tsarinsa ko kuma a ce saita shi, to amma mutum zai dan shiga wani yanayi na daban na dan lokaci kafin jikin nasa ya saba da wannan sauyi.

Masanin ya ce, ''idan kai me tashi daga barci da wuri ne ka shiga gasa da yamma, to ka gamu da matsala. To amma za ka iya sauya lokacin barcinka ya dace da lokacin gasar.''

Dakta Brandstaetter ya ce, wannan matsala ta agogon cikin jikin mutum, ita ce ke shafar fafutukar Ingila a gasar cin kofin Zakarun Turai na kwallon kafa.

Ya ce, ''kana da 'yan wasan da suke kokari sosai a gasar Premier ta Ingila da karfe uku na rana(GMT) amma kwatsam sai ka ga ba sa kokari kuma da almuru a gasar kofin Zakarun Turai.''

Masanin ya ce, yana ganin saboda a Spaniya ana harkoki kusan da yamma ne idan aka kwatanta da Birtaniya inda ake farawa da wuri, wannan shi ya sa kungiyoyin wasan Spaniya ke samun nasara a kan wannan kasa.

Image caption Emily Defroand mai tashi barci da wuri daga hagu

Emily Defroand mai shekara 20 wadda ta yi wa tawagar kwallon gora ta Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 wasa har sau 56 tana daga cikin wadanda aka gudanar da binciken a kansu kuma ta ce ingancin sakamakon ya ba ta mamaki matuka.

Tana daga cikin masu tashi daga barci da wuri, daliba ce ta daban wadda da karfe 7:30 ta tashi daga barci.

Ta ce: ''Muna wasanninmu na ranar Asabar ne da karfe 12:30, kuma ina ganin wannan lokaci ne da ya yi min daidai. To amma fa da zarar lokacin ya wuce haka sai na ji na gaji ina bukatar in dan sha wani abu da zai kara min kuzari.''

Sai dai wannan bayanin da ta yi ya sha bamban da na abokiyar wasanta ta kungiyar, Olivia Chilton.

Ita kuma cewa ta yi: ''Ina tashi ne da karfe 11:00 na safe idan zan iya. Na fi son yin atisaye ko motsa jiki wuraren karfe 4:00 na yamma ko ma dai da la'asar sakaliya.

''A gaskiya da safe ji nake ban wartsake ba daga barci idan muna atisaye, sam-sam ba na ji na garau yadda zan iya wasa sosai.''

Neman sabbin 'yan wasa:

Dakta Brandstaetter ya ce binciken ya bayar da dama mai kyau ta nemo sabbin 'yan wasa.

Ya ce,'' wannan abu ne da sau da dama yake faruwa a kan matasa baligai wadanda mun san cewa rabinsu ba sa tashi da wuri saboda ba sa barci da wuri, to amma neman 'yan wasa abu ne da ake yi a lokacin karatu a makaranta inda kowana dalibi yana nan.''

''A don haka wannan lokaci ne da suke kan kwazonsu na tsakanin kashi 70 zuwa 80 cikin dari saboda haka muna asara sosai domin muna yin gwaji a lokacin da bai dace ba.''

Da yake magana akan sakamakon binciken, Dakta Thomas Kantermann, na Jami'ar Groningen ya gaya wa BBC cewa, ''binciken ya kara mana ilimi game da agogon cikin jikin mutum (wanda a kimiyyance ake kira circadian clock ko

body clocks a Ingilishi) da kuma tasirin agogon a kan kwazo ko kokarin mutum na jiki.

Ya ce ,'' ta hanyar la'akari da lokacin aikin jikin mutum ne kadai za a iya tantance kokarin mutum na gaskiya.''

''Wannan bincike ya tabbatar da bincikenmu na baya tare da bude hanyar gudanar da wasu binciken masu amfani a nan gaba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Bedtime 'has huge impact on sport'