Sau nawa maza suke tunanin jima'i?

Ko maza suna tunanin jima'i a duk dakika bakwai? Ba lalle ba. To amma maimakon ya yi mamakin ko hakan gaskiya ne, Tom Stafford ya yi tambaya ne kan yadda za a ce za a iya tabbatar da hakan ko a'a.

An gaya mana cewa maza suna yawan tunanin jima'i kusan a duk dakika bakwai kamar yadda wasu bayanai suka nuna.

Yawancinmu mun yarda da wannan magana tsawon lokacin da ya kai har ma muna shakkun gaskiyarsa.

To maimakon ka tsaya kana tunanin ko hakan gaskiya ne, kawai ka tsaya ka yi tunanin yadda za ka tabbatar da hakan ko ka karya ta.

Idan mun yarda da wannan kididdiga ta cewa maza kan yi tunanin jima'i a duk bayan dakika bakwai a rana hakan na nufin ke nan sau 514 suke yi a duk sa'a daya. Ko kuma ma a ce sau 7,200 a duk ranar da yake a farke(ba ya barci).

Hakan ya yi yawa ne ko in ce lambar ta yi girma ne? Ina ganin abin ya yi yawa ina ganin hakan ya wuce yawan duk tunanin da nake yi a rana. To amma ga wata tamabaya mai kyau: ta yaya zan iya kirga yawan tunani na ko na wani(na jima'i ko na wani abu) a rana ?

Hanyar masana kimiyya ta kirga tunani dai ta hada ne da dakatar da mutane kwatsam a daidai lokacin da suke wani abu, a kuma bukace su, su fadi tunanin da suke yi a wannan lokacin kuma a wannan wurin.

Terri Fisher da ayarinta na masu bincike daga Jami'ar Jihar Ohio ta Amurka sun gudanar da wannan binciken.

Sun bai wa wasu daliban kwaleji 283 abin da za su rika dannawa na kirge, inda suka raba daliban gida uku suka ce musu a duk lokacin da suka ji tunanin jima'i ko abinci ko barci ya zo musu to su danna wannan abu domin kirgawa.

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Ta hanyar wannan bincike sun gano cewa akalla cikakken namiji yana tunanin jima'i sau 19 a rana.

Wannan ya wuce na matan da aka gudanar da binciken a kansu, inda su kuma binciken ya nuna mace tana tunanin jima'in kusan sau goma a rana.

Sai dai kuma binciken ya nuna cewa maza bayan tunanin na jima'i suna kuma tunani a kan abinci da barci, wanda hakan ke nuna cewa maza sun fi zama wadanda wasu abubuwan na rayuwa ke shigar musu rai.

Ko kuma in ba haka ba wadanda aka yi binciken a kansu sun rika kirga duk wani abu da ya zo musu rai ko da ba wani tunani ba ne na sosai, sai su dauke a matsayin tunani.

Babban dai abin sha'awa a kan binciken shi ne yawan bambance bambancen da aka samu na tunani iri-iri.

Kamar yadda wasu suka ce suna tunanin jima'i sau daya ne a rana, yayin da wasu kuma suka nuna cewa suna tunaninsa sau 388, wanda hakan ya nuna cewa kusan duk minti biyu suna tunanin jima'in.

Sai dai wata babbar matsala da wannan bincike ita ce, dabi'ar nan ta dan-adam, wadda a duk lokacin da ka fara tunanin wani abu, idan ka so ka daina tunanin daga nan zai rika ci gaba da dawo maka.

Wannan shi ne yanayin da daliban da aka gudanar da binciken Fisher suka samu kansu a ciki.

Hakkin mallakar hoto Getty

Ka duba ka gani, masu binciken sun basu abin da za su rika dannawa a duk lokacin da suka ji tunanin jima'i ko abinci ko barci ya zo musu. To ka yi tunanin sun bar wurin da suke wato sashen nazarin halayyar dan-adam na kwalejin, suna rike da wannan abin dannawa a hannu suna kokarin ka da su yi tunani a kan jima'i a ko da yaushe kuma a dai dai lokacin suna kokarin tunawa su danna wannan abu.

Anan abin da nake gani shi wancan mutumin da ya ce yana tunanin jima'i ko ya yi tunanin jima'i sau 388 yanayin da ya samu kansa a ciki ke nan.

Ko da yaushe a raina:

Wata hanyar binciken kuma ita ce wadda Wilhelm Hoffman da abokan aikinsa suka yi, inda suka bai wa wasu Jamusa manya wayoyin salula na komai-da-ruwanka, wadanda aka saita ta yadda za su rika tunatar da su sau bakwai a rana a lokuta daban daban har tsawon sati daya.

Masu binciken sun bukace su da su rubuta a cikin wayar abin da ya zo musu a tunaninsu a duk lokacin da kararrawar wayar ta kada.

Dalilin sa su, su rubuta abin a wayar domin adanawa, shi ne saboda tunaninsu ya kasance ba abin da yake ciki da ya shafi adana abin da ake so su rubuta, ma'ana idan suka rubuta abin a wayar za su iya ci gaba da harkokin da suka saba ba tare da wani abu ya shiga ransu ba.

Sakamakon da aka samu ba za a iya kwatanta shi kai tsaye da na (mai bincike) Fisher ba, domin mafi yawan da aka samu shi ne wanda ya yi tunanin sau bakwai a rana.

Mutanen sun samu sakamakon da ya nuna cewa kusan sau daya mutum ke yi a rana idan aka kwatanta da sakamakon Dakta Fisher wanda ya nuna sau 19 mutum ke tunanin jima'i a rana.

Gab daya dai abin da ya bayyana shi ne mutane suna tunanin jima'i amma ba kamar yadda wancan bayani na baya ya ce ba, na cewa mutum na yi sau daya a duk dakika bakwai. Abin bai kai haka ko kusa.

To sai dai kuma abin mamakin da binciken Hoffman shi ne yadda wadanda aka gudanar da binciken a kansu tunaninsu ba ya kawo musu maganar jima'i.

Abubuwan da tunaninsu ya kunsa su ne, abinci da barci da tsaftar jikinsu da ganawa da jama'a da hutu da shan gahawa( a kusan karfe 5:00 na yamma) da kallon talabijin da duba wasikar email da kuma sauran abubuwan da suka shafi harkar sadarwa ko labarai a duk tsawon rana.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A zahirin gaskiya ma tunanin jima'i ya zo musu ne kusan a karshen rana(kusan 12:00 dare) kuma ko a lokacin ma ya zo ne bayan tunanin barci.

Haka shi ma wannan bincike na Hoffman za a iya cewa ya gurbata da matsalar da na Fisher ya gamu da ita, domin mutanen da aka gudanar da binciken a kansu sun san cewa a wani lokaci a rana za a bukace su, su rubuta abin da suke tunani a cikin wayar, wannan zai sa su ga cewa sun yawaita wasu ko wani tunanin.

Idan ya kasance tunanin jima'i din suke yi, hakan zai sa su ji kunyar nuna cewa tunanin jima'i sukle yawan yi a rana, saboda haka sai su ki rubutawa da yawa.

Duk da cewa za mu iya yin watsi da labarin da ke cewa yawancin namiji babba yana tunanin jima'i sau daya a duk dakika bakawai a rana, to amma kuma fa ba za mu iya tabbatar da cewa ga ainahin yawan da yake na hakika ba.

Wannan abu ne da zai iya kasancewa ya bambanta daga mutum zuwa mutum, kuma ko da a kan mutum daya ma ya danganta da yanayin da yake ciki da lokaci. Kuma abin da zai kara rikita lissafin ma shi ne duk wani kokari na kirga tunanin mutum a kan wani abu, hakan zai iya sa ya sauya tunanin nasa.

Bayan wannan kuma akwai matsala ko muhawar cewa babu wata hanya ta kidaya tunanin mutum dalla-dalla.

Tunani ba abu ba ne mai tazara ko nisa da za a iya cewa an auna shi kamar yadda ake auna nisan gari ko tsawon wani abu na fili ko zahiri.

To in haka ne menene ya hadu ya zama tunani? Kamar girman me zai kai kafin a iya kirga shi? Ba tunanin da ka yi ko daya ko ma da yawa yayin da kake karanta wannan? Akwai tarin abubuwa da dama da za a yi tunani a kai!

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How often do men really think about sex?