Ko damuwa za ta iya sa ka furfura a dan lokaci?

Wannan abu ne da ake yawan fade wanda har ma aka ce ya faru a kan Marie Antoinette.To amma kamar yadda Claudia Hammond ta gudanar da bincike abu ne mai wahala a gano matsalar.

A 1982 wani matukin jirgin sama Eric Moody ya shirya tsaf domin tafiyar cikin dare daga Kuala Lumpur zuwa Perth.

Komai ya kasance tsaf, yanayin sama yana da kyau kuma ma'aikatan jirgin kowa yana cikin walwala saboda sun samu karin hutu a Malaysia.

Bayan sun tashi, suna sararin samaniyar birnin Java sai wani injin jirgin ya lalace.Kafin wani lokaci kuma sai wani injin shi ma ya lalace.

Haka dukkanin injinan jirgin suka rika lalacewa daya bayan daya har sai da ta kai duka injinan sa guda hudu ba wanda yake aiki.

Daga nan ne sai matukin jirgin cikin murya mai kwantar da hankali ya sanar da mutanen cikin jirgin cewa injinan jirgin gaba daya hudu sun lalace, amma suna iya kokarinsu domin gyara su, ya kara da cewa,'' na san ba za ku damu ba kwarai.''

Duk a wannan yanayi da ake ciki, Eric Moody, bai nuna wata damuwa ko fargaba ba sosai, har ya samu ya yi saukar gaggawa a filin jirgin Jakarta.

Daga baya ne ya gano cewa tarin kurar tokar talgen wani dutse ne ya lalata injinan.

Watanni shida bayan wannan tsallake rijiya da baya da suka yi ne sai Eric ya lura cewa gashinsa na goshi ya fara yin fari.

Cikin shekara daya kuma sai sauran gashinsa shi ma ya zama haka, ya yi furfura.

Wannan matukin jirgin sama, ba shi kadai ya taba gamuwa da wannan abu ba, na yadda lokaci daya gashi zai yi fari.

Lamarin ya faru da fitattun mutane da da yawa kuma a dan kankanin lokaci.

Lokacin da aka kai sarauniyar Faransa Marie Antoinette, wurin na'urar datse wuya tana da shekara 37, an ce gashinta ya yi furfura kafin daren shigar da ita wurin, saboda fargabar za a aiwatar mata da hukuncin kisa.

Haka lauyan nan na Ingila Sir Thomas More,wanda daga baya aka ayyana shi a matsayin waliyyi,bayan an aiwatar masa da hukuncin kisa a hasumiyar Landan a 1535 shi ma an ce gashinsa ya zama fari kafin mutuwarsa.

Wadannan duka labarai ne masu kyau a kan wannan lamari ,to amma haka suke a kimiyyance, abu ne da zai iya kasancewa a kimiyya?

Gashin mutum zai iya yin furfura a lokaci daya? Akwai wata hanya ta zahiri da tsananin damuwa zai iya sa gashi ya yi furfa da sauri haka?

Gashi yana samun launinsa ne daga wasu sinadaran halitta biyu, eumelanin, wanda shi ne zai sa irin bakin da gashi zai yi, sai kuma pheomelanin, wansa shi kuma shi ne zai sa yawan launin ja ko ruwan dorawa ko rawayar da gashin zai zama.

To yayin da muke girma ko tsufa kwayoyin halittar da suke kofar gashinmu sai su daina samar da sinadaran nan biyu, daga nan sai gashinmu ya zama maras launi.

Daga nan ne sai hadin gashi mau launi da maras launi ya sa a rinka ganin kai ko jikin mutum ya yi furfura musamman a wurin mutanen da suke da bakin gashi.

Abin da yake haddasa wannan sauyi ba a fahimce shi sosai har yanzu, inda wani bincike ya nuna cewa gashi yana furfura ne ko rasa launi ta hanya iri daya da yadda ake sauya launin gashi idan mutum yana son ya yi ado ko wani abu na fitar da launin gashinsa, ta amfani da sinadari na kanti(bilichi).

Abin da aka fahimta kawo yanzu ta hanyar amfani da bera, aka yi gwaji shi ne, kwayoyin halittar da suke sinadarin melanin (wanda yake sa launin) suna kuma samar da sinadarin hydrogen peroxide, wanda shi kuma wani sinadarin da ake kira catalase yake sarrafa shi.

To yayin da mutum yake tsufa sai wannan sinadari na catalase ya ragu, wanda hakan kuma yake shafar samar da hydrogen peroxide, sai hakan ya sa sinadarin melanin ya daina samuwa, gashi ya daina launi.

Bayanin da aka bayar mafi gamsarwa kawo yanzu a game da lamarin da yake sa gashin mutum ya zama fari cikin dan kankanin lokaci shi ne, ba wai gashin ne yake sauya launi ba, sai dai gashin ne mai launi yake zubewa ya haifar da sanko ko fili a inda da gashi yake.

Ana ganin hakan yana samuwa ne ta hanyar yadda tsarin garkuwar jiki ke mayar da martani ko daukar mataki kai tsaye.

Damuwa ko wahala ka iya sa hakan ya ci gaba cikin gaggawa, wanda kuma hakan ya sa ake danganta furfura da wahala ko damuwa.

A wasu lokutan lamarin ko kuma sankon ba ya shafar furfurar ko farin gashin.

Haka kenan yana nufin idan mutum ya gamu da wani abu da ya ta da masa hankali sosai, zai iya sa gashinsa mai launi ya rika zubewa, ya bar shi da farin, sai a ga furfura kawai a kansa, ko kuma lamarin ya shafi sinadarin da yake samar da launi ga gashin, launin ya daina yi.

Hakan ya yi kama da yanayin da matukin jirgin saman nan (moody) ya gamu da shi, inda a shekara daya kawai gashinsa ya zama fari gaba daya.

Sai dai yanayin da yake sa gashin mutum ya zama fari cikin dare daya ko dankankanin lokaci kamar na Marie Antoinette, na da wuyar fahimta.

Ita dai Marie an tsare ta ne tsawon shekara daya, kuma watakila ana ganin an hana ta ruwan magani ko sinadarin tura gashinta a lokacin da take tsare.

Hakan ya sa ake ganin a lokacin da aka zo aiwatar mata da hukuncin kisa, mutane suka ga gashinta ya zama fari saboda an rarrage mata gashin sai tohon gashinta mai furfura ya nuna.

Sai dai wannan bayani ba zai iya zama dalili na yadda wasu mutanen suka gamu da tasu matsalar ba.

Misali akwai matasan da suke da furfura 'yar kadan wadanda kuma idan duk bakin gashinsu ya zube za a ga farin gashin da ke kansu ya yi warawara(wato wasu wuraren ba gashi sosai).

Akwai kuma na kusa kusan nan, wanda ya faru akan wata mata 'yar kasar Switzerland, wadda gashin kanta ya dan zube a wani wuri, sai aka ba ta wasu magunguna da suka warkar mata da wurin gashinta ya dawo.

To amma kuma sai kawai cikin 'yan makwanni gashinta gaba daya ya zama fari duk da cewa babu wani abu na tashin hankali da ya same ta kuma gashin nata ya daina zubewa.

A shekara ta 2011 wani bincike da wasu masana karkashin jagorancin daya daga cikin mutanen da suka samu lambar yabo ta Nobel Robert Leftkowitz a 2012, ya samar da wasu 'yan bayanai.

Masu binciken sun nuna yadda wani abu mai matukar tayar da hankali ya yi illa a kwayoyin halittar bera na DNA(da suka yi gwaji a kansa), wanda hakan zai iya sa ya yi furfura.

Gano yadda matsalar cewa gashinka zai iya yin furfura abu ne da ake ganin kamar marar wahala a fagen kimiyya, to amma lamarin ba haka yake ba.

Idan dai ana son gudanar da wannan bincike dole ne sai an yi nazarin gashi kafin wani abu na damuwa ko tayar da hankali ya samu mutum da kuma bayan ya same shi, a yi nazari cikin tsanaki na kan launi da kuma kaurin gashin.

Wani abu kuma a nan shi ne, abin da zai tayar wa da mutum hankali sosai ba abu ne da yake faruwa ba a ko da yaushe sai a lokuta, kuma babu wata hukuma da za ta yarda a sa wani mutum cikin irin wannan hali da sunan gudanar da bincike.

Duk da haka akwai wani abu game da dalilin da yake sa mutum furfura idan ya gamu da wani abu na tashin hankali ko damuwa, mai ban sha'awa. Watakila a iya cewa duk yadda ka kai da boye halin da kake ciki na damuwa, mutane ba su gane ba, kamar yadda wannan matukin jirgin sama Moody, ya yi har ya ceci rayukan mutanen cikin jirgin 247,jikinka sai ya nuna.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Can stress turn your hair grey overnight?