Me ya sa yawancinmu masu amfani da hannun dama ne?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Mutane masu amfani da hannun dama(ba-damai) sun fi yawa a duniya- me yasa haka? Jason G Goldman ya bincika

Mu mutane ba kasafai muke yarda da komai ba haka kawai,amma duk da haka akwai abu daya da za a iya cewa yawancinmu mun amince da shi ba tantama: wannan kuwa shi ne hannun da ya fi saukin sarrafawa ko kuma hannun da muka fi amfani da shi.

Idan kana amfani da hannu daya wajen rubutu da wuya a ce ba da shi kake amfani wurin cin abinci ba, kuma a nan kusan kashi 85 cikin dari na jinsinmu (mutane) mun fi amfani da hannuwanmu na dama.

A takaice ma dai babu wani rahoto ko bincike da ya nuna cewa akwai wata al'umma da mutane masu amfani da hannun hagu suka fi yawa a cikinta, kamar yadda masaniya kan ilimin binciken kayan tarihi na kasa Natalie Uomini ta Jami'ar Liverpool a Birtaniya ta ce.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Nuna fifiko wurin amfani da wani hannu yawanci yana farawa ne daga kwakwalwa, tun da mun san wasu ayyukan da mutum yake yi yawanci bangaren hagu ne na kwakwalwa ke tafiyar da su, yayin da bangaren dama kuma yake tafiyar da wasu ayyukan shi ma.

Sai dai kuma wani abin mamaki ko rudarwa shi ne bangaren kwakwalwa na hagu shi yake tafiyar da ayyukan da sashen jikin mutum na dama yake yi, wato su ido su hannu su kafa da sauransu. Haka kuma bangaren dama na kwakwalwa shi yake tafiyar da ayyukan sashen jikin mutum na hagu.

Wasu masanan suna ganin wannan tsari na rabon aiki tsakanin jiki da kwakwalwa, abu ne da dabbobi suke da shi tun shekaru miliyan dubu 500.

Ana ganin tsarin ya samo asali a jiki domin ta hakan bangarori biyu na kawakwalawar za su fi aiki da kyau ta yadda za su iya yin ayyuka daban daban a lokaci daya.

Misali bangaren hagu na kwakwalwar ya kasance ne domin ya rika ayyuka kamar neman abinci, yayin da shi kuma bangaren dama zai zauna kawai yana lura da duk wani abu na barazana da zai iya nufowa( misali wata dabba ta kawo hari ) domin daukar matakin da ya dace.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Za a iya ganin hakan a kan kifaye da kwadi da kuma tsuntsaye wadanda suke iya kai hari kan wani abu (dabba) da idonsu na dama ya gani.

Saboda haka abu ne da za a iya cewa (ko da yake da wuya a tabbatar) lokacin da kakannin dan-adam na asali,( kamar yadda masana kimiyya suka nuna cewa dan-adam ya faro ne daga wasu halittu masu kama da biri), suka fara mikewa suna tafiya da kafa biyu maimakon hannu da kafa, sai suka rika amfani da hannuwan wajen yin wasu sabbin ayyukan kamar kayayyakin aiki(misali wuka da fatanya da tukunya na dutse da sauransu).

Masaniya kan ilimin kwakwalwa Stephanie Braccini da abokan aikinta sun kara jaddada wannan bayani a wata mujalla ta kimiyya, Journal of Human Evolution, inda suka ce fifita amfani da bangaren jiki daya abu ne da ya samo asali tun lokacin da kakannin dan-adam na farko suka fara mikewa suna tafiya da kafa biyu lokacin farautar abinci da amfani da kayayyaki na tafiyar da rayuwa.

Domin su kara jaddada wannan dalili na su, Braccini da abokan binciken nata, sun duba yadda birrrai suke idan suna tafiya hannu da kafa, inda ba sa nuna wani fifiko a kan wani bangare a lokacin, amma da zarar sun tashi tsaye daga nan ne kuma sai su ba da fifiko wajen amfani da wani hannun nasu na haugu ko na dama.

To amma duk da wannan akwai bukatar sanin abin da ya sa halittun da suka kasance kakannin dan-adam na farko suka zama yawanci sun fi amfani da hannun dama(ba-damai) kamar yadda muke gani yau a tsakanin mutane.

Mun ga yadda wannan sauyi ya samo asali daga yadda masu bincike suka yi irin nasu kayayyakin na ayyukan rayuwa irin na zamanin halittun na da (kakannin da-adam), insa masanan suka yi amfani da hannun hagu ko na dama, wajen sassaka abubuwan, kafin su hada su da na zamanin na da.

Yin hakan ya nuna cewa shedar da ake da ita kadance, ta cewa kakannin dan-adam da suka sassaka kayayyakin nasu sama da shekaru miliyan biyu da suka wuce masu amfani da hannun dama ne.

Sai dai kuma kayayyakin aikin na zamanin da, da aka yi tun shekaru miliyan daya da rabi da suka wuce, a Koobi Fora da ke kasar Kenya, wadanda halittun na zamanin da suka yi da duwatsu, sun nuna alamun wadanda suka yi su masu ba da fifiko wajen amfani da hannun dama ne.

Haka kuma lokacin da aka samu karin rikida ko sauyin halittun da suka kasance kakannin na dan-adam( daga Homo habilis zuwa Homo erectus zuwa Homo heidelbergensis) a kusan shekaru dubu 600 da suka wuce, sai fifikon na amfani da hannun dama ya fito karara a wancan zamanin.

Hakkin mallakar hoto BRIAN VILMOARE

A binciken da aka gudanar a jikin hakoran halittun na zamanin (wadanda aka adana) an ga yadda hakoran suka goge sakamakon yawan amfani da su yau da kullum daga wani bangare, abin da ya nuna cewa suna kai abinci baki ne da hannun dama.

Wannan ya nuna mana a lokacin da aka samu wannan sauyi amma bai nuna mana dalilin hakan ba. Wasu na ganin hakan ya dangana ne kacokan ga yare ko harshe.

Kamar yadda mutane da yawa suke masu amfani da hannun dama kamar yadda idan mai karatu ya tuna a baya an ce bangaren hagu na kwakwalwarsu ke tafiyarwa, haka kuma yawancin mutane suke aikin abin da ya shafi harsunan da suke yarawa da sashen hagu na kwakwalwar tasu.

Bincike ya nuna cewa ma yadda sashen na hagu na kwakwalwa ya kware da abin da ya shafi yaren mutum, har ma ya fi na amfani da hannun daman.

A kan hakan ana ganin yadda bangaren hagu na kwakwalwar yake aiki sosai a kan abubuwan da suka shafi harshe ko yaren mutum, karkatar mutum wurin hannun dama fiye da hannun hagu ta kasance ne a matsayin wata illa da hakan ya haifar.

Saboda haka ne ake ganin kasancewar yawancinmu da muke amfani da hannun dama abu ne da ya faru sakamakon yadda kwakwalwarmu ke aikatuwa.

Sai dai kuma wannan abu ne da yake da wuya ko kuma wanda ba zai yuwu ba a tabbatar da gaskiyarsa domin akwai bukatar gudanar da bincike na kwakwalwa da sauran sassan jikin halittun da suka juye suka zama mutum, wadanda kuma sun mutu da dadewa.

Gaskiyar magana dai ita ce mai yuwuwa ba za mu iya taba sanin abubuwan da suka faru daki-daki har ya zama halitta dangin dan-adam ta zama ta fi karkata a bangaren dama na jikinta da kuma bangaren hagu na kwakwalwarta.

Ku kuwa masu amfani da hannun hagu (bahago) ? Ka da ku damu! Kamar yadda wani bincike da aka wallafa a 1977 a wata mujalla mai suna Psychological Bulletin, ya nuna, shedar da ake da ita, ta cewa wai masu amfani da hannun hagu na da wata tawaya 'yar kankanuwa ce, ba ta taka kara ta karya ba.

A gaskiya ma wasu masu binciken sun nuna cewa masu amfani da hannun hagu za su fi saurin warkewa idan suka ji rauni a kwakwalwarsu.

Haka kuma bahagwayen sun fi kokari ko samun nasara a wasanni irin su dambe ko fada. Wanda duka wadannan abubuwa ne da ke tabbatar da cewa akwai dai amfanin kaucewa ko sabawa abin da ya zama al'ada.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Evolution: Why are most of us right-handed?