Yadda za ka yi nasara a komai

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A wasanni ba za ka iya hashashen mutane ba da kwarin gwiwa. Abin da za ka iya yi kawai shi ne ka gano wannan dabi'ar ta boye sai ka iya yin nasara a kan duk wani abokin karawarka a duk wata gasa. Inji David Robson

Ko da ike dai ba za mu iya magance matsalar yanayi ko wani bala'i na daga Allah ba, to amma akwai hanyoyin da za mu iya lakantar wasu abubuwan da ba a iya hashashensu wadanda kuma suke da tasiri ko suke juya yawancin rayuwarmu da ta sauran mutane.

Kamar yadda William Poundstone ya rubuta a sabon littafinsa mai suna How to Predict the Unpredictable( wato yadda za ka yi hashashen wanda ba za a iya hashashensa ba), idan ka fahimci yanayin dabi'ar dan-adam daga nan za ka fara fahimtar wasu abubuwan da muke yi da ake dangantawa da hauka kuma mu yi amfani da wannan ilimi ko fahimta domin amfanin kanmu.

Duk abin dai ya ta'allaka ne da yadda mutane suke fargaba ko ganin abu ne mai wahalar gaske su jarraba wasu fannonin na daban sabanin abin da suka saba yi yau da kullum, ko su je wani bakon wuri da ba su sani ba sabanin inda suka saba zama.

Idan da ace kasan yadda za ka gano wannan dabi'a kuma ka zama mai kokarin jarrabawa kai kanka, to da ba da jimawa ba da za ka murkushe abokan karawarka a wadannan wasannin:

Wasan: Rock, Paper, Scissors ( na ishara da alamar dutse wanda dunkulallen hannu ke nan, da takarda wadda ake nunawa da tafin hannu da kuma almakashi wanda ake nunawa da yatsu biyu alamar nasara);

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wannan wasa ne da za a dauka ba shi da wani muhimmanci sosai, to amma ana amfani da shi wajen daukar matsaya a manyan harkokin kasuwanci.

Misali a shekara ta 2005 wani kamfanin kayan laturoni na kasar Japan ya bukaci dillalansa Christies da Sotheby's da su fafata a tsakaninsu wajen fitar da wanda za a ba wa damar sayar da wasu kayayyakin kamfanin na fasaha na dala miliyan 20.

Poundstone ya ce, a wannan wasa maza sun fi zabar alamar karfi, wato ishara da dutse (Rock), yayin da ita kuma alamar almakashi (Scissors) ba ta da farin jini a wurin maza da kuma mata. A saboda haka ne idan ka zabi alamar takarda(Paper) ka fi tsira, domin ko dai ka yi nasara ko kuma canjaras( ba a kasa ka ba).

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wata dabarar kuma ita ce, ka fadi alamar da za ka yi a fili, daga nan abokin karawarka zai dauka yaudara kake yi daga nan sai ya zabi wani abin da ba lalle ya yi nasara ba, sai ka yi galaba a kansa.

Wasan karta:

A wasanni kamar na Poker(sunan Ingilishi) mutane da dama ba sa yaudara a lokuta daban daban.Saboda idan aka gano mutum, musamman dan koyo ko sabon shiga, to ba zai iya karfin halin da zai sake yin hakan ba, domin yana ganin abokin karawar tasa ya riga ya fahimci salon wasansa. To amma kwararru kuwa za su iya yaudara sau biyu ko sau uku a jere ba tare da wata fargaba ta cewa abokin wasan katin zai gane salon takunsu ba, to amma ko su ma kwararru bayan yaudara ta biyu ko ta ukun a jere daga nan da wuya su ci gaba da yi.

Kwallon tennis:
Hakkin mallakar hoto All Sport

A wasan kwallon tennis, a ko da yaushe ka dauka abokin karawarka idan zai fara wasa(musamman dan koyo) zai bugo kwallon ne a gefen da ya ga ka kauce wa, ma'ana idan kana gefen dama ne to zai cilla kwallon gefen hagu.

Poundstone ya bayar da shawarar cewa, idan kana son ka sauya yadda tsarin yake wato ka jarraba wasu hanyoyin da hakan zai sa ka rikita lissafin abokin karawarka, kana iya yin amfani da agogonka, ka ce zuwa dakika 30 za ka buga kwallon bangaren dama, sanna kuma daga 30 zuwa 60 hagu za ka buga kwallon.

Cacar Lottery:
Hakkin mallakar hoto AP

Za ka ce ai wasan Lottery ana zabar lambobi ne ta ko yaya saboda haka ba wani abu ko da me wasu su ka yi, haka ne? To abin ba haka yake ba. Ko da yake nazarin tunanin dan-adam ba zai iya iko da yadda sakamkon zai kasance ba, amma zai iya hasashen abin da za ka ci(yawan kudin da za ka iya samu).

Amfanin al'adarmu ta camfa wasu lambobi ke nan, inda muke danganta wasu da nasara sosai wasu kuma da nasara kadan ko ma rashin nasara.

A wasa ko cacar Lottery wadda aka fi yi, inda za ka zabi lambobi shida tsakanin 1 da 49 Poundstone ya ce, kowacce daga cikin wadannan lambobin za ta iya ba ka nasara sosai: 10, 20,29,30,32,38,39,40,41,42,48,49.(to amma fa ba shakka idan miliyoyin mutane suka karanta wannan bayani to wannan dabara ko shawara ba za ta yi tasiri ba ke nan)

Idan kana ganin duka wadannan shawarwari masu sauki ne sosai, ina ba ka shawara da ka duba shawarar babban mai nazarin adabi Sherlock Holmes,wanda a littafinsa Hound of the Baskervilles, ya ce,''duniya na cike da abubuwan da suke a bayyane, wadanda ba wanda ya taba lura da su.

Ba tabbaci ba ne na samun nasara, amma sanin dan wani abu na hasashen yadda mutum yake tabbas zai iya ba ka nasara a kansa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How to win at (almost) everything