Abin da kila ba ka sani ba kan tafiya a jirgin sama

Abubuwa da dama suna faruwa a kewayenka a lokacin da ka hau jirgin sama, wadanda ba lalle ka san da su ba.BBC ta yi nazarin wasu daga cikin abubuwan da suka fi ban mamaki a wannan lokaci na tafiya taka.

Yawan mutanen da suke kasancewa a cikin jirgi a lokaci daya na ci gaba da karuwa inda suka doshi miliyan daya a yanzu. Bugu da kari a wannan lokaci na shekara ne mutane da dama a kasashen duniya suke shirin tafiye-tafiye a jirgin sama.

Ga wasu daga cikin irin abubuwan mamaki da BBC ta binciko wadanda suka shafi masu tafiye-tafiye a jirgin sama.

1. An daina amfani da na'urorin binciken kwakwaf da suke nuna wa masu bincike hoton mutum Zigidir(haihuwar uwa), ba tufafi a jikinsa, bayan da aka yi korafi.

2. Jirgin saman fasinja samfurin Airbus A380, yana iya daukar mutane 853.Saboda girmansa, ya sa dole aka sake tsarin wurin tsayuwar jiragen sama na filin jirgin Heathrow na Landan.

3. A yanzu jirgi zai iya tashi sama kai tsaye, kamar yadda jirgi mai saukar ungulu ke yi, ba sai ya yi gudu ko tafiya a kasa ba, idan da bukatar hakan, saboda karfin injin da aka yi masa na ko-ta-kwana (wato sifiya injin).

Hakkin mallakar hoto Reuters

4. A lokacin gwada jirgin da aka kera, a kan lankwasa fukafikinsa har kusan ya jingina a jikinsa domin a tabbatar da cewa ba karamin abu ko matsala ba ce za ta iya cire fikafikin, wato dai jarraba irin wahalar da jirgin zai iya jurewa.

5. Wasu masu tsarin filayen jiragen sama, su kan yi wasu dabaru na bunkasa kasuwanci a wurin, ba tare da ka sani ba. Za ka ga a wuraren da aka kebe na masu tafiya ba bu isassun kujeru na zama.

To a kan yi hakan ne domin idan ka rasa wurin zama maimakon ka tsaya sai ka tafi wurin sayar da abinci ko wasu kayayyaki ka shiga siyayya.

Hakkin mallakar hoto Getty

6. Dandanon bakinmu yana sauyawa idan muna tafiya a cikin jirgin sama. Saboda haka ne kamfanonin jirage suke kara gishiri a cikin abincin da suke rabawa mutane. Iskar cikin jirgin ce take sa mutane ba sa jin dandano sosai.

7. Mun fi yin tusa idan muna tafiya a jirgin sama. Ba ka jin haka abin yake to amma haka yake, idan ka tsaya ka lura. Saboda hakan ne ma ake sa wani abu da yake hana yaduwar wari ko doyi a cikin jirgin(Charcoal filter).

8. Hanyar da za ka rage gajiyar tafiyar jirgi ita ce, ka shirya wa doguwar tafiyar kafin ka fara ta

9. Duk da manyan haduran jirage da aka yi a shekarun nan, tafiya a jirgin sama ta fi kwanciyar hankali fiye da yadda take a da.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What you may not know about taking a flight