Me ya sa muke barci da ido?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Idanuwanmu suna kwantsa idan muna barci, to amma mecece kwantsar nan? Kamar yadda Jason G Goldman ya gano, abar tana da amfani fiye da yadda ake dauka.

Abu na farko da nake yi idan na tashi daga barci shi ne, na duba wayata na ga tarin abubuwan da yakamata in yi wadanda suka taru a lokacin da nake barci.

Abu na biyu kuma shi ne na goge kwantsar da ta taru a gefen idona, da daddaren.

Ko ma da wana suna ka kira ta da shi, ka dai san abin da nake nufi da kwantsa.

A kullum, ina tunanin abin da wannan aba ta kunsa da kuma dalilin da ya sa take fitowa a idon mutum, saboda haka ne na shiga bincike domin na gano wadannan bayanai.

Abu ne da ya fara da hawaye ko kuma ruwan da ke idonmu.

Shi ido ko a fuskar mutane ko karnuka ko bushiya ko giwaye duka dai dabbobin da ke shayarwa na tudu (doron kasa, ba na ruwa ba ko na sama),yana cikin gida uku ne na ruwa ko hawaye, ta yadda zai yi aiki sosai.

Gida na farko da yake kusa da idon, gida ne da yawanci ya kunshi ruwa mai yauki kamar majina, inda kwayar idon take, kuma ya ke jawo ruwa, wanda hakan ya ke samar da gida na biyu wanda shi kuma na ruwa ne.

Shi gida na farkon shi yake tabbatar da rarrabuwar gida na biyu wato ruwa a ido yadda ya kamata, wa to ya ce yawan ruwan da yake a nan shi ne a can.

Wannan rukuni na gidajen ido yana da muhimmanci, shi yake tabbatar da idonmu yana da ruwa ta yadda zai iya motsi, shi ne kuma yake wanke duk wani abu da zai kawo wa ido cuta.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Idan idanuwanmu ba sa barci ganinmu zai gamu da matsala

A karshe kuma sai gida na uku, wanda yake a waje, wanda kuma ya kunshi ruwa mai maiko da sauran abubuwa da suka jibanci mai.

Wannan ruwa mai maiko da ke cikin wannan gida na uku ya kasance ne daidai da yadda jikin dabbobi masu shayarwa suke.

A lokacin da yake yanayi na daidai da dumin jikin dan-adam, za a gan shi a yanayi na ruwa mai maiko-maiko. Idan kuma ya yi sanyi da akalla lamba daya a ma'aunin digirin Celcius sai ya bushe ya zama busasshiyar kwantsa da muka sani.

Wannan busasshiyar kwantsar za ta iyakasancewa a idon mutum da yawanta saboda wasu dalilai.

Da farko dai jikin mutum yana dan yin sanyi da dare, saboda haka wannan ruwa yakan yi sanyi ya daskare a wannan lokaci.

Na biyu kuma kamar yadda wani likitan ido dan kasar Australiya Robert G. Linton da abokan aikinsa suka ce, ''barci yana sassauta aikin jijiyoyin da ke kai wannan ruwa mai maiko na wannansashe na ido wanda hakan zai iya sa a samu kwararar ruwan da yawa a lokacin barcin wanda hakan yake sa ya kwarara a fatar da ke rufe idi da kuma gashinta.

Ba shakka ba wani abin damuwa ba ne mu murtsika idonmu don mu wartsake sosai idan muka tashi daga barci, amma to me ya sa, muke da wanna ruwa mai maiko a da yake zama kwantsarma ?

To abu na farko shi ne, wannan ruwa mai maiko shi yake hana hawaye ya rika zuba ba tsayawa daga idonmu, yana kwarara a kumatunmu.

Idan muka duba za mu ga ke nan idan hawaye yana ta kwarara daga idonmu zai yi wuya mu iya tafiyar da ayyukanmu na yau da kullum da idonmu ba tare da wahala ba.

Ta hanyar hana hawayenmu zuba a ko da yaushe, wannan ruwa mai maiko, yana sa idonmu ya kasance yana da lema a ko da yaushe.

Wani bincike ma ya nuna cewa yayin da idanun zomo ya rasa wannan ruwa mai maiko, ruwan idonsa yakan fice ta hanyar tururi da linki 17 kan yadda yake yi a ka'ida

Hakkin mallakar hoto spl
Image caption Sanyi a lokacin da muke barci yana taimakawa wurin taruwar kwantsa

Wannan ruwa mai maiko ba shi kadai ba ne yake hana ruwan idanuwanmu bushewa ba.

Kifta idanuwan da muke yi ma hakan yana da amfani, saboda wannan 'yar runtsawar da muke yi tana tatso wannan ruwa da hakan ke sa a samu dan karin wannan ruwa mai maiko a idon kari a kan wanda daman yake kwararowa cikin idon.

Haka kuma wannan kifta ido da muke yi na taimakawa wajen haduwar shi ruwan mai maiko da ruwan hawayenmu su samar da wani ruwan mai maiko sosai wanda shi kuma yake zama kamar makari ga kwayar idon.

Idan ka dade ba ka kifta idonka ba wannan ruwan mai maiko sosai sai ya rabu, domin ruwa da mai ba sa son haduwa, hakan sai ya sa kwayar ido ta kasance ba ta da kariya daga iska.

Wanda kuma hakan zai sa ka ji idonka ba dadi, idan kuma abu ya yi tsanani sai ya sa idon shiga wani yanayi da ake cewa busasshen ido.

Bushashen ido:

Wani likitan ido na Japan Ekiti Goto, ya bayyana wannan cuta ko yanayi na busasshen ido da wata babbar larura ta rashin hawaye a ido, wadda take shafar miliyoyin mutane a duniya.

Bayan bushewar idon, matsalar tana kuma sa gajiyar ido da jan ido da kaikayi sannan kuma mutum ya rika jin idon ya yi masa nauyi, ba kamar yadda ya saba ji ba.

A wani lokacin idan yanayin ya yi tsanani yana shafar ganin ido, amma kuma duk da wadannan matsalolin da idon kan gamu da su a wannan yanayi ba a daukar matsalar a matsayin wata babba.

Ta hanyar amfani da kayan gwaji na zamani, Goto ya gano cewa a wannan yanayi na bushewar ido, idon yana rasa santsin da yake da shi.

Daga nan sai idon ya daina ganin abubuwa tsaf yadda ya kamata, domin hasken da yake shiga idon yana fadawa ne kan wurin da ba shi da santsi saboda haka hoton abin da ido ya kalla ba zai kasance mai kyau ba kamar yadda yake.

Haka kuma Goto ya gano cewa mutumin da yake da wannan larura yana kifta biyu linki biyu a kan yadda wanda ba shi da wannan matsala yake yi.

A kan haka ya ce yana ganin mai larurar yana yin hakan ne ba tare da ya sani ba, da nufin ganin idaon yanuna masa siffar abin da yake kallo yadda ya kamata.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Bushewar ido? Za ta iya sa a hana ka lasisin tukin mota

Za ka iya dauka cewa wannan binciken yana kawo wata hanya mai sauki ta maganin wanna larura: ko alama. Ka jarraba kikkifta idonka a ka a kai, yadda za ka iya.

Za ka ga hakan ba abu ne mai saukin yi ba a wannan zamani da muke amfani da na'urori iri-iri a ayyukanmu na yau da kullum.

Karatu da tuki da rubuta sakonni ko wasika ta wayarmu ta salula da aiki da kwamfuta na sa mu rage kifta idanuwanmu.

Wannan na nufin duka wadannan ayyuka da makamantansu suna rage mana yawan yadda muke kifta idanuwanmu.

Misali a lokacin da muke tuka mota da gudu musamman idan gudun ya wuce kilomita 100 a sa'a daya muna rage kifta idanuwanmu.

Hakan na nufin ganin mutumin da yake da matsalar bushewar ido zai ragu a wannan lokaci, da ba zai cancanci a bashi lasisin tuki ba, domin yawancin karfin ganin mai wannancuta shi ne 0.3, wato kasa da 0.7 da ake bukata mutum ya samu a Japana kafin a ba shi lasisin, a Amurka kuwa 0.5 ne mafi kankanta kafin a baka lasisin tukin mota.

Wannan ya nuna cewa wasu marassa lafiyar idon, da ke da larurar bushewar idanu, ba lalle su kasance suna gani da kyau ba a lokacin da suke tuki.

Saboda haka daga yanzu idan ka tashi daga barci kuma kagoge duk wannan kwantsar da ke idonka, watakila za ka dan saurara ka yi tunanin amfaninta.

Idan kana son karanta wannan da harshen Ingilishi latsa nan Why do we get sleep in our eyes?