Labarin zuciya a tambayi fuska

Idan kana son ka iya sanin abin da ke cikin zuciyar mutum, to ka je kusa da shi, ka tsaya ka kura wa idanuwansa ido da kyau, za ka iya sanin abin da yake sakawa a zuciyar. In ji Mo Costandi.

A wasu lokutan a kan ce, labarin zuciya a tambayi fuska, domin idanu sukan bayyana wani hali ko yanayi da mutum yake ciki wanda ba ya son ya nuna ko kuma a ce yake boyewa.

Duk da yadda kimiyyar zamani ta ke kawar da maganar tabbatar ruhin mutum, to amma duk da haka tana ganin akwai alamun kanshin gaskiya a wannan magana.

Ba kawai ido yana nuna alamun abin da mutum yake tunani ba ko yake sakawa a zuciyarsa ba, ido zai kuma iya tasiri a kan yadda muke tuna abubuwa da kuma matakin da muke dauka.

Ba a ko da yaushe muke sane da yadda idanuwanmu suke motsi ba.

Idanuwanmu na kikkiftawa a kai a kai, duk da cewa muna sane da yadda suke motsi, a yawancin lokaci ba ma sanin motsin da suke yi.

Misali idan muna karatu mukan motsa idonmu sosai da sosai da wuri muna bin kalma zuwa kalma.

Idan muka shiga daki mukan kalli cikin dakin kusan gaba daya a lokaci daya.

Akwai kuma dan motsin da muke yi da ido, lokacin da muke magana, a wasu lokutan maimakon motsin da muke yi da kai da kuma daidaita yadda muke kallon abubuwan da suke gabanmu na duniya.

Haka kuma idanuwan namu sukan yi motsi nan da can lokacin da muka kama hanyar barci, muke gyangyadawa.

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Idan mutum ya bude idonsa sosai, alama ce ta rashin tabbas

Abin da a yanzu yake kara bayyana shi ne, wani daga cikin irin motsi da muke yi da idanuwanmu zai iya bayyana abin da muke tunani a zukatanmu.

Wani bincike da aka wallafa a shekara ta 2014, ya nuna cewa, bude idanuwa sosai na da alaka da rashin tabbas(idan mutum ya bude idonsa sosai).

Wato idan mutum ba shi da tabbas a kan wani mataki ko wani abu, za ka ga ya bude idonsa kamar abin ya dan daga masa hankali, sai ka ga kwayar idonsa ta fito sosai.

Haka kuma wannan yanayi da mutum kan yi da idonsa, ka iya nuna matsayin da wani mutum zai dauka a kan wata magana ko kuma abin da zai fada.

Misali wasu masu bincike sun gano cewa idan suka lura da lokacin da mutum ya buda idonsa sosai a lokacin magana, za su iya hasashen lokacin da mutumin da ke da natsuwa da

kiyayewa a kan al'amura, zai iya cewa ''e'' (wato ya amince da abu).

Kallon idon mutum zai iya taimakawa wajen sanin lambar da ke zuciyar mutumin.

Tobias Loetscher da abokan aikinsa a Jami'ar Zurich, sun tara mutane 12, suka yi nazari kan motsin idanuwansu a lokacin da suke warware jerin lambobi 40.

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Wace lamba nake tunani?

Masu binciken sun gano cewa wurin da idon mutum yake karkatawa da kuma motsin idon sun zo daidai da hasashen ko lambar da mutum ke shirin fada ta fi ta baya girma ko ta kai ta girma ba, kuma nawa ne bambancinsu.

Idon kowanne daga cikin mutanen 12, yakan daga sama kuma ya karkata zuwa dama kafin su fadi lamba mai girma.

Kuma idan karamar lamba ce, sai a ga idon ya yi kasa kuma ya karkata zuwa hagu.

Yawan girman karkata idanun daga wannan bangare zuwa wancan, shi ne daidai girman bambancin lambobin.

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

...babbar lamba saboda sama nake kallo kuma bangaren dama

Wannan na nufin a kwakwalwarmu mun danganta girman lamba, wanda abu ne da ba ma gani a zahiri da girma ko kankantar motsi(na ido).

Sai dai binciken bai gaya mana cewa wanne ne ya zo a farko ba: ko tunanin wata lamba shi ya sa sauyin wurin da idon yake, ko kuma wurin da idon yake shi yayi tasiri a kan tunaninmu.

A shekara ta 2013 wasu masu bincike a Sweden sun wallafa shedar da ke nuna cewa, wurin da idon yake shi yayi tasiri a kan tunaninmu.

Masu binciken sun yi amfani da dalibai 24, inda suka sa kowanne ya lura da abin da ke faruwa kan wasu abubuwa a cikin wata kwamfuta(a gefe daya na gilashin kwamfutar).

Daga nan ne kuma aka bukace su, su saurara su ji jerin abubuwan da ake fada a kan wasu daga cikin kayan da suka gani a kwanfutar, kamar a ce, '' motar na fuskantar bangaren hagu

ne'', kuma aka sa, su zaba da sauri da sauri ko duk maganar da aka fada akan abin da suka gani haka ne ko ga haka ba ne.

Wasu daga cikin daliban an ba su damar su motsa idanuwansu, wasu an ce su tsayar da idanuwansu a kan wata alamar gicciye da ke tsakiyar kwamfutar, ko kuma a kusurwar kwamfutar inda aka nuna abubuwan.

Masu binciken sun gano cewa wadanda aka ba su damar su motsa idanuwansu sun fi wadanda aka sa su tsayar da idanuwansu wuri daya samun nasara.

Haka kuma wadanda aka sa, su tsayar da idanuwansu suna kallon kusurwar gilashin kwamfutar da aka nuna abubuwan kafin a dauke su, sun fi wadanda aka sa su kalli wata kusurwar kokari.

Wannan ya nuna cewa idan idanuwan mutum suka kasance babu bambanci tsakanin inda suke a lokacin da ake nuna wa mutum abu da kuma inda suke lokacin da ake yi wa mutumin jarrabawa bayan an dauke hotunan abin, mutum ya fi tuna abin da aka tambaye shi game da hotunan abubuwan.

Ana ganin hakan watakila ta kasance ne saboda motsin ido yana taimaka mana wurin tuna (kadan daga) yadda abubuwa suke a wuri a lokacin da muke kallonsu.

Asalin hoton, Thinstock

Bayanan hoto,

Wani motsin idon ya kan taimakawa mutum tuna wani abu

Wannan motsin ko kiftawar da ido ke yi abu ne da zai iya faruwa ba tare da mun sani ba.'' Idan mutane suna kallon wasu abubuwa da suka taba gani, idanuwansu yawanci

na mayar da hankali ne a kan bayanai ko abubuwan da suka gani a baya, ko da kuwa ba su haddace ko iya tuna abin da suka gani a can bayan ba.'' In ji Roger Johansson, masani kan

tunanin dan adam a Jami'ar Lund, wanda shi ne ya jagoranci binciken.

Za a iya amafani da kallon motsin idanuwan mutum a san matsayinsa ko hukuncin da zai dauka, kamar yadda wani nazari da aka yi kwanannan ya nuna.

Masu bincike sun tambayi mutane wasu tambayoyi masu sarkakiya ta kwamfuta kamar haka,'' ko akwai damar da mutum zai iya aikata kisan kai?''

An kuma nuna wa wadanda ake jarrabawar da su zabin amsoshi biyu kamar haka, ''e akwai'' da '' a'a babu'', ta hanyar bin motsin idanuwansu da kuma cire amsoshin kai tsaye bayan

wanda ake yi wa jarrabawar ya dau wani lokaci yana kallon daya cikin zabin amsoshin, masu binciken sun gano cewa za su iya sanin cewa ga amsar da mutumin zai bayar.

Kwararrun masu tallata kaya za su iya amfani da motsin idanu, su sa mutum ya sayi kayansu.

Masanin kimiyya a Kwalejin Jami'ar Landan Daniel Richardson, ya ce,'' ba wani bayani da muka kara musu, mun jira lokacin da za su yanke shawara ne kawai, sai muka datse tunaninsu a

daidai wannan lokaci, muka sa suka sauya shawara.''

Masanin ya kara da cewa,'' to wannan shi ne abin da kwararru a tallata kaya suke yi, wanda watakila sun san da hakan, kuma suke amfani da shi wajen shawo kan mutane su sayi kayansu.''

Ya ce,'' mun dauki mutanen da suka iya magana da cewa, su suka fi iya shawo kan mutane, to amma watakila su ma suna lura da yanayin lokacin yanke shawara na mutum ne.''

''Watakila kwararrun masu tallata kaya za su iya gane daidai lokacin da zuciyar mutum take karkata zuwa ga wani matsayi ko wata shawara daga nan sai su yi ma ragi ko su sauya yanayin cinikin ta yadda za ka amince.''

Bazuwar manhajar sanin motsin idanun mutum ta wayar salula ta komai-da-ruwanka da kuma sauran na'urorin tafi-da-gidanka, ya kara jaddada yuwuwar sauya ra'ayin mutane a fakaice

ko kuma ta hanyar na'ura. In ji Richardson.

Ya ce, ''idan kana sayen kaya ta intanet, za a iya amfani da wannan manhaja a sauya maka ra'ayi ta hanyar yi maka tayin wani sauki, misali, yayin da na'urar ta ga ka dena kallon kayan da

kake tunanin saye, sai nan da nan ta kawo maka wata garabasa, ta cewa idan ka saya ba za ka biya kudin dako ba.''

Asalin hoton, Thinstock

Bayanan hoto,

Ba ka bukatar na'ura domin sanin tunanin mutum

A don haka motsin ido abu ne da zai iya bayyana matsayinmu da kuma yin tasiri a kan tunaninmu da hukuncinmu, sannan ya tona mana asiri.

Wannan ilimi ne da zai iya bamu hanyoyin inganta tunaninmu, amma kuma zai sa mutane su gano lagonmu ta yadda za su iya juya mu.

Richardson ya ce,'' ido kamar taga ce ta sanin yadda tunaninmu yake, kuma ba ma la'akari da yawan bayanan da suke fitarwa namu.''

''Ido zai iya bayyana abin da mutum ba zai so a sani game da shi ba kamar ra'ayinsa na wariyar launin fata.''

Masanin ya ce, ''yana ganin wani lokaci da za a zo ana amfani da manhajar bin motsin idanuwan mutane, da za ta san abin da mutum yake son dannawa a wayarsa ta danna masa kai tsaye.

Amma kuma idan aka bar ta a kunne a kowane lokaci za a iya amfani da ita a san duk wasu abubuwa naka, wanda wannan zai sa wasu su rika sanin wasu abubuwa game da kai ko ma

tunaninka abin da ba za ka so wani ya sani ba.''

Masu iya magana suka ce wai, '' naka shi ke bayar da kai'' in ji gafiya an kama ta a jela. Kuma ''labarin zuciya a tambayi fuska.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How the eyes betray your thoughts