Ko mutane za su yi ta kara tsawo?

Hakkin mallakar hoto Getty

A yanzu mun fi tsawo idan aka kwatanta da shekaru 150 baya. Ya aka yi hakan ta kasance tambayar da Adam Hadhazy ya yi ke nan, kuma ya mutane za su zama a shekaru 100 nan gaba?

Dan-adam ya sauya a shekaru 150 da suka gabata Yawan mutanen duniya ya karu daga bliyan daya zuwa biliyan bakwai.

A kasashen da aka cigaba shekarar da yawancin mutane kan rayu ta karu daga 45 a tsakiyar shekarun 1800 zuwa shekaru 80 a yanzu.

Bayan wannan ma kuma siffarmu ta sauya inda yawancin mutane yanzu sun fi tsawo idan aka kwatanta su da na da.

Tsawon yawancin mutane a kasashe masu masana'antu ya karu daga Birtaniya zuwa Amurka zuwa Japan, inda suka karu da kusan santimita 10(centimetres)

A game da karin tsawon da mutane suke yi, wata kasa daya ta wuce saura.

A yau matasa maza 'yan kasar Holland sun kai tsawon kusan santimita 184, yayin da mata kuma suka kai kusan santimita 170, dukkanninsu ke nan sun zarta sa'oinsu na tsakiyar karni na 19 da santimita 19.

Farfesa John Komlos(ritaya) na Jami'ar Munich, ya ce, wannan bambanci ne da zai ba mutane mamakin gaske.

To me ya sa mutane musamman dan kasar Holland suka fi tsawo a yanzu?

Ko hakan na nufin mutane za su ci gaba da kara tsawon, idan kuma hakan ne har zuwa yaushe zai iya tsayawa?

Ko jikokinmu da za su kasance suna rayuwa a duniyar wata da sauran duniyoyin sama za su rika tunanin mu kakanninsu da muka rayu a doron kasa kamar wasu halittu na tatsuniya?

Tambayoyi irin wadannan su suka sa Komlos a shekarun 1980 ya bullo da wani fagen nazari na binciken yadda karuwa da raguwar al'umma ta dogara ga bunkasa ko raguwar tattalin arziki da kuma yanayin zamantakewar jama'a (anthropometric).

A wannan fanni Komlos ya bincika takardun tarihin daukar mutane aikin soji, wadanda suka kunshi bayanin tsawon mutane domin sanin dangantar hakan.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutumin da ya fi tsawo a China Zhang Juncai yana hada tafin hannunsa da na yaro dan shekara bakwai

Binciken ya bayyana cewa kari da raguwar da ake samu a tsawon mutum ya dogara ne ga abubuwa biyu: abinci da kuma cuta, musamman ma a lokacin yarintar mutum.

Idan yara ba sa samun wadataccen abinci mai kyau su ci ko kuma ba sa samun sinadaran abinci masu gina jiki saboda cutar gudawa, wannan zai hana jikinsu yin tsawo da habakar da ya kamata ya yi.

''A takaice'' in ji Farfesa William Leonard na Jami'ar Northwestern a Illinois, ''muhimman abubuwan da ke sa jikin mutum ya yi girma su ne, ingantaccen abinci da lafiya da kuma kyakkyawar rayuwa.''

Tarihi yana cike da misalan wannan dangantaka ta tsawon mutum da lafiyarsa.

A yankin Turai ta Yamma, a lokacin kusan karshen karni na 15 bayan annobar da aka yi wa lakabi da Black Death, wadda ta hallaka kusan kashi 60 cikin dari na yawan jama'ar kasashen,

mutanen da suka tsira sun samu yalwar abinci da rashin cunkoso, wadanda duka sun taimaka wajen rashin yaduwar cutuka.

Mutane sun rika yin tsawo inda Turawan Ingila a lokacin suka gaza da santimita 4 kawai idan aka kwatanta su da 'yan kasarsu na yau.

Hakkin mallakar hoto Getty

To amma a Turai ta karni na 17 an samu raguwar tsawon mutane sosai. A lokacin yawancin mutanen Faransa ba su wuce santimita 162 ba.

A lokacin tsananin sanyi ya rage amfanin gona, rikici ya barke a ko ina, kama daga yakin basasa na Ingila zuwa yakin Louis na 16(Louis XIV) na Faransa da kuma yakin shekara 30 na inda a yau ake kira Jamus.

Komlos ya ce,'' Turai ta kacaccala kanta ne kawai a wannan lokaci na karni na 17.''

Haka kuma lokacin bunkasar masana'antu na karni na 18 wanda ya jefa jama'a yanayi na rayuwa a gidaje masu kazanta da cutuka a birane shi ma ya dakushe girma mutane.

Amma shekarun gaba na karni na 19 tawayen jama'a ya haifar da ingantaccen tsarin noma da samar da ruwan famfo da kuma tsabta a birane da kuma bunkasar tattalin arziki. Yankin yammacin Turai ya ci gaba da wannan bunkasa ta tattalin arziki tsawon shekara da shekaru kuma har kawo yanzu.

Wannan alaka ta tsawon mutum da lafiyarsa har yau din nan tana nan a zahiri.

A misali irin na yau ka duba Koriya ta Arewa da ta Kudu, inda ta Arewa take matsayin kasa ta 188 daga cikin jerin kasashe195 a kan cigaban jama'a na Majalisar dinkin duniya, wanda wannan ma'auni ne na tsawon ran mutane da samunsu da kuma iliminsu.

Babban mutum a Koriya ta Arewa bai kai takwaransa na Koriya ta Kudu ba tsawo da kusan santimita 3 zuwa 8.

Kuma Koriya ta Kudu ita ce kasa ta 15 a shekara ta 2014 a jerin kasashen Majalisar dinkin duniya, wadanda rayuwar mutanensu ta ci gaba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Duk da haka a wasu kasashen masu karfin masana'antu, kamar Amurka, karin tsawon tun karni na 19 ya tsaya.

Tun daga yakin juyin juya hali na karni 18 zuwa yakin duniya na biyu a tsakiyar karni na 20, Amurkawa sun fi takwarorinsu na sauran kasashe masu masana'antu.

Amma kuma a yau yawancin Amurkawa maza sukan kai tsawon kusan santimita 176 mata kuma sukan kai santimita 163, wanda hakan shi ne kusan tsawon Dan-Amurka a shekaru 45 da suka wuce, wanda kuma bai kai tsawon dan kasar Holland na yau ba.

Leonard ya ce, tsawon yawancin Amurkawa a yau bai wuce yadda yake ba sosai a tsakiyar shekarun 1970 da kuma karshen shekarun 1960 ba.

Ya ce, ''muna magana ne a kusan shekaru 40 zuwa 50.''

Ta yaya aka yi mutanen arewacin Turai suka fi tsawo ke nan?

Komlos ya yi imanin bambancin abinci mai gina jiki da kula da lafiya a Amurka idan aka hada da tsarin da ya fi kyautatawa jama'a a kasashen Turai da suka ci gaba shi ne sanadin bambancin.

Miliyoyin Amurkawa ba su da inshorar kula da lafiya kuma ba sa samun damar ganin likita sosai.

Mata masu juna biyu ba sa samun kulawa sosai a Amurka,amma takwarorinsu a Holland har gida ma'aikatan jiyya suke zuwa duba su kuma a kyauta. In ji Komlos.

Kuma kari a kan wannan kashi daya bisa uku na yawan Amrkawa suna da kiba, saboda cin abinci na gwangwani da sauran tarkacen abinci na kwalam da makulashe.

Abincin kanti mai matukar maiko zai iya dan dakushe karuwar tsawon mutumin da yake girma.

Hakkin mallakar hoto Getty

Komlos ya ce,'' shan Coca-Cola da cin abincin McDonald da makamatansu ba za su sa ka yi tsawo kamar 'yan Holland ba, a takaice,''

Ka da a manta da kwayar halitta:

Ya zuwa yanzu mun duba tasirin rayuwar yau da kullum maimakon halitta wajen samar da tsawon mutum.

Kamar duk wata dabi'a ko halitta ta dan-adam kwayoyin halitta suna da irin rawar da suke takawa wajen girmansa.

Magidantan masu tsawo kusan a iya cewa suna da dukkanin kwayoyin halitta da ke sa tsawo.

Amma duk da haka irin yadda wasu mutane ke tsawo a yanzu ba za a ce lalle abu ne da ya danganci kwayoyin halitta ba.

Hakkin mallakar hoto AFP

A zahirin gaskiya, idan aka yi la'akari da nazariyyar Charles Darwin ta cewa halittar da ta fi dacewa ko wadata ta fi haihuwa, kishiyar hakan ne ke faruwa da mutanen yau.

Za ka ga iyalan da suke cikin fatara da talauci, ba su da lafiya sosai ko harkar kula da lafiya mai inganci kuma ga su gajeru sun fi haihuwar 'ya'ya a kan iyalan da suke da wadata.

Misali Nijar wadda daya ce daga kasashen da suka fi talauci da rashin cigaba a tana da mata da suka fi yawan haihuwa, inda mace daya ke haihuwar sama da 'ya'ya bakwai.

Saboda haka Leonard ya ce,''to ka duba za ka ga yawanci bambancin tsawon ya dogara ne da bambancin karfin wadata da abinci mai kyau.''

''Maimakon a danganta karuwar tsawon yau da kwayar halitta sai dai a ce hakan na kasancewa ne saboda kwayoyin halittar suna samun duk abin da suke bukata daga wurin mutumin da yake da wadata,'' in ji Leonard.

Komlos ya kara da cewa,''babban darasin shi ne muhalli yana taka rawa a jikin mutum. Ba kwayar halitta ba ce kawai.''

Sha'awar dogo: Bayan duka wannan abu ne da ya kamata a sani cewa tsawo halitta ce da ke daukar hankali da ake so a al'ummomi da dama. Haka kuma ana daukar tsawo a matsayin halitta da ke karawa mutum damar samu.

A wani bincike da aka yi a 2004 an gano cewa a duk inci daya na tsawo da mutum yake da shi da ya wuce tsawon yawancin mutane ana ganin mutum zai iya samun karin dala 789 a duk shekararsa ta aiki(kusan dala 976 ko fan 625 a yau).

To sai dai ba a kullum ake kwana a gado ba, domin duk abin da yake da amfani ta wani bangaren kuma zai iya samun rashin amfani.

Tsawo ba lalle yana nufin idan mutum yana da shi yana da damar samun karin dukiya ba ke nan, idan muka ajiye 'yan wasan guje-guje da tsale-tsalle da masu tallata tufafi ko kayayyaki a gefe ba.

Shugabannin manyan kamfanonin kasuwanci na duniya ba dukansu ba ne dogaye, kuma a wani lokacin ma tsawon naka sai ya zama illa, ta yadda idan ka je wucewa ta wata kofa ko mota sai ka yi ta fama.

Haka kuma mutane masu tsawo sun fi hadarin kamuwa da wasu cutuka kamar bugun zuciya da ciwon mahadar jiki.

Robert Wadlow, wanda shi ne mutumin da a hukumance aka sani ya fi kowa tsawo a wadanda suka rayu babban misali ne.

Sakamakon matsalar kwayar halitta da yake da tsawonsa ya kai mita 2.72 ko kafa takwas da inchi 11.

Dole sai da ya rika daura abin da zai rika taimaka masa na musamman wajen tafiya idan ba haka ba ba zai iya tafiya ba, kuma kujin da ya fito masa sakamakon irin wannan abin da ya yi amfani da shi wanda ba I dace da kafarsa ba ya rasu yana da shekara 22.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Robert Wadlow

Bisa ga dukkanin wadannan bayanai da aka gabatar Komlos yake ganin watakila dan-adam ya kai karshen tsawonsa.

Ya ce,'' a wurina mutanen Holland za su ba ka misalin karshen tsawon da mutane za su kai, domin sun kai kusan karshen tsawon da za mu iya kaiwa idan komai ya kai daidai yadda muke bukata.''

Cimma wani sabon tsawon:

Idan mun kai karshen tsawonmu na wannan doron duniyar to ina kuma maganar na sauran duniyoyi kamar ta wata da Mars da sauransu?

Ko mutanen da za su zauna a irin wadannan duniyoyin na wajen wannan da muke ciki za su fi mu tsawo.

Duk da cewa ba za mu san ainahin yadda lamarin yake basai mun je can, za mu iya sanin dan kadan daga hakan ta hanyar 'yan sama jannati.

Hakkin mallakar hoto mdrs esa
Image caption Tashar 'yan sama jannati ta duniya

Zama na 'yan watanni a tashar 'yan sama jannati ta (ISS) da ke wajen duniyar nan tamu, saboda yanayi ne na wurin da ba wani abu da ke da nauyi, ya sa mutane suka

kara dan tsawo ko da ike na wucin-gadi ne, domin tsawonsu ya dawo yadda yake bayan da suka dawo duniya da 'yan kwanaki.

To amma Leonard ya ce yana ganin rayuwa a duniyar Mars abu ne da zai sa tsawon mutum ya ma ragu. Domin Mars hamada ce mai kankara wadda babu iskar shaka.

Kuma duk wata rayuwa da mutum zai yi a can sai dai ya yi ta a cikin tanti ko daki, bugu da kari kwanaki a duniyar ta Mars sun fi na wannan duniyar tamu tsawo, wanda hakan zai jirkita agogo ko lokacin da jikin mutum ya ke wajen tafiyar da ayyukansa cikin sa'oi 24, in ji Leonard.

Hakkin mallakar hoto esa nasa

Masanin ya kara da cewa, a kawar da duk wani jin dadi na wannan duniya tamu, rayuwa a duniyar sama ko wata duniya ta daban kamar Marsmutanen da za su rayu a can za su iya gajarcewa idan aka kwatanta su da na duniyar nan.

''In dai komai ya kasance yadda yake a yanzu,'' in ji Leonard'' ina ganin girman mutum zai ragu a duniyar Mars maimakon ya karu.''

Idan kana son karanta wannana harshen Ingilishi latsa nan Will humans keep getting taller?