Lakantar manta abu a zamanin fasaha

''Idan ba mantuwa ba za a taba rayuwa ba.'' Wannan kalamin Friedrich Nietzsche ke nan a shekarar 1874. Tom Chadfield ya nitsa cikin wannan magandomin ganin yadda lamarin yake.

Nietzsche yana ganin za a kai wani lokaci da wani gagarumin cigaba zai kawar da wasu abubuwa a manta da su.

To idan aka yi maganar mantawa da abu a shekara ta 2012 intanet ita ce wannan gagarumin cigaba da yake cikin kowane daki.

A yau akwai bayanan kusan komai da muka yi tunani ko muka fada ko muka gani ko muka yi ko ma muka so a ce ba mu yi ba.

Wadannan bayanai suna nan tare a shafukan sada zumunta ko akwatin email ko shafukan matambayi-ba-ya-bata (search engines) da makamantansu.

Ko muna so, ko ba ma so ga alama mun kama hanyar tabbatar da fargabar da Nietzsche ya yi, cewa zamani zai kawo cigaban da zai sa a manta da abubuwa.

Abin da ya ja hankalina ba wai yadda a yau ake iya adana bayanai a intanet ba ne, a'a, abin shi ne, abubuwan da fasahar adanawar ta intanet za ta kawar da sunan adanawa.

A kwai kuma wani abin mafi muhimmanci da wannan cigaba da ake gani (wanda ya zama kamar na mai haka rijiya) zai shafa, wanan kuwa shi ne yadda muke samo kalmomi da basira ko tunanin yin abu tun da fari, wanda wannan cigaba zai gusar gaba daya.

A kwanan nan na je wurin adana kayan tarihi na Tate Modern da ke Landan, domin halartar nunin kayan tarihi na rayuwa da ayyukan Yayoi Kusama( mai ayyukan fasaha na al'ada).

A yayin baje kolin abubuwan da suka ba ni mamaki da daukar hankalina sun hada da yanayin kwarewa da siga ta ayyukan wannan fasiha da kuma takardu da wasikun da ta rubuta da hannunta zuwa abokanta da sauran jama'a da hukumomi.

Fasihan da aka haifa yau ba shakka za su fi wadanda aka haifa a 1979 ballantana wadanda kuma aka haifa a 1929 kamar Kusama, cin moriyar bayanai da abubuwan da ake adanawa a intanet da sauran hanyoyin fasaha na zamanin nan na kwamfuta.

Amma kuma duk da haka, irin abubuwan da na gani a cikin gilashin nan a lokacin baje kolin na kayan wannan fasiha(Kusama) a Tate, tuni sun zama tarihi hatta tarihin ma da suke tattare da shi ya bace.

Wato tarihin wasikun da aka buga da kuma rubutun hannu da aka gyara wasikun da mamakantan irin wadannan abubuwa, ba za mu sake ganinsu ba.

Hatta karanta rubutu kamar wannan da kake yi a yanzu, a kwanfuta ko ta waya, da ma yadda ake yin rubutun tun da farko kafin ya zama yadda kake karanta shi bayan an gama komai ya kua daga tarihi.

Hannun marubucin rubutun, wanda yake buga wadannan kalmomi a kwamfuta a wani wuri da ke kusa da birnin Landan, wanda kuma bayan rubutawar a kwamfuta zai yi 'yan gyare-gyare da hannunsa, za ka san da shi ne kawai ta hanyar rashinsa.

Idan har yanzu kana ganin wannan ba wani abu ne mai girma ba da aka rasa, ka duba labarin da Farfesa Sherry Turkle ta Babbar makarantar fasaha ta Massachusetts MIT, da ke Amurka ta rubuta a wani littafinta mai suna Alone Together a shekarar 2011.

Malamar ta lura da wata dabi'a ce wadda ba ta saba gani ba, inda, dalibai a tsakaninsu suke ware daya daga cikinsu da ya fi iya rubuta sakon waya(text, sms) ko kokari ya rubuta a madadinsu.

Ko kuma wani ko wata da yake son ya rubuta wani sako na waya zuwa ga saurayi ko budurwarsa, wato kamar abin da ake da shi a da na wasikar soyayya, a misali sai ya sa wani da ya kware da haka ko kuma ya dauki tsawon lokaci yana ta kokarin ya rubuta wannan sako na haruffa 140.

Ba wai rashin gani a zahiri abubuwan da suka wakana kafin a kai ga rubuta sakon na karshe ba, rashin ganin takardar sakon a zahiri da kuma rashin alamar cewa wannan mutum ne ya rubuta da kansa ba, wani babban bangare ne na shi kansa rubutun ko sakon.

Ba karamin abin mamaki ba ne, a ce babu wata alama ta sauya tunani da sauya ra'ayi misali a lokacin rubuta sako ko wasika da makamantansu da dan-adam kan yi, a kafar sadarwar da ke ikirarin hada sauri da kuma ajiye abu dindindin a matsayin amfaninta ba.

Ba wanda yake tsammanin wata wasika ko littafi ko kuma wani zane ya bayyana gaskiya gaba dayanta.

To amma ita kanta hanyar ta zamani, wato shafukan sada zumunta na intanet-''me kake yi a kai''?

Abu ne mai sauki ka yarda da wadannan abubuwa da ke fito da su ka yi magana a kan fasahohin zamani marassa kyau ko masu illa kamar yadda wani zai dauke da kuma irin illolin da suke haifarwa.

Maganar ita ce ba wai a ko za mu samo wani tsari ne mai kyau ba ta yadda za a iya rika wasu abubuwan ba.

Abin shi ne yadda za mu amfana sosai da abin da muke da shi a hannu.

Wanda wannan abu ne da zai fara cewa dole ne mu rika sani tare da la'akari da illoli ko gazawar fasahohin zamani da kuma gazawar mu kanmu.

Kamar yadda Nietzsche ta sani karara ba za a iya yarda da tunani ko haddar mutum ko niyyarsa ba gaba daya.

Ko kuma kamar yadda Mark Twain, wanda shi ma wani babban masani ne na lokacinsa ya ce, ''lokacin da nake karami zan iya tuna komai, ko ya faru ko bai faru ba.''

Idan za mu rika dan sa shakku a kan abubuwan da muke gani a intanet kuma watakila mu dan rage hanzarin da muke na kwalliyar da wasu za su ganmu da kyau, watakila mu lakanci yadda za mu rage mantawa da abubuwa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Mastering the art of forgetting in the digital age