Me ya sa muke son abinci sosai?

Hakkin mallakar hoto Getty

Akwai abinci iri-iri da kusan kowane mutum zai ji a ransa ga wani da ya fi so a wani lokaci, kuma idan ba ya same shi ba, sai ya ji ba dadi ko da kuwa abincin nan ba wani na a-zo-a-gani ba ne.

To me ya sa jikinmu ke fama da irin wannan takura? Veronique Greenwood ta bincika.

Ba abin da ya fi dadi kamar ka samu taliya ruwa ruwa da zafinta ta sha romon naman shanu da kuma kayan hadi iri daban daban. To amma dai ba da ni ba a wannan dabdala yanzu domin

ni kam na sha ta a da,inda har na rubuta yadda wanna abinci ya taimaka min a lokacin da nake budurwa.

Amma a gaskiyar lamari har yanzu ina matukar san wanna abinci musamman ma idan na gaji ko ba ni da lafiya.

Watakila kai ma kana da irin wannan sha'awa ta wani abinci a tarin irin abincin da kake ci, sha'awar da ta shafe duk wata sha'awa taka ta abinci, abincin da yake kwantar maka da hankali

ya sa ka nishadi, wanda saboda tsananin shiga ranka za ka iya tunanin yadda siffarsa take a kwakwalwarka a yayin da kake jiran jirgi a tashar karkashin kasa a kan hanyarka ta zuwa

gida ko kuma kana tunkarar abincinka na dare a hankali a hankali tsakanin ababan hawa.

Ba duk abinci ba ne da ka zaku ka samu wanda ya shiga ranka yake sananne a wurinka.

Ko akwai lokacin da ka taba samun kanka a irin wannan hali da ma ka manta yadda abincin da kake so yake.

An ce mata masu juna biyu sukan yi sha'awar abinci wanda yake kusan a ce na daban. Dukkan wani abinci dai da ya shiga ran mutum wanda ya amsa sunansa yana da wannan tsanani a

ran mutum. Za ka ji kamar wasu sakonni ne masu amfani daga jikinka. Amma kuma ba haka suke ba.

Farfesa Eva Kemps ta Jami'ar Flinders a Adelaide da ke Australia, ta bayyana cewa, duk da yadda aka dade ana ta kokarin danganta sha'awar wani abinci da mutum kan yi da rashin wasu

sinadarai, ina bukatar wannan alewar chakuleti ne ba don saboda wasu dalilai na jiki ba.

Wani fitaccen dalili daya na tsananin sha'awar alewar chakuleti, misali, wadannan abubuwa da suke tasowa da mutum wannan tsananin sha'awa shi ne ba su da sinadarin magnesium

wanda chakuleti za ta iya bayarwa.

To amma kuma kayan abinci da yawa da suka hada da alaiyahu suna da sinadarin magnesium fiye da chakuleti wadda ita ce abar ci da ta fi shiga ran mutane a kasashen Yamma, na

Turawa. ''To sai dai kuma abin mamakin shi ne mutane ba sa tsananin bukatar alaiyahun.'' In ji Kemps.

Tasirin kwayoyin halitta

Akwai abubuwa dama masu kama da wannan. Amma matukar sha'awar wani abinci ana ganin tana da alaka da yanayin mutum da kuma wasu dalilai na mu'amullar mutum da suke tasowa

da mutum sha'awar ta hanyar tuna masa da wani abu na baya.

Yayin da ake ganin yunwa za ta iya sa mutum ya ji irin wannan sha'awa, ita yunwa ana danganta ta da abin da ya shafi tunanin mutum maimakon abin da ya shafi jikinsa. Kasancewar mutum cikin yanayi na damuwa ko kadaici ko zakuwa da makamantansu wanna ka iya jawo masa wannan yanayi na matukar sha'awar abincin in ji Kemps.

Hakkin mallakar hoto reuters

Abinci a matsayin abin da ke sa mutum ya ji dadi ba ya bayyana dalilin da ke sa mutum ya tsinci kansa a wannan yanayi na matukar bukata, sai dai kawai saboda mukan ji sha'awar abincin da muka sani a baya ne.

Haka kuma mukan yi matukar sha'awar abin da ba mu dade ba da ganin hotonsa ko muka gani a muhallinmu.

Ba wai cewa babu alakar aikin jikin mutum ba ne a cikin wannan abu. Bisa kididdiga, an gano cewa mata sun fi samun kansu a wannan yanayi na sha'awar wani abinci a cikin kwanakinsu

na kafin al'ada, da kuma cewa wannan sha'awa ta mata masu juna biyu ita ma tana nuna cewa da alama akwai wasu kwayoyin halitta da suke jawo hakan.

Amma ko wannan abu ne da yake taso da wannan sha'awa ta abinci ko kuma kawai wata hayaniya ce a jijiyoyin mutum Kemps ba za ta iya tabbatarwa ba.

Kuma a zahirin gaskiya wannan sha'awar abinci abu ne da ya hada komai da kowa ba kawai sanadiyyar juna biyu ba ko al'ada ta mata ba.

Ko ma menene asalinta sha'awar abincin wata aba ce da ke matukar takura wa mutum. Bincike da dama da aka yi ya nuna cewa aba ce da ke da wuyar sha'ani wajen jarrabata kan wani bincike da ya shafi kwakwalwa.

James Wannerton masanin dan dano da aka yi wa tambayoyi a wanna shafi kwanannan, ya ce yana gamuwa da wannan matsala ta sha'awar wani abinci a lokuta da dama. Duk da cewa ba ya son abincin da ya kejin sha'awar ta sa, ala dole yake tanadarsa ya ci domin kawar da wanna tunani ko sha'awa daga ransa idan ta taso.

Domin fahimtar yadda wannan lamari na matukar sha'awar wani abinci yake domin sanin yadda za a iya dakile shi, Kemps da abokiyar bincikenta Marika Tiggeman sun yi nazarin yadda lamarin yadda ake ji.

A nazarin da suka gudanar sun bukaci mutane 130 da su tuna wani da lokaci suka shiga wannan yanayi, su rubuta daki-daki yadda ya kasance, ta yadda abin ya fara da yadda suka bullo wa lamarin.

A binciken sun gano cewa mutane ba sa tunani a kan wani sauti ko wani abu da za a taba, inda suka gano cewa abin da ke da tasiri a ciki sosai shi ne ganin yanayin siffar abincin da kuma tunanin dandanonsa da kanshinsa.

Sun yi tunanin ko sanya mutane su yi tunanin siffar wani abu da ba abinci ba kamar bakan-gizo ko lambun furanni hakan zai iya sa su yi maganin sha'awar tun daga farkonta.

Kamar yadda sakamakon ya kasance, wannan na samar da hotunan ko siffa ya rage tsananin sha'awar.

Wani rukunin masu binciken kuma ya gano cewa zai iya saukakawa mutane wannan sha'awa ta hanyar sa mutum ya yi wani wasan bidiyo na kwamfuta (tetris) ta yadda zai dauke masa

hankali , kamar yadda Kemps ta ce kallon wasu hotuna na talabijin ma zai iya yin hakan.

Kemps da abokan aikinta a yanzu suna shirya yadda za sujarraba wani nazari da zai iya dauke hankalin mutum daga wannan saha'awa tun kafin ta yi tsanani.

Idan wannan sha'awa ta fi karfin mutum, ta zama kullum tana taso wa mutum, ta haka za ta iya shafar lafiyarsa, saboda cin abincin da sha'awar ke so na nufin mutum zai tara maiko a

jikinsa wanda hakan wata illa ce.

Sai dai idan wannan sha'awa ta kasance tana tasowa mutum ko da yaushe Kemps tana da shawara ga wannan mutum. Shawar ita ce,'' abin da ya fi dacewa kawai shi ne ka biya

bukatarka kawai domin hakan ya fi''

''Idan sha'awar ta cigaba da kara karfi a jikinka, za ka zamar mata jiki kai ma.''

Idan kana son karanta wanna a harshen Ingilishi latsa nan Why we want food so much it hurts