Yadda harshen Ingilishi ya zama shirme

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ka ga yadda mai son rubuta kalmar 'Excellence' ya kare

James Harbeck ya bincika dalilin da ya sa harshen Ingilishi yake da wahala a rubuta shi da kuma abin da ya sa za mu dora wa kanmu laifin hakan.

Watakila ka taba ganin wakar da Gerard Nolst Trinite ya rubuta mai suna The Chaos.

Ita dai wannan waka ta kunshi kusan kalmomi 800 wadanda ke ba wa mutum matukar haushi saboda rashin takamaimai wani kyakkyawan tsarin rubuta su.

Shi dai rubutun kalmomin Ingilishi wani abu ne da yake kamar irin wasan kwamfutar nan wanda duk yadda ka kai da kokarinka, ba za ka yi nasara ba, a karshe, sai ka fadi.

To amma duk wannan tarkacen shirme sun kasance ne saboda wasu dalilai na dan-adam.

Matsalar ta fara ne da harafin harshen shi kansa, domin gina tsarin rubutu na harshen Ingilishi ta hantar amfani da haruffan harshen Latin, duk da cewa harsunan biyu ba su da dangantaka ta wajen furuci, kamar gini ne da tubalin toka.

To amma daga Tlingit zuwa Czech sauran harsuna da dama wadanda ba su yi kama da Latin ba, suna dacewa da samfurinsu na harufan harshen Latin din.

Idan haka ne to me ya faru da Ingilishi nasa ya zama daban?To shi kam,lamarinsa abu ne da ya kunshi kutse da sata da kuskure da alfahari da lalaci da sauransu.

Laifin wadannan matsaloli ya rataya ne a wuyan mutane, wadanda suka hada da kai da ni, da masu karatu, kasancewarmu masu hadama da lalaci da kuma girman kai.

Mamaya da sata

Bari mu fara da handama: mamaya da sata. A karni na farko na shekarar miladiyya(AD) Rumawa sun mamaye Birtaniya inda suka shigar da harufansa na rubutu.

Sai kuma karni na bakwai, inda Turawan Latin da na hadakar Jamus da Holland da Denmark suka karbe iko da Birtaniyan suka kuma shigar da harshensu.

Farawa da karni na tara Turawan kasashen Denmark da Sweden da Norway wato yankin da ya fi sanyi a Turai sun kame wasu sassa na Ingila suka kuma shigar da wasu kalmomi kamar 'they wadda ta maye 'hie'.

Sai kuma mutanen Arewacin Faransa da suka kama kasar a shekarar 1066 inda su kuma suka maye yawancin kalmomin Ingilishin da na Faransanci, wadanda suka hada 'beef' da 'pork' da 'invade' da 'tongue' da 'person'

Hakkin mallakar hoto gl archive alamy
Image caption Zanen yadda mutanen Faransa suka ci Birtaniya da yaki a 1066

Bayan da Turawan Ingilan suka kori na Faransan da suka mamaye su(amma ban da kalmominsu), 'yan karnoni kadan sai su kuma suka fara mamaye wasu yankuna a duniya da suka hada da Amurka da Australiya da Afrika da kuma Indiya.

Da wannan ne kuma sabuwar daular Birtaniya ta samu kalmomi kamar su, 'hickory' da 'budgerigar' da 'zebra' da 'bungalow'.

Turawan na Birtaniya sun kuma yi huldar kasuwanci da kowa wanda kuma ta hakan ma suka rika daukar kalmomin wadanda suke cinikayya da su din, abin da muke kira aron kalma, duk da dai cewa Ingilishin ya rike kalmomin . Harshenmu na Ingilishi dai gidan kayan tarihi ne na mulkin mallaka.

Me ya hada duka wanna da rubutun kalmomi? Idan muka aro kalmomi, galibi suna fitowa ne daga tsarin rubutu na Latin, amma kuma furucinsu ya bambanta da yadda muke furta su a Ingilishi.

Harsuna da dama suna rike kalmomin da suka aro. Misali Turawan Norway sun mayar da kalmar 'chauffeur' zuwa 'sjafor, su kuma 'yan Finland suka mayar da 'strand' zuwa 'ranta'.

Maimakon irin wannan al'ada, mu a Ingilishi, muna amfani da kalmomin aron ne galibi kamar yadda muka karbo su, ba kunya ba tsaro, sai ma alfahari.

Amma dai a wasu kalmomin da muka aro, mun karbe su da yadda ake furta su, sai dai mun sauya yadda ake rubuta su:

Misali kalmar 'galosh' (daga Faransanci 'galoche') da 'strange' (daga Faransanci 'estrange').

Wasu kalmomin kuwa ba mu sauya yadda ake rubuta su ba, amma kuma mun sauya yadda ake furta su kamar kalmar 'ratio'( wadda asalinta a Latin kamar 'ra-tsee-o' ake kiranta) da 'sauna' (wadda Turawan Finland ke furta 'au' din kamae 'ow') da 'ski' (wadda Turawan Norway ke furta ta kamar 'she').

Ko kuma a wani lokacin mu bar yadda ake rubuta kalmar a asalin harshen da muka aro ta da kuma kusan yadda suke ambatonta, kamar kalmomin: 'corps' da 'ballet' da 'pizza' da 'tortilla'.

Ragon harshe:

Kari a kan hadama sai kuma lalaci a abubuwan da suka hadu suka sa harshen Ingilishi ya zama tarin tarkacen shirme, ko kuma kamar yadda masana harshe suke cewa, ''tsimin furuci'' (economy of effort).

A wannan fannin yadda ake fadin kalma yana iya sauyawa domin saukaka wa ko dai mai magana(ta hanyar ajiye wani sauti) ko kuma maisauraro(ta yadda sauti zai fito sosai).

Sakamakon tasirin Turawan Faransa da na kasashen Aktik(Actic ko Scandinavian) masu tsananin sanyi, mun yi watsi da wasu sautukan na wasu kalmomin kamar 'hopian' ta koma 'hope' haka kuma a kwana a tashi sautin 'e' da ke kalmae 'end' shi ma aka daina fito da shi.

A karnin baya bayan nan, mu kan bar rubutun kalma yadda yake duk da cewa mun guntile sautinta misali kamar sautin 'vittle' wanda har yanzu ake rubuta kalmar kamar a da 'victual'.

Haka mun saukaka yadda ake fadar hadakar wasu sautukan misali, 'kn' ya zama 'n' ( know) da 'wr' wanda ya zama 'r' (wrong).

Sannan kuma mun daina amfani da wasu sautukan gaba daya, amma ba mu daina rubuta su ba, kamar sautin 'kh' wanda muke rubutawa 'gh' yanzu mun mayar da shi sautin 'f' kamar yadda yake a kalmar 'laughter' (dariya).

Ko kuma misalin inda ma muka cire sautin gaba daya shi ne kamar a kalmar 'daughter' ('ya).

Wani lokacin kuma haka kawai sai sauti ya sauya ba tare da wani dalili ba.

Misali daga shekarun 1400 zuwa kusan shekara ta 1700, bisa wani dalili da har yanzu ba a sani ba, wasullanmu da ake ja, wajen fadarsu suka kwarare daga bakinmu kamar yadda kunfa take kwararewa daga kofin shayi, inda kafin wannan lokaci 'see' ake furta shi da 'eh', 'boot' ake fadinsa kamar 'boat' yayin da 'out ake fadinsa kamar 'oot'.

Duk da cewa sautin ya sauya amma rubutun ya cigaba da zama yadda yake.

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Zanen masu dab'i na kasar Holland da suka fara zuwa Ingila a karshen karni na 16

Harsuna da kunnuwa ba su kadai ba ne malalata. Sakatarori da masu buga rubuta ma za su iya kasancewa.

Idan ka kawo sakatarori daga Faransa ko masu buga rubutu daga Holland da Belgium, inda masu dab'i na farko na Birtaniya suka fito, za su bi yadda suka saba yi ne a kasashensu.

Sakatarori 'yan Faransa da tasirin harshen Latin ke tare da su, ba su ga dalilin da za mu rubuta 'cwen' ba alhalin abin da suka ji an fada ya kamata a rubuta shi kamar 'queen' ne.

Masu buga rubutu 'yan kasar Holland su kuma suna ganin akwai wani abu da ya bace a kalmar 'gost' saboda haka suka yi satar shigar da 'h' kalmar ta koma 'ghost'.

Sai kuma dagawa da ji-da-kai:

Wani abu kuma da ya yi tsayin-daka domin ganin rubutun harshen Ingilishi ya zama gagararre shi ne ji-da-kai ko dagawa.

Wannan ya fara ne a karni na 11, lokacin da Faransanci ya zama harshen manyan mutane masu matsayi, wadanda suka isa, kuma ya cika mana fannin girkinmu da na shari'a da kuma wakoki da kalmominsa.

Amma wannan dagawa ta bunkasa ne a zamanin farfadowar adabin Turai daga karni na 14 zuwa na 16, lokacin da masana suka bayar da fifiko wajen amfani da kalmomi na ainahi.

Daga nan ne suka rika aro kalmomi gaba daya, wanda shi ya sa za ka ga sunayen yawancin abubuwanmu da suka shafi kimiyya da fasaha sun fito ne daga harshen Latin da Girka(kuma yawancin masu suna Girkan sun shafi Latin kan yadda ake rubuta su).

To amma duk da haka a lokacin masanan sun ga cewa kalmomin da muke da su mu ma ya kamata a ce su nuna asalinsu su ma.

Ko kalmar 'peple' ta samo asali ne daga kalmar 'populus' ta Latin? Duk da haka suka ga ya kamata a ce ta samu kariya ta musamman domin ta nuna martabarta, a don haka suka kara mata 'o' suka mayar da ita 'people'.

Kalmar 'det' kuma ta ci bashin 'debitum' ne? To a sa mata 'b' domin ta fito fili sosai mu santa, shi ne ta zama 'debt'.

Kalmomi da yawa an kara musu harufa ne ta irin wannan hanya ta laifi('fau {l}t) na tuhuma (indi{c}table).

A wasu lokutan suna sauya yadda ake furta su domin ya zo daidai da yadda rubutunsu yake kamar kalmar 'fault'.

Kuma a wasu lokutan masu sauya rubutun ba suna kuskuren tarihin asalin kalma; misali yayinda 'isle' wadda a da aka san ta a matsayin 'ile' ta samo asali ne daga 'insula' shi ya sa aka sa mata 's', ita kuma kalmar 'island' ba haka take ba, domin ita ta fito ne daga tsohon Ingilishi inda aka san ta da 'iegland'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lokacin bunkasar adabi a Turai masu amfani da Ingilishi suka rika aro kalmomin Latin da na harshen Girka

Wani karin bangare na dagawa da ya kara sarkakiya a kasahen Yamma a 'yan daruruwan shekarun da suka wuce nan kusa shi ne; kishi ko alfahari da kasa.

A nan sai mu ce 'yan kalmomi na Turancin Amurka da ake gani masu saukin rubutu kamar 'color' a madadin 'colour' da 'center, a maimakon 'centre' galibi sun samu ne bisa burin masanin

adabin nan na Amurkan Noah Webster na samar da wani Turanci na daban da za a ce na Amurka ne.

A daya bangaren kuma ita ma kasar Canada ta zami ta yi amfani da kalmomi kamar yadda suke a Birtaniya domin ita ma ta yi alfahari da asalinta, wato kishiyar abin da Amurka ta yi.

To ya lamarin yake a yau kuma? To ai a yau kuma, ba ma son mu rubuta kalmomin Ingilishi kamar yadda muke furta su, idan ba haka ba me za ka ce da mutum da ya rubuta kalmomi kamar

haka, 'hed' da 'hart' da 'lafter' da 'dotter' da kuma 'det'? Jahili watakila ko? Za ka yi fushi saboda sun yi sauki ko? Eh! Haka lamarin yake muna jin dadin wahalar da muke jefa kanmu ciki.

Kuma muna barin abubuwan da ba su da muhimmanci su zama mizaninmu wajen cewa wannan shi ne wane wannan kuma karansa bai kai tsaiko ba, shi ba kowa ba ne.

Mun dauki abin da yake da muhimmanci mun mayar da shi wanda zai nuna mana wanene wane wanene kuma ba wane ba.

Hadama dai ita ta faro da wannan matsala ta harshenmu sai lalaci ya share mata wuri ta zauna dagawa kuma ta tabbatar da zamanta daram.

Tarihin harshen Ingilishi labari ne da ya kunshi abubuwa munanan dabi'u(vice) wanda wannan kalma ce da daman Faransawa suka kawo mana, duk da dai cewa ba za mu dora musu alhakin munanan dabi'un ba (vices) su kansu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How the English language became such a mess