Dalilin da ya sa zaki yake da zaki

Hakkin mallakar hoto Getty

Za ka dauka cewa 'ya'yan ita ce kamar Mangwaro da gwanda da sauransu suna da zaki ne saboda sukarin halitta da ke cikinsu.

To saurara Veronique Greenwood ta ce ka sake tunani domin abin ba haka yake ba.

Muna daukar sukari a matsayin kanwa uwar gamin duk wani zaki, saboda haka ne ma idan mun ji lemo ya yi mana cakwai a baki sai mu dauka saboda sukarin da yake da shi ne da

harshenmu ya dandana, haka kuma muke cewa a kan duk wani dan itace kama daga tumatur zuwa inibi da sauransu.

To sai dai Linda Bartoshuk ta Jami'ar Florida wadda masaniya ce a kan dandano, tare da abokan aikinta suna da wani bayani na daban a kan wannan fahimta ta tun tal-tale ko iyaye da kakanni.

Masanan a bincikensu sun gano cewa yawanci sinadaran da suke sa dan itace ya yi dandano mai zaki ba wai wadanda ake jin dandanon nasu ba ne, a maimakon haka wadanda ake jin kanshinsu ne.

Bartoshuk ta ce tun a shekarun 1970 aka taba tattauna wannan magana ta cewa ana ganin sinadaran da ake jin kanshinsu a jikin wani dan ita ce su ne kila suke sa shi zaki.

To amma tasirin kowa ne sinadari ba shi da yawa haka kuma shi kansa sinadarin ba shi da yawa a jikin dan itacen, to ta yaya za a ce kuma wannan sinadari shi ke sa hi zaki ba sukarin ba?

Bartoshuk ta ce, ''na san akwai wannan magana, to amma ban taba sanin an yi wani babban bincike a kai ba, kuma haka abin yake.''

Masaniyar ta ce, a 'yan shekarun da suka wuce, a lokacin da suke bincike tare da abokan aikinta a kokarin gano sinadaran da mutum ke ji idan yana shan tumatur daga nan ne ta gano wani abin mamaki.

Hakkin mallakar hoto

Ayarin masu binciken sun yi nazari a kan sinadaran nau'in tumatur daban daban har iri 152, suna daukar bayani kan yawan sidarai daban daban da suka danganci sukari(glucose, fructose, fruit acids) da kuma wasu daban har 28.

Haka kuma a cikin shekaru uku masu binciken suka hada wani ayarin masu dandana dandano domin tantance sama da 66 daga cikin sinadaran da aka ware inda za su sanya kowanne a

matakin da suke sonsa da zakinsa da tsaminsa da sauran bayanai da suka shafi dandanonsa.

Har yanzu Bartoshuk na tuna yadda a wani lokaci da take zaune a ofishinta da tarin wadannan bayanai ta ji yanayin bukatar gano sinadarain da ya fi sanyawa a ji dandanon zaki.

Tana tsammanin bincikenta ya gano sukari a mtsayin amsa, ko da ike dai ba shakka sukarin na daga cikin sinadaran da suke haddasa zakin to amma, ''sai da na kusan tuntsirewa a

kujerata, domin na ga wasu sinadarai bakwai da suke sa dandanon zakin sosai.'' In ji ta.

Bugu da kari wadannan sinadarai bakwai da alamu su ne suka sa wadannan masu dandana dandanon suka ce wani nau'in tumatir daga cikin wadanda suka tantance ya fi wasu wadanda suka fi shi sukari zaki nesa ba kusa ba.

Lokacin da masu tantancewar suka debo wadannan sinadarai daga tumaturin suka zuba su a ruwan sukari sai ruwan ya kara zaki.

Haka kuma Bartoshuk da abokan aikinta sun guidanar da irin wannan bincike da nau'in dan ita ce na inibi na Strawberry wanda suka gano ya fi na blueberry zaki duk kuwa da cewa shi na

biyun ya fi na farkon sidadarin sukari, amma na farkon ya fi shi wadannan sinadaran kamar na wancan tumatir din da ya fi zaki.

A gwajin da masanan suna yi, na zuba wadannan sinadarai na inibin na farko a cikin ruwan sukarai sai suka ji zakin ruwan har ya fi na ruwan farko da aka sa masa sinadaran cikin tumaturin.

Haka kuma da suka sanya wa ruwan suklarin sinadaran tumaturin da na inibin sai zakin ya linka biyu.

Hakkin mallakar hoto Getty

A ruwan sukarin ba kanshin 'ya'yan inibin na strawberry ba ne ko na tumaturin yake tashi, domin ba a ma sa su yadda za su yi yawan da za a ji kanshinsu ba.

Me yake faruwa a nan ?Har yanzu masu bincike na kokarin gano abin da ya sa kwakwalwa ta ke hade wannan bayani.

An san cewa bayanan da suke fitowa daga kwayoyin halittar da ke karbar dandano wadanda sinadaran nan( da suke sa a ji zaki amma ba na sukari ba) suka tsokano suna tattaruwa ne a

wuri daya da ke sarrafa bayanan dandano a kwakwalwa, maimakon su hadu da bayanan da suke fitowa daga hanci shi kansa. In ji Bartoshuk.

Mai binciken ta ce ko da ike dai ba fagenta ba ne wannan amma, tana ganin,a kwakwalwa idan kana da sinadaran da suke shafar kwayoyin halittar da dandano yake shafa, to kwakwalwa tana hade wadannan bayanai waje daya ne.

Kuma daga cikin wannan hadewar ne, na wasu sinadaran sai asamu karuwar wani dandano.

Yayin da su masu bincike ke ci gaba da kokarin gano wannan bakon abu, mu kam ba abin da za mu yi sai mafarkin abin da zai iya kasancewa.

Watakila a kai wani yanayi da za a rika hada ruwan lemo(juice) mai zaki ba tare da an sa sukari ba sai sinadaran wasu 'ya'yan ita ce.

Bartoshuk ma ita tana ganin yuwuwar ko za a iya kaiwa ga samar da wani dan itace mai zaki sosai idan binciken ya yi nisa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The real reason sweet tastes sweet