Ko kin cin abincin safe na kara kiba?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Nazari ne mai rauni, amma sai ka duba shaidun da aka gabatar. Za ka ga yadda lamarin ya kara daburcewa. In ji Claudia Hammond wadda ta bincika.

An saba gaya mana cewa abincin safe wani muhimmin bangare ne na abinci mai gina jiki, musamman idan kana gudun ka da ka yi kiba fiye da yadda kake bukata.

Wasu makarantun har abincin safen suke bayarwa domin tabbatar da ganin yara da dama ba su rasa wannan muhimmin kalaci a rana.

To amma fa ba kowa ne yake iya cin abinci da safe ba, domin a Turai da Amurka tsakanin kashi 10 cikin dari da kashi 30 cikin dari na jama'a ba sa bari.

Kuma binciken ya nuna yawanci 'yan mata masu shekaru goma sha ba lalle ba ne su ke yin kalaci, inda suke cewa ba su da lokaci ko ba sa jin yunwa ko kuma suna kan tsarin rage yawan cin abinci saboda rage kiba.

Barin cin abincin safe a kan dalilin rage kiba ko makamancin haka ya saba wa ka'idoji ko shawarwari da yawa.

Hakkin mallakar hoto PA

Matsalar ita ce barin kalaci yakan sa ka ji yunwa tsawon rana, inda za ka rika sayen 'yan kayan abinci na kwalan da makulashe wanda kuma zai kai ka ga tara maikon da kake gujewa har ka yi teba.

To amma nazariyya ce maras makama sosai, idan ba sheda ka samu ba ta sosai ka tabbatar cewa mutanen da ba sa cin abincin safe sun fi kowa yawancin maikon da ke sa kiba.

Abu ne mai wuyar gaske ba kamar yadda kake tsammani ba, a iya nazarin tasirin barin cin abincin safe a kan kara jiki.

Matsalar farko ita ce a kan wana ma'auni za ka zabi abincin na safe. Yawan abincin da ya kai nawa ne za a iya cewa ya kai kalaci?

Za ka rika cin abinci sau bakwai ne da safe a duk mako, kafin a sa ka cikin rukunin masu cin kalaci?

Kuma da karfe nawa za ka ci abinci kafin a ce ka ci abincin safe? Domin misali, ma'aikatar ayyukan gona ta Amurka ta gudanar da bincike a kan haka, inda a yawancin nazarin da aka yi aka ayyana abincin da ake ci kafin goma na safe a matsayin kalaci.

A bisa hakan duk wanda ya ci abinci da karfe 10:05 na safe ba a daukarsa ya ci abincin safe domin haka zai iya rikita sakamakon binciken.

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

Wani abin kuma shi ne abincin da ake ci a matsayin kalaci ya bambanta daga kasa zuwa kasa.

A yankin da ya fi sanyi a kasashen Turai (Scandinavia) abincinsu na safe zai iya kasancewa kifi banda, a Jamus kuwa zai iya zama nama mai yanka-yanka (cold meat), yayin da a Birtaniya kuwa abincin na kalaci zai iya kasancewa

nau'in hatsi ko alkama da aka sarrafa (kamar Corn Flakes).

Wannan ne ya sa nazarin tasirin cin kalaci zai yi wuya a duniya baki daya saboda amfanin abincin ya dogara ne da abin da kasa a abincin.

Amma idan muka takaita nazarin a kan yawan sinadarin maikon da mutum yake ci a abincin, akwai bincike da dama da aka yi a kan nauyin da hakan ke jawowa jikin mutum.

A nazarin tarin binciken da aka yi kafin 2004 an gano cewa a gaba daya wadanda ba sa cin abincin safe, ba sa cin wani karin sinadarin maiko na abinci a ranar wanda zai maye wanda ba su ci ba da safe.

Mutanen da suke cin kalaci sun fi samun abinci mai gina jiki amma hakan ba yana nufin sun fi samun wanda ya fi sinadarin maiko ba ne.

Nazarin da ya yi magana a kan kara nauyi ko jiki a kan wadanda ba sa cin abincin safen yana da 'yar sarkakiya.

A wasu bincike da aka gudanar guda hudu, an gano cewa yaran da ba sa cin abincin safe yawancinsu sun fi nauyi, amma kuma wani nazarin da aka yi guda uku sai aka ga ba bu wani bambanci.

Bambancin wadancan guda hudu na farko shi ne masu binciken sun yi kokarin kawar da wasu abubuwa uku wadanda za su iya shafar sakamakon.

Saboda haka ne shedar sakamakon ta fara karkata wurin dangantaka tsakanin barin cin abincin da kuma karin nauyin mutum.

Wani abu kuma da za a ce ya kara rikita lissafin shi ne wani nazari da aka yi a Amurka a 2011 wanda ya nuna wadansu bincike da aka gudanar biyar da suka gano alaka tsakanin barin cin abincin safen da kuma kara nauyi.

Uku daga cikinsu sun gano cewa rashin cin ba ya sa wani bambanci da daya kuma da ya ke nuna kishiyar hakan; cewa a cikin yara masu nauyi sosai, wadanda suke kalaci sun fi nauyi.

Haka kuma wani abuin da ya kara wata sarkakiyar a kan binciken shi ne kuma, wani nazarin da aka gudanar a kan sakamakon wasu binciken guda 19 da aka yi a yankunan Asiya da Pacific an gano alaka tsakanin karin nauyi da kin cin abincin safe.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kazalika wani nazarin bincike da aka yi a Turai an samu sakamako iri daya amma kuma wani nazari daya ya gano cewa alaka tsakanin kin yin kalaci da nauyin mutum na faruwa ne kawai a wurin maza.

To me zai kasance idan ka juya tambayar? Bincike guda bakwai sun gano cewa yaran da suka yi nauyi da yawa sun fi yuwuwar kaucewa kalaci.

To amma wannan ya kara nuna matsalar da ke tattare da wannan nazari; abu ne da ya ratsa ko ina ba sa fitar da wani tabbataccen dalili.

Ba za mu iya cewa ga abin da ya haifar da wannan ba, ko wannan ne ya jawo wannan ba kai tsaye ( kwai ne ya samar da kaza ko kaza ce ta samar da kwai); watakila wadannan yaran ba sa cin abincin safe ne saboda suna son

rage nauyi domin damun sun riga sun yi kiba shi ya sa suka rage cin abinci.

Wani zabin mafuta a nan kuma shi ne a yi nazarin mutane na tsawon lokaci, kuma bincike irin wannan da aka yi na farko an yi shi ne a 2003.

Masu binciken sun gano cewa yaran da ba sa cin abincin safe yawancinsu sun fi kiba.Amma da suka sake nazari a kan yaran bayan shekaru uku sai suka gano cewa yaran da suka fi nauyi daga cikin wadanda ba sa cin abincin

safen sun rage kiba a tsawon wannan lokacin.

A karshe dai mun kasance da yanayin da ke nuna cewa yawancin bincike, amma fa ba duka ba, sun nuna yaran da ba sa kalaci sun fi kasancewa masu kiba sosai.

Sai dai ba za mu iya tabbatarwa ko abincin da suke ci ko kuma kalacin da ba sa ci ba ne ke sa su kara kiba.

Idan rashin cin abincinsu ne yake taimakawa wajen sa su kara kiba, to ba a san dalili ba domin ba sa cin wani karin kayan maiko idan aka duba abincin da suke ci gaba daya.

Idan kuma ba maganar yawan maikon da suke ci ba ne, ko za a iya cewa lokacin cin abin nasu yana iya yin tasiri ke nan?

Ko abinci uku kanana sun fi biyu manya? 'Yan bincike da aka yi a wannan fanni kadan ne kuma a warwatse ko kuma samfur aka bi wajen yinsu, amma a kwai wanda aka yi a kan manya a 1992.

A gwajin an bai wa wasu mata masu teba tsarin cin abincin da za su rika bi kullum, inda kowacce za ta rika cin abincin da yake da yawan sinadarin maiko daya da sauran.

Rabinsu an tsara musu cin abinci sai uku a rana kamar yadda mutane suka saba, amma kuma abincin dan kadan ne, yayin da 'yan daya bangaren aka hana su cin abincin safe amma za su ci na rana kadan kuma su ci na dare mai yawa.

Sakamakon wannan bincike ya bayar da sha'awa da mamaki:

Wadanda aka hana su cin abin safe sun rage teba, idan aka sa su a rukunin wadanda suke yin kalacin.

Su kuma wadanda suke cin abincin safen sun fi zubar da teba idan da za su bar kalacin. A takaice dai abin da aka gano a wannan bincike shi ne sauyin yanayin cin abincinsu yana sa su rage teba.

To a nan watakila abin koyo a wannan bincike shi ne ka jarraba wani abu daban da yadda ka saba yi.

Hakkin mallakar hoto obesity

Masu nazari kan tunanin dan-adam a Jami'ar Hertfordshire a Birtaniya sun kirkiro tare da gudanar da tsari na rage teba a kan wannan hanyar da aka gwada.

Wannan dai wani lamari ne mai rikitarwa, wanda shi ya sa ma a wata makala da aka wallafa a kan sarkakiyar rage teba ta hada da maganar cewa kin cin abincin safe na taimaka wa wajen rage kiba da cewa abu ne da ba a tabbatar ba.

Amma idan ka zabi magana daya ko wani nazari guda daya ka dogara a kansa ko za ka iya samun mafita a duk ra'ayin da ka bi.

Saboda haka idan ana maganar rage teba ne ko jiki, ba a kawo maganar alkali( sai kawai yadda ta kaya).

To amma dai watakila akwai wani alfanun da ke tattare da yin kalacin.Domin wasu samfuran bincike da aka gudanar a yankunan karkara na Jamaica da Peru an ga cewa yaran da ake ba su kalaci a makaranta sun kara kokari.

Wannan ba yana nufin hakan abin yake a ko ina ba fa ke nan, domin su sukan iya kasancewa daman ba sa samun abinci mai gina jiki kafin wannan gwaji, a don haka kalaci zai iya yin tasiri a kansu maimakon yaran da suke samun abinci sosai.

To mu koma kuma kan ainahin tambayar da ta jawo wannan abu baki daya; za ka ci abincin safe idan kana son rage kiba ko kuma za ka daina kalacin ne?

Mutanen da suke karyawa da safe jikinsu ya fi samun sinadaran abinci masu gina jiki,amma kuma idan kana ra'ayin rage jiki ne kawai, to sai ka jira sai an sake wasu gwaje-gwajen da nazari abu ne dai da ya shafi zabin mutum.

Wasunmu dai ba ruwansu da maganar karya kumallo. Idan kana cikin wannan rukuni sai ka dora alhakin hakan a kan kwayar halittar aikin jikinka (chronotype); domin wani sabon bincike ya nuna mutanen da ba sa barci da wuri ba kasafai suka damu da cin abinci da safe ba.

Saboda haka in dai ba wani sabon nazari aka yi ba, wanda ya saba da wannan, to hanyar lafiya kawai, ka bi maganar cikinka ka da ka yi masa tawaye ko ka yi fada da shi!

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Does skipping breakfast make you put on weight?