Yadda rayuwa take idan ba ka iya jin kanshi ko wari

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

Idan ka daina iya sansana abu abin da ka rasa ya wuce jin kanshi da wari, in ji Emma Young. Mutanen da hancinsu ya daina jin kanshi ko wari suna jin cewa sun yi rashi mai yawa.

Mu mutane ba ma daukar kanmu cewa mun kai sauran dabbobi jin kanshi da wari. Amma duk da haka bincike ya nuna cewa wannan dama ta jin kanshi tana iya tasiri a kan tunani da dabi'ar mutum.

Mutanen da suka daina jin kanshi da wari sakamakon wani hadari ko rashin lafiya, suna bayyana irin babban rashin da suke ji ya same su wanda ke da tasirin da ba za su taba tsammani ko tunani ba.

Watakila ba ma daukar wannan dama da muke da ita ta tantance kanshi da wari da muhimmanci a kan sauran abubuwan da jikinmu ke yi har sai mun rasa wannan lafiya.

Hakkin mallakar hoto istock
Image caption Za mu iya jin dubun dabatar kanshi daban daban

Nick Johnson mai shekara 34 zai iya gane lokacin da ya rasa wannan fanni na lafiyarmu da ba kasafai muke sanin muhimmancinsa ba idan komai na tafiya daidai.

A ranar 9 ga watan Janairu na 2014 ne lokacin da yake wasan kwallon gora na kankara tare da wasu abokansa a filin kofar gidan mahaifansa da ke Collegeville a Pennsylvania ta Amurka, ya gamu da matsalar.

A lokacin wasan nasu ne ya fadi har kansa ya fashe a wuri uku ga jini yana fitowa daga kunnensa kuma ya suma.

Har lokacin da aka kai shi asibiti bai farfado ba sosai sai dai jifa-jifa. Ya ce, ''ban san abin da ke faru da ni ba.''

Bayan da ya warke an ba shi damar ya koma tuka mota bayan mako shida, kuma ya koma bakin aikinsa a matsayin babban jami'in talla na yanki na kamfanin barasa na Troegs .

Bayan wani dan lokaci sai suka zo wani taro na kamfanin a kan wata sabuwar barasa da kamfanin zai yi.

''Kowa yana dandana ta, yana cewa ko kaji kanshin abu kaza, ka ji kanshin wannan abin?''

''Amma ni ban ji komai ba, sai na dandana ta, akwai wadanda suke cewa sun ji kanshin kaza da kaza, ni kuma har yanzu ban ji ba. Daga nan ne na san cewa yanzu bana jin kanshi ko wari.''

Damuwar hadarin da yayi da kuma maganin da ake masa ne watakila suka sa bai san ya gamu da wannan matsala ba da wuri.

Ya ce, abin ya girgiza shi, amma da yake yanzu ya san da ita, ya rungumi kaddara, matsalar ta zama jiki a wurinsa.

Mutanen da suka daina jin kanshi da wari sukan yawaita kukan rashin jin dadin abinci da abin sha.

Za ka iya dandana abin da ke da zaki da mai gishiri da mai tsami da kuma daci da harshenka.

To amma wasu abubuwan kamar lemon girho da balangu ko gasasshen nama(barbecued steak) sanin dandanonsu ya dogara ne ga jin kanshi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Johnson ya yi mamakin ma yadda hatta kanshin jaririnsa ba ya ji

Johnson da sauran masu larura irin tasa bayan kanshi da warin abubuwa da ba sa ji akwai kuma wani da ba sa ji kuma samsam.

A lokacin da Johnson ya gamu da wannan hadari matarsa na dauke da cikin wata takwas na 'yarsu ta biyu.

A lokacin da suke cin abincin rana sai ya ce, ''Ba na jin warin kunzugun 'yata. Ba na jin kanshin 'yar tawa ma.

Ta tashi yau da karfe hudu na asuba yau. Ina rike da ita muna kwance a gado. Na san yadda kanshin dana yake lokacin yana jariri. Wani lokaci abin ba dadi amma dai yana da wannan warin ko kanshi. Amma a wannan ban taba ji ba.''

Yadda abin ke kasancewa:

Kididdigar yawan mutanen da ba sa jin kanshi da wari ta kama ne a kusan dan kashi kadan na manyan mutane cikin dari. Hakan na nufin miliyoyin mutane ne ke nan suke da matsalar. Wasu an haife su ba sa ji wasu kuma sun gamu da matsalar ne daga baya.

Matsanancin ciwon hanci shi ne daya daga cikin cutukan da ke jawo wannan matsala a tsakanin matasa.

Wata matsalar kuma tana faruwa ne saboda kwayoyin halittarmu da suke karbar sakon kanshi ko wari sun yo kasakasa ne a bakin kofofin hancinmu, wanda hakan ya sa su cikin hadarin gamuwa da illa daga guba ko kwayoyin cutuka da muke shaka.

A kan mutanen da suka tsufa amma ba wadanda suka girma ba yawanci wannan larura tana samunsu ne yawanci sakamakon kwayar cutar birus(virus) wadda ke haddasa mura, kuma hatta ita kanta murar ma za ta iya jawo musu matsalar.

Abin da ba a sani ba zuwa yanzu shi ne, me yake jawo wasu mutanen hakan wasu kuma hakan ba ta samunsu.

A lokacin da muka kai shekaru 70 zuwa 80 kadan daga cikinmu ne za mu tsira da lafiyar hancinmu ta jin kanshi da wari.

To amma ba dindindin abin yake ba domin kwayoyin halittar da ke wannan aiki suna mutuwa ne wasu kuma na fitowa.

Sai dai yayin da muke girma shekaru na kama mu haihuwar tasu sai ta rika jinkiri, sai kwayoyin halittar da ke karbar kanshi da warin su mika wa kwakwalwa ita kuma ta sanar da mutum sai su ragu.

Image caption Harshe zai iya gane dandanon barkono amma kana bukatar jin kanshi kafin ka tantance wani dandanon mai sarkakiya

A game da matsalar Johnson watakila raunin da ya ji a 'ya'yan halittun da ke masa aikin jin kanshi da warin ya yi tsanani ne.

Su wadannan jijiyoyi sun tashi ne daga hanci zuwa kwakwalwa. Saboda haka lokacin da ya yi hadarin ya kuma kansa a kankarar, watakila motsin da curin kwakwalwarsa ya yi, shi ya tsinke jijiyoyin ko kuma ya matse su a jikin kashin kokon kai, a dalilin hakan ba sa iya karbar sako daga hancinsa su mika zuwa kwakwalwar.

Yadda ake jin kanshi:

Johnson ya kurbi ruwan barasarsa ta Nugget Nectar, wadda ita ce ya fi so.

Daga nan ne kwayoyin sinadaran barasar za su tashi daga ruwan zuwa hancinsa a lokacin da ya kai kofin bakinsa, inda za su tafi har zuwa cikin saman hancinsa, wato bangaren da ya kware wajen aikin jin kanshi da wari.

Bayan ya kurbi ruwan kuma sai wadannan kwayoyin sinadari na barasar su sake tashi daga can cikin bakinsa zuwa wannan sashe na saman hancinsa, to daga nan ne mutum zai san yadda kanshi ko warin abu yake.

To daga nan ne kuma sai kwayoyin sinadaran su harke a cikin majinarsa da ke hanci. Wajibi ne wannan ya kasance kafin a ji kanshin abu.

Babu wanda zai iya kallon yanayin halittar kwayar wani sinadari ya ce ga yadda kanshinta zai iya kasancewa ko kuma ma za ta yi kanshi ko wari ko kuma ba za ta yi ba ma sam-sam.

Abin dai da muka sani shi ne kafin wani abu ya kasance da kanshi ko wari dole ne sai kwayoyin sinadaransa suna tashi kamar tururi yadda iska za ta dauke su a shake su, amma kuma dole ne fa sai sun narke a cikin majinar hanci ta yadda jijiyoyin kai sako daga hanci zuwa kwakwalwa za su san da su.

Fahimtar yadda aikin jin kanshin barasa ko jikin da ko jaririnka ko kuma rigar matarka ko mijinki ko abokin zama a wurin mutumin da yake da lafiya sosai abu ne kamar wanda ba a fayyace ba sosai, tamkar wani dabo ne.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Jijiyoyin da ke kai sakon kanshi ko wari na hancinka suna reto hakan ya sa suke cikin hadari idan wani abu ya taba su

Kafin Johnson ya gamu da hadarin nan, irin mutanen nan ne da hancinsu ke saurin jin kanshi ko wari komai kankantarsu. Ba kamar ni ba, nan da nan zai iya bambancewa tsakanin barasar da ya saba da ita da saura.

Amma dai duk da haka abin ya hada da sabo na yau da gobe. Bayan sarrafa sakon kanshin, sai jijiyoyi su aika da bayanin zuwa sassan kwakwalwa ciki har da yankunan da ke kula da harda(memory) da yanayin mutum(emotion) da kuma inda tunani ke ke samuwa.

Daga nan ne sai cikin gaggawa mu san kanshin kwayoyin sinadaran da muke shinshinawa ko wadanda muka sansano.

Kafin yanzu an yi kiyasin cewa dan-adam zai iya tantance watakila kanshi ko wari dubu goma ne kawai, amma yanzu an samu sauyi.

Kamar yadda Joel Mainland wanda ke bincike a kan wannan fanni a cibiyar binciken kanshi ko wari ta daya a duniya (Monell Chemical Senses Center) da ke Philadelphia ta Amurka ya yi bayani.

A wata makala da aka wallafa a mujallar kimiyya ta Science, an yi kiyasin mutum zai iya jin kanshi ko wari sama da miliyan dubu sau dubu.

Sai dai akwai wasu tambayoyi da aka yi dangane da wannan nazari da aka samu wannan kididdiga ko alkaluma kuma har yanzu ana muhawara a kan ainahin yawan, amma shi kuwa Mainland yana ganin mun takaita baiwarmu.

Saboda yanayin aikinsa Johnson (mutumin da muke maganarsa a baya wanda yayi hadari) ya halarci horo da dama kan hanyoyin inganta jin kanshi.

Sauranmu ba mu samu wannan damar ba, wa ya sani ko mu ma muna da wata baiwar da ba mu sani ba.

Ba shakka an san kare da baiwar gano kanshi ko warin mutum a nesa.A lokacin da Mainland yake karatunsa na digirin-digirgir, malaminsa ya neme shi da ya bincika ya ga ko mutum ma zai iya yin abin da kare yake yi idan aka ba shi horo. Sai ya gano lalle mutum ma zai iya kuwa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Karnuka suna da jijiyoyin jin kanshi fiye da mu,amma kamar yadda Mainland ya nuna shanu kuma sun fi karnuka yawan wadannan jijiyoyi(su suna da kusan 1,200 karnuka kuma 800), sai dai ba a san ko shanu sun fi karnuka jin kanshin ba.

Abin da ya sa mutane ba sa jin kanshi kamar karnuka shi ne, su mutane ba sa daukar lokaci mai yawa suna bin kanshi ko wari wanda hakan ya sa ba mu saba ba.

Wane bambanci za mu gani idan har muka kara zage damtse wajen kwarewa wajen sanin kanshi da warin abubuwa?

Dalili daya na amfanin karin kwarewa wajen sanin kanshi da wari, hakan zai taimaka mana wajen sanin karin wasu abubuwa game da mu'amullarmu da sauran mutane.

Wasu mutanen da aka haife su da matsalar rashin jin kanshi ko wari ba, za su sha wahala wajen gane yanayin halin da wasu mutanen ke ciki, in ji Mainland.

Duk da cewa wasu mutanen su kan dogara da yanayin fuskar mutum, su san halin da yake ciki, to amma akwai abokanan da idan suka ji wani warin na jikin abokinsu za su iya gane wani yanayin na mutum.

Hakan ma zai iya sa su yi watsi da yanayin fuskarsa da suka gani kamar na murmushi ko bata rai.

Mainland ya bayar da misali cewa, kamara tsakanin abokai ne, wani zai iya magana a kan wata daga cikinsu: ''Kai ba ta farin ciki samsam.'' Sai sauran duka su ce, ''Amma fuskarta ta nuna tana farin ciki.'' Sai wani kuma ya ce, '' Eh, haka ne a zahirin za ka ga kamar tana farin ciki amma a gaskiya ba ta farin ciki.''

Masu bincike sun kuma gano cewa wari ko kanshi zai iya sauya dabi'ar mutum. George Preti da abokan aikinsa a Monell, sun gano cewa dan warin hammatar namiji ba jirkita yawan kwayoyin halittar da ke sa mace al'ada ba ma zai iya sa ta ji dadi da kuma kwanciyar hankali.

Pam Dolton kuma ya gano cewa mutane za su iya gane warin jikin mutumin da ke cikin damuwa ba tare da sun sani ba.

Saboda haka za a iya barin mutanen da ba sa jin kanshi ko wari a baya a wurin sanin wasu abubuwa da suka shafi mu'amulla da mutane.

To ko za a iya yi wa masu wannan matsala wani magani? Akwai hanyoyin magani masu kyau sosai. Idan matsalar ta same su sakamakon tsananin cutar hanci za a iya yi musu magani wani lokaci cikin sauri kuma su dawo suna jin kanshi ko wari kamar da.

Amma mutane kamar John wadanda suka samu matsalar ta hadari, dan abin da za a iya yi musu kadan ne ko za a dace kadan ne.

Domin ya je har wannan babbar cibiya ta duniya ta Monell,don neman shawara, inda babbar shawara da suka ba shi ita ce, ya rika shinshina wasu abubuwa sosai a wasu lokuta kullum domin akwai shedar cewa hakan zai iya farfado masa da jijiyoyin ya dawo yana jin kanshin.

Za a iya samun wani sauyi a nan gaba domin akwai rukunin masana a wanna cibiya ta Monell da suke gwaji a kan kwayoyin halitta na hanci a yanzu.

Suna gudanar da bincike ne kan hanyar da za ta fi dacewa da za su juya kananan kwayoyin halitta (stem cells) zuwa kwayoyin halitta masu aikawa da sako.

Fatansu shi ne za su yi amfani da wannan hanya su sabunta jijiyoyi ko halittun da ke aikin sarrafa kanshi a hancin mutum da kwakwalwarsa, ga mutanen da suka rasa nasu ta hanyar hadari ko kuma ma nasu suna da matsala tun lokacin haihuwa.

Masanan na fatan jarraba wanna hanya a jikin dabbobi a watan Satumba na wannan shekara ta 2015.

Kuma idan gwajin ya yi daidai nan da shekara biyar ko goma a yi a jikin mutane.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Johnson ya gano cewa matsalar ta sa ba ya iya sanin dandanon barasa

A yanzu dai akwai alamun kyakkyawan fata a wurin Johnson, domin wasu abubuwan masu kanshi sosai yana dan jin dan alamun kanshinsu.

Ko da ike yana ji ne kamar kanshin konannen mai ya ce.Amma kuma a 'yan watannin baya abin ya kai yana dan jin dan kanshi mai dadi.

Wannan na nuna alama cewa jikin nasa yana wani dan gyara a ciki. Tuni dai Johnson ya yi imanin cewa zai dawo ya ci gaba da rayuwarsa kamar da kafin ya ji wannan rauni.

Inda tuni ya koma wasansa na kwallon gora a kankara ( ko da ike yana murmushi, ya ce, yanzu ya sayi hular kwano wadda ta fi kowacce tsada yana amfani da ita).

Sanin irin hadarin da ya tsallake, wanda da yanzu sai dai ace ya mutu tuni, amma kuma yau ga shi a raye, ya ce, ''na gode da hakan, idan ma abin ya tsaya cewa na rasa jin kanshin ke nan har iya rayuwata to na karbi kaddarar hakan.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi to latsa nan How it feels to live with no sense of smell