Fasahar mayar da hoto kamar mai rai

Hakkin mallakar hoto Weiyao Lin

Wata fasaha ta bullo kan yadda za ka iya sauya fuskar mutum a hoto idan yana dariya ne ya turbune fuska ko kuma idan yana murmushi ne fuskar ta koma a turbune. David Robson ya duba wannan sabuwar fasaha.

Ta ya za ka sauya yanayin fuskar hoton mutum da aka dauka tun shekaru kusan dari da suka wuce?

Fasaha a yau ta kai yadda za a dauko hoton da aka dauka shekaru aru aru baya a karkade shi a sauya yanayin fuskar mutumin, idan a lokacin ya bata rai ne ya zama mai fara'a, idan kuma yana fara'ar ne a mayar da shi ya bata rai.

Da wannan fasaha tamkar za a dawo da motsin fuskar, sannan a bi duk wani kwarmi ko tsoka a malkwada ta yadda ake so ta yadda za ta zo daidai da yadda ake son hoton ya kasance.

Haka kuma masana na ganin da wannan fasaha za a iya inganta ko sauya duk wata soga ta hoto kama daga hoton sinima da hoton da ka dauki kanka da waya fuskarka a yakune.

Weiyao Lin da abokan aikinsa a Jami'ar Shanghai Jiao Tong da ke China wannan aiki, burinsu shi ne su bullo da fasahar da za a iya samar da yanayin fuskar mutum na dariya ko murmushi ko bacin rai da sauransu, yadda ake bukata sannan a dora ta a wani hoton.

Hakkin mallakar hoto PA

Ga mai karatu watakila ya ga wannan ai ba wani abu ba ne, amma a lokacin da ka duba ka ga dan murmushin da mutum zai yi fatarsa sai ta mike ko ta ja a kusan dukkanin fuskar.

Bisa la'akari da bambance bambancen da ke siffar fuskar mutane, sarrafa fatar fuska ta zama yadda ake bukata ba tare da wani sashe ya tabune ba jan aiki ne.

Ire iren wannan yunkuri da aka yi a baya yakan kare ne da samar da hoton fuskar da ke da jone-jone kamar ta wani dodo.

A wannan fasaha ta Lin, an ajiye hotuna biyu ne, daya wanda ake son a sauya daya kuma wanda ake son daukar fasalinsa.

Daga nan sai aka auna 'yan kananan bambance-bambancen da ke fatar fuskar, sannan aka kwatanta girman abubuwan da ke fuskar(ido da hanci da lebe da sauransu).

Daga nan ne kuma sai a kwatanta yadda fatar fuskar za ta motsa ta yadda za ta bayar da yanayin da ake bukata, daga nan kuma sai ka dora wannan lissafi a kan duk fuskar da kake bukata.

A kwanan nan mun bukaci Li da abokan bincikensa su jarraba wannan fasaha a kan hotunan wasu fitattun mutane na da. Sakamakon da aka samu ya dan firgita mu.

Hakkin mallakar hoto fatcatart

Mun sauya yanayin fuskar hoton nan na Mona Lisa kamar yadda kuma Lin din ya dauki fuskar mawakiyar nan Miley Cyrus da ta yi gatsine ya dorawa Sarauniya Victoria.

Haka kuma Lin yana fatan za a yi amfani da wannan fasaha ta yadda jaruman fim za su iya sa abubuwa a fim su yi motsi kamar suna da rai kamar a finafinai irin su Frozen, wanda hakan zai kasance ba tare da amfani da fasahar da ake yi da ita ba a yanzu mai wahala

Lin ya ce, ''wannan ba masu shirya fin kadai za su amfana ba, hatta miliyoyin mutane ma za su iya yin bidiyonsu na wata siga da suke bukata ssu sa shi a intanet.''

Sannan da wannan fasaha za a iya yin tarho na bidiyo, wato za a iya sarrafa hoton fuskarka daya ya rika motsi kamar yadda na bidiyo yake yi, kamar yadda idan kana waya kake dariya da motsi da fuskarka nan da can yadda za ta nuna yanayin da ka ke son wanda kuke wayar ya gani, wato maimakon ka yi ta hoton bidiyon kamar yadda yanzu kake yi idan kana waya da wani ta bidiyo( hakan zai sa ba sai kayi ta bata kudin wayarka na intanet ba).

Ya iya kasancewa ka dauki hoton kanka da waya a wani wuri mai kyau amma kuma fuskarka sai ta kasance kamar ta wani dolo, to a nan kana iya amfani da wannan fasaha ka sauya fuskarka ta zama kana murmushi ko dariya, daga nan sai ka tura hotonka duk inda kake so a gani.

Sai dai ba mu da tabbacin ko Sarauniya Victoria wadda a ko da yaushe za ka ga ba ta dariya ko murmushi a hotonta za ta yarda cewa wannan wani cigaba ne.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How to make Mona Lisa gurn and Queen Victoria twerk