Sau nawa ya kamata ka ga likitan hakori?

Hakkin mallakar hoto PA

Shin ko zuwa ganin likitan hakori duk wata shida wajibi ne? Claudia Hammond ta bincika

Da yawa mun dauka cewa lalle ne mu ziyarci likitan hakori kowane wata shida- ko da kuwa ba ma yin hakan.

Maganar wannan ziyara zuwa wajen likitan hakorin a duk wata shida a shekara har yanzu ita kanta magana ce da ake muhawara a kanta.

Hasali ma dai ba a san inda wannan magana ta samo asali ba, yayin da wasu ke ganin ta faro ne tun karni na 18, tun kafin a yi gwaje-gwajen da za su tabbatar da amfaninta.

Ba shakka mutanen da suke da matsalar hakori, suna bukatar ziyarar likita a kai a kai.To amma ya maganar sauran mutane?

Hakori na dindindin galibi ya fi fuskantar hadarin rubewa bayan ya gama fitowa, saboda haka da zarar hakorin yaro na dindindin ya fara fitowa yana bukatar a rika kai shi yana ganin likita yadda ya kamata.

Su kuwa matasa 'yan shekara goma sha hakoransu ba kasafai suke fuskantar hadarin wata matsala ba, har sai ka kai shekara 20, lokacin da hakorin girma ya fara fito maka. Saboda haka hadarin matsalar hakori abu ne da ya dogara da shekarun mutum.

A shekara ta 2000 kashi uku bisa hudu na likitocin hakori da aka tattauna da su a New York, sun bayar da shawarar mutane su rika ziyarar likita duk wata shida a shekara, duk da rashin wata sheda da ke nuna bambancin amfanin ziyarar tsakanin masu hadarin gamuwa da cutar rubewar hakorin ko kuma ta dadashi.

Har a yau dinnan, kungiyoyi da hukumomi da dama na ba da shawarar ganin likitan hakorin a duka wata shida a shekara.

To amma tsawon shekara da shekaru wasu na ganin zaben wata shida na ganin likitan a matsayin lokacin da ya fi dacewa abu ne kawai da bai zama dole ba.

Tun a shekara ta 1977 Farfesa Aubrey Sheiham na fannin kula da lafiyar hakori a Jami'ar Landan (university College London) ya wallafa wata kasida a mujallar harkokin lafiya, The Lancet, inda yake nuna takaicinsa na rashin wata tartibiyar sheda ta tabbatar da dalilin ganin likitan hakorin duk wata shida. Kuma kusan shekara 40 har yanzu yana jaddada wannan matsayi nasa.

Hakkin mallakar hoto z

A shekara ta 2003 an gudanar da bincike kan nazarce-nazarcen da aka yi a kan batun, inda aka samu sakamako iri daban-daban masu karo da juna.

Wasu binciken sun gano cewa babu bambanci tsakanin wadanda suke ziyartar likita a kai a kai da wadanda ba sa ziyara yadda ya kamata a kan cutar rubewar hakori da cuko ko kuma fitar hakorin.

A wadansu binciken kuma an samu dan bambanci wajen cike hakorin tsakanin wadanda suke zuwa wajen likita sosai da wadanda ba sa zuwa.

A bangaren dadashi kuwa yawancin binciken ba su samu wani bambanci tsakanin masu zuwa wurin likitan sosai ba da wadanda ba sa zuwa sosai a cutukan da ke shafar hakori na dindindin, kamar zubar jini.

Wani bincike ya nuna cewa ganin likita fiye da sau daya a shekara ba ya nuna wani bambanci a kan girman kurji ko cutar daji a farkonta.

Wani binciken kuma ya nuna idan mutum ya tsaya har sai bayan shekara yake ganin likitan, kurjin ya kan kasance ya girma a lokacin da aka gano shi.

A shekarar 2014 ma kungiyar taimako kan harkokin lafiya ta duniya ta Cochrane Collaboration, ta sake nazarin wannan bincike daban-daban inda ta sha mamaki kan abin da ta gano.

A sakamakon ta gano cewa yawan bincike da irin nazarin da aka yi ba su cancanci suka da amincewa da maganar ka'idar ziyarar likitan hakorin a duk wata shida ba.

Kungiyar ta gano cikakken bincike daya ne kawai inda ake shawartar mai larurar hakori ya rika ziyartar likita ko dai sau daya a shekara ko kuma duk bayan shekara biyu.

Kuma sun gano cewa wadanda suke zuwa duk shekara sun fi samun lafiya,amma kuma mai yuwuwa ne likitocin sun san wadanda suke zuwa duk shekara da masu zuwa a shekara biyun, wanda hakan zai iya kawo bambanci a maganin da suke yi musu ya kuma sa a samu san rai a sakamakon.

Akwai abin da ya kamata mu yi la'akari da shi a nan. Ko da wani nazari ya nuna misali yaran da suke ziyartar likita a kai a kai hakoronsa na da dan cuko fiye da wadanda ba sa zuwa, watakila akwai wasu abubuwan da suka sa hakan.

Abubuwan za su iya kasancewa su ne, wadannan yaran suna da wata dama da wadancan ba su da ita.

Za su iya kasancewa 'ya'yan masu hali ne fiye da wadancan, ko suna cin abinci mai kyau da kuma samun kayan kula da hakora mafiya inganci.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Akwai kuma wani dalilin na ziyarar likitan hakori. Ko da likitan bai gano wata matsala ba, mai yuwuwa ya jaddada maka muhimmancin ci gaba da kula da hakoranka da goge su sosai, ko da ike ita ma wannan magana babu wata tsayayyar sheda ko dalili kan hanyar da ta fi dacewa a yi hakan.

To sau nawa ya kamata ka rika ziyarar likitan hakorin ke nan?

Kungiya kamar Nice, wadda ke bayar da shawara a kan harkokin kula da lafiya a Biritaniya da Wales, ta ce wannan abu ne da ya dogara ga mutum kawai.

Hukumomin kungiyar sun ce, yara za su iya zuwa akalla sau daya a shekara saboda hakoransu na iya saurin rubewa.

Su kuwa manya sukan iya zuwa sau daya a shekara biyu amma ga wadanda ba su da wata larura ta hakori.

Sun ma ce ga mutumin da yake kula da hakoransa da dadashi sosai zai iya wuce shekara biyu bai gana da likita ba.

Haka a can Finland ma, wasu kwararru sun bayar da irin wannan shawara a 2001, inda suka ce matasa 'yan shekara 18 zuwa sama wadanda ba sa fuskantar wata matsala ta cutar hakori ko dadashi za su iya ziyarar likitan a duk bayan shekara daya da rabi ko shekara biyu.

To a kan wadannan maganganu na masana ina muka dosa ke nan game da lokacin da ya dace mu ziyarci likitanmu na hakori, idan muka ga sanarwar tunatarwar lokacin zuwanmu wurin likitan?

Yanzu ke nan za mu fake da wani dalili na rage zuwa ganin likitan idan har muna zuwa ke nan.

Idan ma kuma ba ka da wata matsala za ka iya saurarawa har bayan watanni shida kafin ka yi tattaki ka je ka wage bakinka a dudduba.

Amma dai komai ya rage ga yadda kai da likitanka na hakori kuka duba yanayin lafiyar bakin naka, kafin tsayar da wa'adin da ya kamata ka rika kai ziyarar.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How often do you need to see a dentist?