Wace hanya ce ta fi maganin shakuwa?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kama daga matse hanci da sauran wasu dabaru na al'ada mutane kan yi kokarin raba kansu da shakuwa idan ta same su.

Kai me kake yi idan ta same ka kuma me ya sa kake yin hakan? Claudia Hammond ta yi nata binciken.

Da zarar shakuwa ta kama ka sai ka ga kowa na bayar da shawarar yadda za ka rabu da ita, walau matse hancinka ne ko kuma ba ka tsoro ne.

Ganin yadda ake da hanyoyi da dama da za a zaba na maganin shakuwar, maganar ita ce, wacce ce kimiyya ta yarda da ita?

Da zarar ka yi shakuwa sai tantanin bakin huhunka ya tsuke, wanda hakan yake sa iska ta shiga huhun da sauri.

Wannan sai ya sa jijiyoyin da kake amfani da su wajen magana su rufe da sauri sai ka ji dan karan nan 'hik' (hic).

A kwai larurori fiye da 100 da ke haddasa shakuwa amma yawanci ba masu cutarwa ba ne.

A wani lokacin ma wani magani ne da mutum yake amfani da shi yake jawo masa shakuwar.

Amma kuma a yawancin lokaci ba daya daga cikin wadannan da ke jawo ta.

Dariya da shan barasa da yawa da cin abinci hannu-baka-hannu-kwarya(sauri da sauri) ko shanye wani abu da sauri, duk wadannan ka iya jawo shakuwa.

Sannan kuma za ta iya tasar wa mutum haka kawai ba wani dalili na bayyane.

A kan wasu mutanen ta kan iya yin tsanani. Mutumin da ya yi fama da shakuwa fiye da kowa kamar yadda aka sani a tarihi, shi ne wani dan Amurka Charles Osborne.

Mutumin ya yi fama da shakuwa ne tun daga 1922, kuma an ce kamar yadda aka ruwaito a labarin, yana kokarin auna nauyin alade ne a lokacin.

Tun daga wannan lokaci bai daina shakuwa ba sai a watan Fabrairu na 1990, wato shekaru 68 cif-cif.

Duk da cewa akwai hanyoyi masu sauki na maganin shakuwa, amma ra'ayi ya bambanta kan wadda ta fi dacewa.

Yawancin hanyoyi na al'ada da ake amfani da su a gida sun dogara ne a kan abubuwa biyu.

Na farko hanyoyi ne da suke kara yawan iska mai dumi wadda mutum ke fitarwa waje ta numfashinsa (carbon dioxide) a cikin jininsa, domin hana kofar nan da ake samu a tantanin huhunsa wadda iska ke shiga ta haifar da shakuwar.

Wadannan hanyoyin sun kunshi dakatar da numfashinka ko kuma mutum ya yi numfashi a cikin wata jakar takarda.

Wani lokaci wadannan dabaru sukan yi aiki (dakatar shakuwar) amma masu bincike ba su da tabbacin dalilin haka.

Wasu na ganin wata dabara ce ta dauke hankalin jiki, ta yadda zai mayar da hankali kan samar da iskar mai dumi (CO2).

Wasu kuma na ganin karancin wannan iska mai dumi ne yake sa shakuwa saboda haka kari ko yawanta zai yi maganin shakuwar.

Wata hanyar kuma ta magance shakuwa ita ce, ta yin wani abu da zai zaburar da jijiyar da ta tashi daga kwakwalwa zuwa ciki, wadda ke tsara aikin numfashi da hadiya.

Ta wannan hanya za a yi wani abu ne da zai karkato da hankalin wannan jijiya ne ta aika da sako kwakwalwa da sauri cewa kwakwalwar ta hanzarta yin wani abu kan wannan sabon abu da ke faruwa (shakuwa).

A nan ne maganar kwankwadar ruwa da shan lemon tsami ko kuma tauna kankara ta zo.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Haka kuma jan tsinin harshenka ko sanya yatsunka a kunnenka ko danna kwayar idonka a hankali duka za su iya zaburar da wannan jijiya.

Duka wadannan abubuwa ne da za ka dauka a matsayin masu dauke hankalin jikinka daga wannan shakuwa da yake yi, wanda hakan daidai ne da dabarar tsorata mutum da wani abu lokacin da yake shakuwar.

Akwai kuma wata hanyar ta daban, wadda ba lalle ka so ka gwada ta ba a gida.

Francis Fesmire na kwalejin koyon aikin likita ta Jami'ar Tennessee, a Amurka, shi ne ya kawo dabarar a wata kasida da aka wallafa a 1988 (mai suna "Termination of intractable hiccups with digital rectal massage" da Ingilishi).

Wannan dabara ta samu ne, lokacin da wani mutum ya je sashen bayar da kulawar gaggawa na marassa lafiya, yana kukan cewa a kwanaki biyun da suka gabata yana shakuwa a duk dakika biyu.

Bayan da aka jarraba duk wasu dabaru da hanyoyi na dakatar da shakuwar wadanda aka saba yi, abu ya gagara, sai likitan ya tuna wata dabara da aka wallafa a wata kasida a shekarar da ta gabata.

Wannan dabara kuwa kan wata tsohuwa ce mai shekara 71 wadda likita ya rage saurin bugun zuciyarta wanda ke yi da sauri-sauri, ta hanyar cusa mata dan yatsa a takashinta.

Likitan ya jarraba wannan dabarar a kan mutumin da ke da wannan larura ta shakuwa kuma ta yi aiki.

Lokacin da ya samu kyautar yabo kan wannan dabara, Fesmire ya ce, tun daga wannan lokaci ya kuma gano cewa, inzali ( zuwan maniyyi ta hanyar sha'awa), ka iya yin tasiri iri daya da tura dan-yatsan, kuma ma marassa lafiya za su fi jin dadin inzalin.

Dukkanin wadannan dabaru biyu dai za su zaburar da jijiyar tsakanin kwakwalwa da ciki ne, wadda ke tsara aikin hadiya da numfashi ta yadda kamar yadda muka bayyana a baya, kwatsam za ta aika wa kwakwalwa sako cewa ta bar wannan aiki na shakuwa ga wani aiki na daban ya taso.

Gaskiya ne yawancin dabarun da mutane ke amfani da su na maganin shakuwar ba su da wata sheda ta gwaji.

Amma duk da haka, suna maganinta kuma ana ganin dukkansu ba su da wata illa.

Haka kuma dukkaninsu ba wadda za a tabbatar da ingancinta da cewa hanya ce ta magani dari bisa dari, wanda hakan ke nufin watakila akwai ma wasu tarin hanyoyin da ba a gano ba, amma dai duk da haka, ba za a kira su almara ba.

Idan shakuwa ta same ka, nan gaba, ka iya jarraba kowacce daga cikin dabarun.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Which hiccup remedies really work?