Gaskiya ne jikakken gashi na sa mura?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Masana kimiyya sun yi gwaje-gwaje da dama na tabbatar da gaskiya ko akasin wannan magana. Claudia Hammond ta bincika mana.

''Mura za ta hallaka ki'', wannan shi ne gargadin da kakata take yi min kullum, idan ta ga zan fita daga gida da kaina a jike a lokacin huturu.

A tsawon shekaru da dama a sassa daban-daban na duniya ana cewa mura za ta kama ka, idan ka shiga cikin sanyi musamman ma idan a jike kake.

To amma kamar yadda ka sani duk wani likita idan zai yi maka bayani a kan mura zai ce maka, wata kwayar cuta ce ta bairus (virus) take haddasa ta.

To hakan kenan na nufin ka da na damu da gargadin da kakata take yi min idan a ce, bayan na wanke kaina (gashi) yanzu-yanzu sai wata bukata ta taso min wadda za ta sa lalle sai na fita daga gida?

Tun da a Biritaniya nake da zama zan fara duba wannan lamari ne ta fannin yanayi. A tarin binciken da aka gudanar a Jamus da Ajentina an gano cewa yawancin mutane na kamuwa da mura ne a lokacin huturu, yayin da kuma a kasashe masu dimi (ko marassa sanyi sosai), kamar Gambiya da Guinea da Malaysia mutane sun fi kamuwa da mura a lokacin damuna.

Saboda haka daga wannan binciken za mu iya cewa sanyi ko ruwa (damina) suna sa mura, amma dai akwai wani bayanin bayan wannan.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Za mu ga cewa idan ana tsananin sanyi ko ruwa, mun fi kasancewa a daki kuma kusa da wasu mutanen tare da kwayoyin cutarsa.

To shin me yake faruwa idan muka kamu da sanyi ko muka jike? Wasu masana kimiyya sun shirya wasu gwaje-gwaje a dakin bincike, inda suka sa wasu mutane cikin daki mai sanyi kuma suka sakar musu kwayoyin cutar bairus mai sa mura.

Sai dai wadannan bincike da aka yi ba su tabbatar da ainahin gaskiyar lamarin ba, domin wasu masu binciken sun fahimci cewa mutanen da aka sa su a daki mai tsananin sanyi sun fi fuskantar hadarin kamuwa mura, yayin da wasu masu binciken kuma suka ga sabanin haka.

Sai dai kuma wani gwajin da aka yi na daban ya nuna cewa, da alamun gaskiya a maganar( jikakken gashi na jawo mura).

Darektan cibiyar yaki da mura da ke Cardiff a Biritaniya, Ron Eccles, yana son ya san ko kamuwa da sanyi da kuma jikewa na jawo kwayar cutar Bairus din wadda ita kuma ke sa mutum ya yi ta atishawa da yoyon hanci.

A binciken nasa, Eccles, ya sa mutane a wani dakin bincike mai sanyin gaske, sai kuma ya fitar da su, suka ci gaba da mu'amullarsu da mutane ciki har da wadanda suke da kwayar bairus din ta mura a hancinsu da makogwaro amma kuma ba su kamu ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba.

Rabin mutanen da Eccles ke gudanar da binciken da su, sun zauna ne a dakin da kafafuwansu a cikin ruwan sanyi har tsawon minti 20.

Sauran rabin kuwa sun kasance ne da safa da takalmansu a kafa amma kuma kafar a cikin bokitin da ba komai su ma har tsawon minti 20.

A cikin kwanakin farko babu wani bambanci na alamun kamuwa da sanyi da aka samu tsakanin bangarorin biyu.

Amma bayan kwana hudu zuwa biyar, kusan rabin mutanen da suka sanya kafarsu a cikin bokiti mai ruwan sanyin suka ce sun kamu da mura.

To amma fa kafin a yarda da wannan, ko a kafa hujja da shi dole ne a gano yadda ko abin da ke sa kafa mai sanyi ko gashin kan da ya jike zai iya sa maka mura.

A wani nazari an gano cewa idan jikinka ya yi sanyi sosai, sai jijiyoyin jini da ke hancinka da makogwaro su tsuke.

Wadannan jijiyoyin jini su ne kuma suke kai kwayoyin garkuwar jikinka da ke yaki da kwayoyin cuta, saboda haka idan aka samu karancin kwayoyin garkuwar jikin a hanci da makogwaro sai garkuwarka ta kwayar cutar da ke sa mura ta ragu na dan wani lokaci.

Idan gashinka(ki) ya bushe ko ka (kika) shiga daki jikinka(ki) ya sake yin dumi, sai jijiyoyin jinin hanci da makogwaron naka su bude, sai a samu karin kwayoyin garkuwar jiki da ke yaki da kwayoyin cuta a wuraren biyu.

To sai dai watakila kafin sannan kwayoyin cutar da ke haddasa murar sun hayayyafa har sun fara nuna alamun kamuwarka da mura.

Ko da yake mun yi maganar kamuwa da tsananin sanyi, to amma wannan kamuwa da sanyi ba shi ne ke sa mana mura ba, amma watakila shi ke tayar da kwayoyin cutar da daman tuni suke kwance a makogwaron.

Amma dai a sani cewa wannan magana ce da har yanzu take tattare da takaddama.

Kuma binciken Eccles ya nuna cewa mutanen da suka shiga sanyi sosai sun ga alamun mura ne kawai.

Wato babu wani gwaji na kimiyya da aka yi domin tabbatar da cewa lalle sun kamu da kwayar cutar bairus din da ke sa mura.

Wani bayani na karshe kuma shi ne, na wata almara da ta shafi lafiya a kasar Nowe (norway), wadda ke cewa mata sun fi gamuwa da matsalar zafin mafitsara da yawan jin fitsarin.

A dangane da wannan wasu masu binciken sun gano cewa sanyaya kafar mutane na sa wadansu mata su gamu da wannan larura ta fitsari, abin da ke nuna alamu cewa irin abin da ke faruwa a hanci da makogwaron mutumin da ya shiga tsananin sanyi (kafarsa), shi ne kila ke faruwa a mafitsarar matan su ma.

A don haka da alamun gaskiya a maganar kakata da ke ba ni shawara ka da in fita daga gida da jikakken gashi.

Ko da yake dai gashin ba zai sa min mura ba, kamar yadda ita take cewa, amma dai zai iya jawo ta.

Amma dai a yanzu ina ganin zan tabbatar da a ko da yaushe na busar da gashina da kyau kafin na fita daga gida, har zuwa lokacin da za a gudanar da karin bincike kan wannan lamari.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Will wet hair give you a cold?