Ko mata sun fi maza yawan magana?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Idan fage ne na hira ko tattaunawa ko kuma musayar ra'ayi, ko za a iya cewa mata sun fi maza karadi? Claudia Hammond ta duba maganar.

Mata suna furta akalla kalmomi 20,000 a rana sabanin takwarorinsu maza da ke ambata kalmomi 7,000 kacal.

Wannan shi ne abin da wasu fitattun littattafan kimiyya suke bayyanawa a kiyasinsu.

Wannan magana ce da ake dangantawa da yawancin kwararrun masana wadda ake amfani da ita sau da dama, wadda kuma da alamu take bayyana halin mata na kwashe rana suna gulma da gada, yayin da takwarorinsu maza ke tafiyar da harkokinsu a yawancin lokaci salin-alin, ba tare da wani karadi ba. To amma shin hakan gaskiya ne?

Za a iya auna yawan magana ta hanyoyi daban-daban. Za ka iya kai mutane dakin gwaji na kimiyya ka sa su tattauna akan wani lamari, kai kuma ka nadi maganganun nasu.

Ko kuma za ka iya sa su rika nadar maganganunsu a gida.

Za ka iya kirga yawan kalmomin da kowane mutum ya furta da lokacin da kowa ya dauka yana magana da yawan karba-karbar da kowa ya yi ko kuma yawan kalmomin da kowa ya yi a zagaye daya.

Da aka hada sakamakon wasu dalibai yara 73, masu bincike a Amurka sun gano cewa mata sun fi maza furta kalmomi, amma da bambanci dan kadan.

Kuma shi kansa wannan dan bambancin an same shi ne a lokacin da suke magana da iyayensu, saboda babu shi idan suna tattaunawa da abokansu.

Wani abu kuma shi ne, an fi samun wannan bambanci idan sun kai shekara biyu da rabi.

Wanda hakan ke nufin watakila abin na nuna yadda maza da mata suke da bambanci wajen saurin koyon magana.

To idan babu wani bambanci mai yawa tsakanin yara, yaya lamarin yake a wurin manya?

A lokacin da masanin tunanin dan-adam, Campbell Leaper daga Jami'ar California ta Santa Cruz, wanda ya gano dan bambancin da ke tsakanin mata da mazan ya gudanar da irin wannan bincike a tsakanin manya sai kuma maza suka wuce mata a yawan maganar. A nan ma kuma bambancin kadan ne.

Wani abin mamaki kuma shi ne, gwajin da aka yi tsakanin maza da matan a dakin bincike inda ake ba su damar tattaunawa kan wani lamari sai aka samu bambanci sosai fiye da wanda ake samu a tattaunawar da bangarorin biyu suke yi a waje, ba a dakin bincike ba.

Wato idan a dakin bincike ne inda ake lura ko nadar abubuwan da suke fada domin nazari sai a ga bambanci da yawa. Amma idan a mu'amullarsu ce ta yau da kullum ba a ganin bambanci mai yawa.

Wannan na nuna da alamu maza sun fi samun natsuwa a yanayi na muhawara da aka shirya kamar a dakin gwaji, fiye da idan suna maganganunsu a waje.

Abin da binciken Leaper ya gano, ya kara tabbatar da nazarin da aka yi kan wani tarin bincike 56 da wasu masu bincike kan harshe suka yi, Deborah James da Janice Drakich suka wallafa a wani littafi a1993, kan bambanci tsakanin yanayin hira na maza da mata.

Biyu ne daga cikin tarin binciken suka gano cewa mata sun fi maza yawan magana, yayin da 34 suka tabbatar maza ne suka fi magana, akalla dai a wani yanayin.

Sai dai wasu 'yan bambance-bambance da aka rika samu a tsakanin gwaje-gwajen sun sa da wuya a iya kwatanta sakamakon gaba daya.

Tattaunawa ko maganganu da mutane ke yi na yau da kullum suna da wahalar nazari saboda bukatar nadar dukkanin maganganun.

To amma James Pennebaker, na Jami'ar Texas, da ke Austin, a Amurka ya kirkiro wata na'ura da ke nadar maganganun da mutane ke yi na tsawon dakika 30 a duk minti 12 da rabi.

Mutane ba za su iya kashe na'urar ta Pennebaker ba, saboda haka za ta iya samar da bayanin da za a iya dogara da shi.

A bayanan da aka wallafa a mujallar kimiyya ta Science a 2007 Pennebaker ya gano cewa a cikin sa'oi 17 da mata suke gudanar da harkokinsu a Amurka da Megziko (mexico) sun furta kalmomi 16,215 yayin da su kuma maza suka furta 15,669. Harwayau a nan ma bambancin ba shi da yawa.

Sai dai ba duka maganganu ba ne ko tattauna wa suke daya. Kila abin da ke da muhimmanci shi ne wanene yake sauraro.

Wani nazari na daruruwan tarukan jama'a da Janet Holmes ta Jami'ar Victoria ta Wellington da ke New Zealand ta yi, ya nuna maza ne suka yi tambayoyi kashi uku bisa hudu, yayin da suka kasance kashi biyu bisa uku na mahalatta tarukan.

Kuma hatta da aka raba yawan mahalatta taron biyu tsakanin maza da mata, a nan ma mazan su ne suka yi tambayoyi kashi biyu bisa uku.

Duk da wadannan shedu da ake samu da ke nuna sabanin cewa mata sun fi maza yawan magana, da alamu ra'ayinmu ya fi karkata wurin cewa mata sun fi yawan babatu.

A zahirin gaskiya wannan daya ne kawai daga cikin fannoni da dama na rayuwa da muke tsammanin samun bambanci sosai tsakanin jinsin biyu.

To amma idan aka hada sakamakon binciken gaba daya, sai a ga maza da mata kusan daya suke sabanin yadda mutane da yawa suke dauka cewa mata sun fi yawan magana.

Lokacin da a farkon shekara ta 2013 masu bincike suka ruwaito cewa mata 'yan shekara hudu sun fi sa'oinsu maza yawan sinadarin furotin (protein) da jiki ke amfani da shi wajen lakantar harshe da magana a wani sashe na kwakwalwa da kashi 30 cikin dari, wasu gidajen rediyo da talabijin sai kawai suka fassara hakan a matsayin dalilin da ya sa mata suka fi yawan surutu.

Alhalin wannan bincike bai gaya mana komai akan manyan mata ko maza ba game da wannan bambanci.

Yawancin wadanda aka yi wannan bincike a kansu 'ya'yan beraye ne, amma kuma akwai yara kanana guda goma da mata da su ma aka gwada su.

To amma fa hatta su kansu wadanda suka wallafa sakamakon binciken sun yi gargadi kan dogaro sosai da wannan sakamako.

Saboda suna ganin bambancin wannan sinadari da ke kwakwalwa a tsakanin mutane ko zai zama sanadin bambanci wurin lakantar harshe abu ne da ke bukatar karin bincike.

A don haka, za mu iya tambayar cewa to daga ina aka samo bayanin da ke nuna maza suna furta kalmomi 7,000 a rana su kuma mata suna fadar 20,000.

Wannan bayani dai daman yana kunshe ne a littafin masaniya kuma likitar masu tabin hankali, a Jami'ar California ta San Francisco, Louann Brizendine, mai suna 'The Female Brain' wanda ta wallafa a 2006, bayanin da ya kasance ana yawan bayar da misali da shi.

Lokacin da Farfesa Mark Liebermann, masani a fannin harsuna a Jami'ar Pennsylvania, ya kalubalanci wannan bayani na alkaluman na littafin, Brizendine da kanta ta yarda da shi kan rashin dacewar amfani da alkaluman, kuma har ta yi alkawarin ba za ta sanya su ba a sabbin littattafan da za ta buga na gaba.

Liebermann bai tsaya a nan ba, sai da ya yi kokarin bin diddigin alkaluman, amma bai dace ba sosai da samun wani karin bayani, in ban da irinsa da ya samu a wani dan karamin littafi na jagoranci kan aure da aka wallafa a 1993, wanda bai dace da wani bincike na kimiyya ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Prattle of the sexes: Do women talk more than men?