Likitan da ke tiyata daga nisan duniya

Hakkin mallakar hoto st josephs healthcare
Image caption Dokta Mehran Anvari yana yi wa maras lafiya da ke can a wani gari tiyata

Fasaha ta kai ta kawo yanzu likitoci na iya yi wa maras lafiya aiki ta hanyar amfani da butum-butumi daga nisan duniya. Haka tiyata za ta zama kenan nan gaba?

Rose Eveleth ta nitsa bincike;

Lokacin da Mehran Anvari ya dauki kayan tiyata, ya yi wa maras lafiya aiki, bai yi amfani da hannuwansa ba a zahiri. Ba ma ya cikin dakin da maras lafiyar yake. Kai a takaice ma yana yin wannan tiyata ne daga nisan kilomita 400.

Daga asibitin St Joseph da ke Hamilton a kasar Kanada (canada), Anvari yake sarrafa na'urar da take sarrafa butum-butumin (robot) da yake wani garin daban a kasar, ya yanka jikin maras lafiya, ya cire abin da zai cire sannan ya dinke wurin.

Ta wannan hanya likitan ya gudanar da tiyata sama da 20 ya zuwa yanzu, kuma aikin ya hada da na kaba da na matsarmama.

Wannan fasaha ta yin tiyata daga nisan duniya yanzu ta kai yadda za a iya amfani da ita sosai, ta yadda mutane za su iya samun kulawa ta kwararru na duniya a harkar lafiya ba tare da sun yi wata tafiya ba. Ko hakan kenan zai zama yadda za a rika yi a asibitoci?

Hakkin mallakar hoto st josephs healthcare

Lokacin da aka yi tunanin samar da fasahar tiyata ta akwatin talabijin daga nisan wata uwa duniya, ba a kawo tunanin yin hakan a ayyukan asibiti na yau da kullum ba.

A gaskiya ma, abin da ya kawo wannan tunani, abu ne da ya shafi wajen doron wannan duniya da muke ciki.

Tunanin wannan fasaha ya samo asali ne tun lokacin da aka fara duba yuwuwar tafiyar mutum zuwa duniyar wata ko samaniya.

Daga nan ne aka yi tunanin yadda likita zai iya yi wa mutum magani a nisan dubban milamilai ko kuma wata uwa duniya.

A 1970 hukumar kula da samaniya ta Amurka, Nasa, ta bukaci masu bincike su duba yadda za a iya amfani da butum-butumi (robot), a rika yi wa 'yan sama jannati tiyata.

Tun daga wannan lokaci ne hukumar sama jannatin da takwararta ta sojojin Amurkan suka dukufa aikin kirkiro butum-butumin da zai iya yi wa wani tiyata a nesa.

Hakkin mallakar hoto david williams
Image caption Tiyata a kasan teku da butum-butumi

A 2006 ne Dakta Anvari ya yi amfani da wani butum-butumi ya dinke wani rauni da wani mutum da ke can karkashin teku a wani gandun halittun ruwa ya ji, domin kwaikwayon yadda wannan shiri na tiyata tsakanin duniyarmu da duniyar wata ko samaniya zai kasance.

Kamar dai yadda duk wani shiri da ya fara da hukumar samaniya da sojin Amurka yake, shi ma wannan na samar da fasahar yin tiyatar asibitin daga nesa ya shiga ran jama'a farar hula.

A shekara ta 2001 ne aka yi tiyata da ta ratsa tsakanin tekun Atalantika, inda aka yi wa wani maras lafiya da ke Faransa aiki daga asibiti a New York da ke Amurka.

Kuma a shekarun nan tuni har an samar da kusan wannan fasaha a kasuwa, inda ake sayar da butum-butumi mai suna Di Vinci, da zai yi wa maras lafiya tiyata, likitan da ke sarrafa shi kuma yana gefe daya.

To shi butum-butumin likita Anvari mai suna Zeus, yana aiki ne a wani asibiti na unguwa da ba shi da kayan aiki da kwararrun ma'aikata kamar inda shi Anvari yake.

Kan yadda yake sarrafa butum-butumin wajen yin tiyatar daga nisan kusan mil 250 wato kilmoita 400, Anvari ya ce, in ban da bambancin wuri kawai, yana ji ne kamar shi kansa yana cikin dakin da ake yi wa maras lafiyar aiki ne, babu wani bambanci.

Ya ce, ''hannuwana biyu suna rike da na'urar da ke sarrafa butum-butumin kamar yadda zan rike kayan tiyatar.''

Yana motsa na'urar da ke nuna hoton yadda aikin ke gudana, wadda ita ce kamar idonsa (likitan), kuma zai iya magana da ma'aikatan jiyyar da ke dakin, har ya ba su wani umarni.

Hakkin mallakar hoto st josephs healthcare

Wannan fasaha za ta fi gudana yadda ya kamata ne ta hanyar samar da layin wayar tarho irin wanda ake amfani da shi a tebur wato ba wayar salula ba, tare kuma da intanet mai karfin gaske.

Duka domin gudun katsewar sadarwa, saboda idan aka gamu da tangardar sadarwa ko katsewa matsala za ta auku.

Domin kamar yadda Tamas Haidegger, mai bincike a Jami'ar Obuda da ke Budapest wanda ke nazari kan irin wannan tiyata a sararin samaniya, ya ce, ''ba abu ne mai yuwuwa ba, ka yi tsammanin idan sadarwar ta katse, butum-butumin ya ci gaba da gudanar da aikin kai tsaye da kansa har ya kammala tiyatar.''

Ya kara da cewa, wannan lalle kam za ta iya zama babbar matsala, musamman ma idan maras lafiyar da ake yi wa tiyatar yana wani wuri mai nisan gaske ne, kamar can sararin samaniya ko duniyar Mas (mars)

Sai dai Mangai Prabakar, injiniya a Jami'ar Florida International, wadda kuma ke kera butum-butumi na musamman, ta ce, a irin wannan yanayi, butum-butumi zai iya amfani da bayanan da aka tanadar a rumbu da kuma tsari na musamman da aka tanadar na samun mafita a wata matsala (formula,algorithms ) wajen karasa tiyatar.

Amma kuma kwararriyar ta ce, ''duniyar Mas da wani sashen na samaniya na da nisa sosai kuma ba za mu iya sadarwa tsakanin wannan nisa ba.''

Ta ce, abin da zai fi kawai shi ne, a samar da butum-butumi da muka yarda zai iya yin tiyata, ba tare da jagorancin mutum daga doron duniya ba. Kuma wannan na bukatar kwamfutoci masu karfin gaske.

Butum-butumin likita

Ita dai tiyata aba ce mai wuyar gaske. ''Za ka iya yin kyakkyawan tsari na yin wata tiyata kuma duk da haka a samu matsala a aikin.'' In ji Haidegger.

'' Ba za mu iya hasashen abin da zai faru ba yayin da aka yi nisa da tiyata. Idan jini ya balle ko numfashi ya tsaya ko kuma wata matsala ta tasirin magani wadda ba a yi tsammani ba ta taso, duka wadannan matsaloli ne da ke bukatar a ce akwai kwararren likita da ke kusa.''

Sai dai duk da haka Haidegger ya yi amanna cewa, a hankali a hankali, za a kai ga samar da butum-butumi da za a yi masa kwakwalwa ko fasaha da zai yi aiki da kansa, wanda kuma za a rika sarrafa shi daga wani wuri daban.

Kuma za a rika bukatar wannan butum-butumi sosai, wanda bukatar ka iya zuwa daga sararin samaniya ko doron duniyar nan tamu.

Bunkasar kasuwancin safarar jama'a zuwa sararin samaniya ta haifar da batutuwa da dama da ke bukatar dubawa a game da fasahar tiyata ta hanyar sadarwa ta amfani da butum-butumi.

Ganin cewa mutane masu shekaru daban-daban na son wannan safara ta zuwa sararin samaniya, akwai yuwuwar wani yanayi ya taso da za a bukaci yi wa wani irin wannan tiyata ta nesa.

Hakkin mallakar hoto st josephs healthcare
Image caption Likita na tiyata da fasahar butum-butumin Da Vinci

A halin yanzu dai ana samun karin likitoci a nan doron duniya da ke nuna sha'awar amfani da wannan fasaha, ta yi wa maras lafiya magani daga wani wuri daban.

Kuma nan da shekara ta 2025, ma'aikatar tsaro ta Amurka tana son samar da wani tsari da zai bayar da damar da likitoci za su yi wa sojoji tiyata daga nesa.

To ko nan gaba za a rika yin tiyata ne daga nesa, inda maras lafiya zai kasance a wani asibiti ko ma wani gari ko kuma ma wata duniyar ta samaniya daban, likitan kuma yana wata duniyar?

''Tuni an riga an samu kimiyyar yin hakan,'' in ji Anvari, ''sauran abin shi ne, wanda yake rike mu.''

Matsalolin sun hada da na ka'idar aiki da sauran dokoki. A haka, wannan fasaha za ta iya haifar da yanayi na yadda mutane ke tururuwa zuwa wasu wurare ko kasashe don neman magani.

Misali marassa lafiyar da ba za su iya biyan kudin tiyata a Amurka ba, sai su nemi likitocin wasu kasashe.

Kuma idan aka samu matsala a aikin, wa za a dora wa laifi, wadanda suke dakin da butum-butumi ke tiyatar ko kuma likitocin da ke Cuba?

Watakila ma babban abin dubawa shi ne, ko hankalin marassa lafiya ma zai kwanta da likitan da ba su taba gani ido da ido ba.

Za ka taba yarda likita ya cire maka koda, ko ya yi maka aiki a zuciyarka daga can wani wuri mai nisan uwa-duniya (daruruwan kilomita)?

Nan gaba kadan za a yi maka wannan tambaya, sai ka tanadi amsa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The surgeon who operates from 400km away