Gashi da farcenka na cigaba da fitowa bayan ka mutu?

Hakkin mallakar hoto Getty

Domin gano gaskiyar hakan ko akasi muna bukatar duba yadda likitoci ke aikin dashen sassan mutum. Claudia Hammond ta duba mana.

Zuciyarka ta tsaya, jininka ya yi sanyi kuma yatsunka sun kame. Amma duk da wadannan alamu da ke nuna ka mutu, farcenka ya ci gaba da tsawo haka shi ma gashinka. kamar dai yadda ake gaya mana.

Irin wannan abu shi ne muke gani a fina-finai na ban tsoro kuma muke karantawa a wasu littattafai su ma na labarai irin na wadannan fina-finai kamar littafin Erich Maria Remarque mai suna, ''All Quiet on the Western Front.''

A wannan littafi mai bayar da labarin cikinsa ya bayyana yadda ya yi tunanin faratan abokinsa wanda ya mutu suka ci gaba da fitowa kamar yadda gashin kansa ma ya yi ta toho kamar ciyawa. To anya hakan gaskiya ne?

To ba mamaki dai daman cewa babu wani bincike mai yawa na musamman da aka yi a kan auna karuwar kullum da farce da gashi suke yi a jikin mutumin da ya mutu.

Domin samun dan wani abu ma iya duba rubuce-rubuce da bayanan da daliban aikin likita da suke aiki da suke ta'ammali da gawawwaki.

Haka suma likitoci masu dashen sassan dan-adam suna da kwarewa wajen lissafin tsawon lokacin da sassan mutum daban-daban ke dauka suna aiki bayan mutuwarsa.

Kwayar halitta ta kowane sashe na jikin mutum tana da lokacin da take mutuwa daban da wata.

Bayan zuciya ta daina bugawa, an yanke hanyar kai iska zuwa cikin kwakwalwa, su kuma kwayoyin halittar tsigar jiki za su mutu a tsakanin minti uku zuwa bakwai saboda babu sauran abincin da za su rayu da shi.

Dole ne likitocin dashen jikin dan-adam su cire koda da hanta da kuma zuciya daga jikin mutumin da ya bayar da su, cikin minti 30 da mutuwarsa a kuma dasa su a jikin wanda za a sanya wa a tsawon sa'a shida.

Kwayoyin halitta na fata su kuwa suna dadewa kafin su mutu, saboda haka za a iya yankar fata daga jikin wanda ya mutu a yi amfani da ita a jikin wani sa'oi 12 bayan ya mutu.

To amma shi kuwa farce ba ya girma sai an samu sabbin kwayar halitta, kuma hakan ba za ta yuwu ba tun da babu sauran sinadarin sukari(glucose) a jikin wanda ya mutu.

Shi farce yana girman digo daya na milimita (0.1mm) a duk rana, wanda kuma hakan yana raguwa yayin da muke kara shekaru.

Wata fata da ke karkashin farce ita ce take samar da yawancin kwayoyin halittar da sabon farce ke fitowa daga su.

Sabbin kwayoyin halittar na farce suna tura tsoffin gaba ne wanda hakan yake sa a rika ganin farcen yana tohowa daga ciki.

To mutuwa tana dakatar da aikawa da sinadarin sukari (glucose) wannan wuri da kwayar halittar da ke samar da wadda ke fitar da farce take saboda haka farce ba zai ci gaba da girma ba ke nan idan an mutu.

Haka ita ma suma ko gashin kai wannan salo ko tsari take bi wajen toho. Iskar da zuciya take turawa kwakwalwa ita take taimakawa wajen sarrafa sinadarin sukari na jikin mutum a samu kwayoyin halittar da gashi zai samu daga cikinsu. To ita ma suma ko gashi da zarar zuciya ta tsaya da aiki saboda mutuwa sai wannan iska da ke zuwa kwakwalwa ta katse a daina samun wannan aiki da ke samar da kwayoyin halittar da gashi ke fita daga cikinsu.

To tun da yadda haka farce da gashi suke samuwa a jikin mutum kuma idan ba rai sai ayyukan su dakata, ta yaya ke nan almarar cewa gashi da farce na ci gaba da fitowa a jikin mutumin da ya mutu ke ci gaba da bazuwa?

Da farko dai wannan magana ko almara ba gaskiya ba ce, amma tana da tushe a kimiyya.

Bayanin shi ne ba wai farce da gashin ba ne suke ci gaba da fitowa ba ko alama, abin da ke kasancewa shi ne, fatar da ke kewaye da su ita ce ke motsewa ta yi baya tun da ruwan jikinta yana ta bushewa, sai hakan ya sa a ga kamar gashi da farcen ne suke kara fitowa.

Masu yi wa gawa sutura a wani lokacin sukan shafawa yatsun gawa mai domin hana motsewar fatar.

Saboda haka idan zuciyarka ta damu da irin bayanan da kake karantawa da hotunan da kake gani a fina-finan ban tsoro na gawawwaki da farce zako-zako da gashi biya-biya to hankalinka ya kwanta, domin wannan abu ne kawai da ake gani a fim amma ba a duniya ta zahiri ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi to latsa nan Do your hair and fingernails grow after death?