Me yake sa mu dariya?

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan tambaya ce mai sauki amma kuma abin mamaki mai wuya ko sarkakiyar amsa. Domin fahimtar dariya na nufin fahimtar muhimman abubuwa a kan yanayi ko halittar dan-adam.

Tom Stafford ya bincika.

Me ya sa muke dariya? To! Ita kanta wannan tambaya abar dariya ce, amma dai tambaya ce da wani mai karatu Andrew Martin, ya kawo shawarar a duba ta, kuma tana da muhimmanci ga bincike.

Domin tambaya ce wadda da farko kamar mai saukin amsawa amma kuma daga baya ta za mo mai wuyar amsawa ko kuma akalla mai amsar da ke da sarkakiya, wadda ta sa mu tattaki har zuwa kokarin fahimtar yanayi ko halittar dan-adam shi kansa.

Mutane da yawa za su iya cewa muna dariya ne saboda wani abin ban dariya. To amma idan ka lura da mutane da kyau lokacin da suke dariya za ka ga ba haka abin yake ba.

Kwararre a kan sanin dariya Robert Provine, ya dauki sa'oi masu yawa yana nadar maganganu a manyan kantuna da ajujuwa da ofisoshi da wuraren liyafa, inda ya gano cewa yawancin dariya da mutane ke yi ba suna yin ta ba ne saboda wani abin ban dariya.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Mutane suna dariya a karshen maganganu da muka saba yi yau da kullum, dalilin wasu kalamai ko tambayoyi ba na ban dariya ba. Misali kamar '' Duba Andre ne,'' ko kuma a ce '' Ka tabbata?''.

Hatta kokarin yin wata magana mai ban dariya wanda ya sa dariyar idan ka duba za ka ga a zahiri ba wani abin ban dariya ba ne.

Provine ya ruwaito cewa 'yan maganganun ma da suke jawo dariya sosai su ne kamar '' Kai ba sai ka sha wani abu ba, kawai mu za ka saya wa.''

Ina ganin ba za ka fahimci wannan magana ba sosai sai ka gani da idonka.

Saboda haka idan har muna son mu fahimci dariya, watakila sai mun kara nutsawa a bincikenmu mu duba abin da ke faruwa a cikin kwakwalwa.

Bangarorin da ke tsara dariya suna can ciki-cikin kwakwalwa ne, kuma idan ana maganar sauyi ne na halitta har zuwa lokacin da aka samu dan-adam, wadannan bangarori suna nan tun zamanin da, kuma su ne ke da alhakin numfashi da motsin jiki.

Wannan na nufin kenan bangarorin da ke kula da dariya suna yanki ne da yake nesa sosai daga yankunan da suka samu a kwakwalwar, daga baya, wadanda kuma suke kula da manyan ayyuka kamar yare ko harshe ko ma haddar mutum.

Watakila wannan shi ne dalilin da ya sa yake da wuya ka iya danne dariya ko da kuwa ka san cewa ba ta dace ba.

Da zarar dariya ta taso daga can cikin wannan wuri na kwakwalwarmu ba wani bangare na kwakwalwar da zai iya hana ta tabbata.

Haka kuma a daya bangaren abu ne mai wuya ka iya kirkirar dariya haka kawai, wato idan aka bukace ka ka yi kenan.

Idan ma har ka yi kokarin dariyar to za a ga ba ta yi daidai da dariya ta gaskiya ba, akalla daga farkonta.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Akwai kuma wani muhimmin bangare na dariya. Dukkanin mutane suna dariya, kuma dariya a ko da yaushe ta kunshi salo iri daya ne na kara mai yawa.

Hatta kurame ma wadanda ba su taba jin wani sauti ko kara ba, su ma suna yin kara na dariya.

Karan dariya da mutane ke yi yayi kama sosai da yanayi na magana, wanda wannan karin sheda ne da ke tabbatar da cewa dariya, tana da iko da bangarorin kwakwalwa da na jiki wadanda muke amfani da su wajen numfashi da magana.

To amma wannan ba yana nufin cewa hakan amsa ce ga tambayarmu ta ainahi ba (Me ke sa mu dariya?).

Ko da mun gano ainahin wuraren da ke kula da dariya a kwakwalwa, kuma ko da mun iya sa mutum ya yi dariya ta hanyar zaburar da wadannan bangarori (wanda za a iya yi) har yanzu ba mu san ainahin abin da ke sa mutane dariya ba.

Eh! Ba shakka mun san abin da dariyar ke haifarwa, to amma me ke haifar da ita, wato, dalilin da ke sa muke ita kanta dariyar?

Domin amsa wannan tambaya watakila muna bukatar mu duba wasu abubuwan da ke wajen jikin dan-adam din, wato abubuwan mu'amullar mutum da ke aiki idan yana dariya.

Idan ba a manta ba tun a baya na yi maganar nazarin Farfesa Provine, na dariya a yanayin harkokin mutane na yau da kullum da suke yinta.

Provine a wannan nazari ya nuna cewa ana amfani da dariya ne wurin yin wakafi ko aya a magana ba kawai ana yinta ba ne sakaka yadda za ta rika katsalandan a magana ba.

Wannan na nufin tana taka muhimmiyar rawa ta sadarwa, wato ba wai wata aba ce mai zaman kanta da ba ta da danganta ko alaka da tattaunawar da mutane ke yi ba, wadda za a ce kawai tana faruwa ne yayin da muke magana da wani.

Masanin ya kuma gano cewa, yawanci mai jawabi ya fi yawan dariya fiye da masu saurare.

Kuma an fi yin dariya a yanayin da ake da kwanciyar hankali da kuma yanayin da mutane suke da yawa.

Wannan duka yana kara nuna muhimmancin da dariya take da shi a mu'amullar mutane.

Kuma ba ko da yaushe ba ne ake yinta domin wani abu na alheri.

Saboda duk da farin ciki da nishadi da annashuwa da ke tattare da yin dariya, tana da wani bangare maras kyau, inda ake yi wa mutum dariyar mugunta ko kuma ta reni.

Watakila abu mafi muhimmanci a dariya da ke hada jama'a shi ne yadda take yaduwa daga mutum zuwa mutum.

Sauraren mutumin da yake dariya shi kadai ma abin ban dariya ne.

Domin jarraba hakan, ka yi kokarin daure fuskarka (ba dariya) lokacin da kake kallon wani fim misali inda wani mutum yake yi wa goggon biri cakulkuli.

Kai da kanka za ka ba wa kanka dariya. Ka fara da dariyar dole ko ta karya, idan ka ci gaba da yi, kafin ka farga za ka ga ka shiga ta sosai.

Abin da wannan tarin bincike ke nunawa shi ne, dariya tana da muhimmancin gaske a mu'amullar mutane.

Kuma tana da tushe a can cikin kwakwalwarmu, a bangaren da tun asalin halittar da masana ke cewa ta rika sauyawa daki-daki har ta zama mutum akwai shi a kwakwalwar.

Muna dariya saboda muna son yinta, ko saboda kwakwalwarmu ta sa mu yi da kuma saboda bukatar mu zama daya da sauran mutane.

Dukkanin wadannan dalilai haka suke. Amma masana sun ware akalla muhimman amsoshi hudu da za ka iya bayarwa domin bayanin dabi'ar ta dariya.

Amsoshin su ne na wadannan tambayoyi: ''Me ya sa ta faro?'' da''ta yaya ta faro?'' da ''Ta yaya ta ci gaba da kasancewa duk tsawon wannan rayuwa?'' da kuma '' Yaya take aiki?''

Wannan bincike ya bayar da wasu amsoshin tambaya ta farko (dariya ta faro ne domin mu'amullar jama'a) da kuma tambaya ta karshe (sassan kwakwalwa da ke tafiyar da numfashi da magana su ne ke tafiyar da ita).

To amma ko da daga yadda wadannan amsoshi na tambayoyin biyu suka fara, ka san cewa ko alama ba a kama hanyar amsa sauran biyun ba.

A duk lokacin da muka kusa samun amsar wata muhimmiyar tambaya, sai hakan ya kara zurfafa fargabar da muke da ita ta kalubalen da ya rage na amsa sauran.

Ba abin da za mu ce sai godiya ga mutumin da ya kawo shawarar bincika wannan magana (Me yake sa mu dariya) Andrew Martin.

Idan kana da wata shawara mika ta ga tom@mindhacks.com

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What makes us laugh?