Mura cutar 'yan gata?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wasu kan ce mura cutar 'yan gata yayin da a wata al'adar kuma ake cewa idan kana mura yi ta dibar girkinka, idan ko zazzabi ne to kyale abinci.

Claudia Hammond ta bincika mana wannan magana

A haka maganar nan da wasu ke yi cewa idan muna mura mu yi ta cin abinci, amma kuma ka da mu ci idan zazzabi mu ke yi, tana da alamun gaskiya a ta wani fannin. Tun da zazzabi yakan dauki kwana daya ne ko biyu kuma ba ka jin dandano a wannan lokacin cin abinci kadan ba wani abu ba ne mai wuya.

Ita mura kuwa ta kan dauki kwanaki tsakanin bakwai da goma saboda haka kana bukatar abinci wanda idan ba ka ci ba jikinka zai yi rauni kuma ba ka da kuzari.

To hakan kenan abu ne da za a iya yi, to amma akwai wata sheda da ke tabbatar da cewa idan ka yi hakan za ka samu sauki da wuri?

Ba kayan abinci na ruwa na da muhimmanci sosai kuma sune kayan abincin da ke sa kwayoyin halittar jiki su yi aiki.

To amma kuma galibi rashin lafiya na sa mutum ya rasa dandano a bakinsa gaba daya, kuma an ce wannan rashin cin abinci na taimakawa wajen kara bunkasa garkuwar jiki.

To amma idan haka lamarin yake, me zai sa kin cin abinci ya jawo hakan a lokacin da ba mu da lafiya kawai.

Wani nazari da aka yi can baya a shekara ta 2002 ya sa jaridu sun rika fitar da kanun labarai iri daban-daban da ke nuna cewa, da ala dai maganar da ake cewa '' ciyar da mura, ka sa zazzabi yunwa,'' ga alama ba almara ba ce.

Masana kimiyya na kasar Holland sun umarci wasu mutane da za su yi gwaji a kansu da ka da su ci abinci da daddare kafin so zo dakinsu na gwaji a jarraba su a lokuta biyu daban-daban.

A ziyararsu ta farko an ba su abinci na ruwa-ruwa, yayin da a karo na biyu kuwa aka ba su ruwa kawai.

Gwajin jinin da aka yi musu bayan sun ci abincin mai rwa-ruwa an gano cewa sinadarin (gamma interferon) da ke kara karfafa garkuwar jiki musamman mai yaki da kwayoyin cutar bairus(virus) mai sa mura, ya karu da kusan kashi 450 cikin dari.

Haka kuma a gwajin da aka yi wa mutanen bayan sun sha ruwan kawai sai aka ga raguwar wannan sinadari mai bunkasa garkuwar jikin.

A wani binciken kuma an gano cewa azumi yana jawo karin wani sinadarin (interleukin-4) mai kara garkuwar jiki har akalla linki hudu.

Fiye da karin da aka gani bayan da aka ba mutanen abinci mai ruwa-ruwa suka karya da shi bayan sun kaurace wa abinci da daddare.

Shi wannan sinadari (interleukin-4) yana taka muhimmiyar rawa ne wajen yaki da cutukan da kwayar baktiriya(bacteria) ke yadawa a jini da tsoka.

Dangane da wannan abu da aka gano, idan mutum ya ci gaba da cin abinci kenan a lokacin da yake mura yana kara samun garkuwa daga kwayoyin cutar da ke damun mutum a lokacin murar.

A daya bangaren kuwa, shi zazzabi da kwayar cutar baktiriya ke jawo shi, rashin cin abinci kenan shi kuma yana maganinsa, ta hanyar samun karin garkuwar jikin da rashin cin abinci ko azumi ke jawowa.

Wannan bincike na masana kimiyyar na kasar Holland ya bayar da madogara kenan ga wadanda suka yarda da waccan magana. Sai dai fa abin ba haka yake da sauki ba kamar yadda za a dauka.

Saboda idan aka duba abin da yawanci ke jawo zazzabi mura ce, wadda ita kuma kwayar cutar bairus (virus) ke haddasa ta, ka ga kenan wancan nazari bai yi daidai ba a nan.

Kuma ma bayan haka wannan dan karamin nazari ne da aka gudanar da shi da mutane shida kawai.

Sannan shi kansa masanin da ya jagoranci gudanar da shi Gijis van den Brink, ya gargadi mutane da ka da su sauya yanayin cin abinci bisa dogaro da wannan nazari.

Akwai kuma wata shedar wadda aka samu daga gwajin da aka yi a kan beraye, wadda ke nuna cewa idan kashi 40 cikin dari kawai na kwayar abincin da ya kamata a ci a rana aka ci, hakan ba kawai yana kara wa bera hadarin kamuwa da mura ba ne, idan zai sa ya dade bai warke ba.

Ko da yake dai akwai kuma binciken da ke nuna cewa takaita yawan abincin da ake ci a rana na kara tsawon rayuwar kananan berayen nan da kashi 20 cikin dari, yayin da shi kuwa katon bera rayuwar tasa ke karuwa da kashi 30 cikin dari.

Kuma hakan na rage musu yuwuwar yawan fitowar kurji a jikinsu.

Idan kuma ana maganar hadarin kamuwa da mura ne sheda ta nuna cewa, ya fi dacewa da kananan beraye su fi abinci sosai.

Idan muka sake dawowa kan mutane kuma, bincike ya nuna babu wata sheda ta kimiyya da ta jaddada wannan magana (ci abinci idan kana mura, idan zazzabi ne kuwa ka da ka ci abinci).

A fannin tarihin adabi da harshe ma, akwai muhawara sosai a kan asalin maganar, inda da yawa ake cewa hatta a cikin tarin labarai na karni na 14 babu maganar.

Akwai maganganun ma da ke cewa an sauya asalin yadda fassarar maganar take ne.

Inda suke cewa an yi nufin a ce, ''ciyar da mura zai kawar da zazzabi '' ne.

Ga wadanda suke son sanin cikakkiyar amsa dole sai su jira sai mun san sarkakiyar da ke tattare da garkuwar jikinmu.

Kafin sannan sha'awarka da abinci ita ce babbar jagorarka ta cin abinci.

Ko kana mura ko kuma kana zazzabi ne abu ne mai muhimmanci dai ka rika ci ko shan abinci na dangin ruwa.

A game da abinci mai nauyi kuwa za ka so jin jikinka da karfi idan har za ka iya, amma dai ya dogara da abin da za ka iya ci.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Feed a cold, starve a fever?