Kamfanin jirgin sama ya taba gwanjon kayanka?

Hakkin mallakar hoto Blend images Alamy stock

Idan kamfanonin jirgin sama suka kasa gano masu kaya, a wani lokacin sai su aika da su kamfanonin gwanjo.

Brendan Cole ya halarci wurin sayar da irin wadannan kayayyaki, inda ya gana da mutanen da ke sayen kayan fasinjojin da aka rasa masu su.

Bayan doguwar tafiya a jirgin sama, wadda ta kunshi sauyin abinci da iskar da mutum yake shaka da dai sauran abubuwa na daban da ke tattare da kasancewa a cikin wannan sunduki a sararin samaniya daga nahiya zuwa wata nahiya ko daga kasa zuwa wata kasa, ba abin da mutum ke bukata da zarar ya ji sun dawo tudun kasa illa ya kama hanyar otal din da zai sauka ko kuma ya nufi gidansa.

Ba mamaki a irin wannan hanzari ka ga fasinja ya manta wani kayansa ko wata daga cikin jakunkunansa.

Idan muka yi la'akari da yawan jakunkunan da suke bi ta filayen jiragen sama na duniya za mu ga cewa samun nasarar kowane fasinja ya tafi da jakarsa ba zago ba gara ballantana bata har 993 a cikin 1000 ba wani abin damuwa ba ne.

Abin damuwar shi ne sauran bakwai din da za su cike dubun sun karkata sun nufi wani wuri ba hannun masu su ba.

To a Birtaniya a nan ne maganar gidajen buga gwanjo ta shigo.

Idan aka yi gwanjon jakar sai kamfanin gwanjon ya dauki kasonsa sannan ya mika wa kamfanin jirgin sauran kudin.

A Birtaniyan kamfanonin gwanjo hudu ne suke wannan hada-hada ta sayar da kayan fasinjojin jirgin sama da aka manta.

Daya daga cikin wadannan kamfanoni shi ne Tooting Greasby, wanda kowace Talata, kusan mutane 150 suke biyan kafin alkalami na fam 100 domin karbar wata lamba wadda za ta ba su damar shiga wannan ciniki.

A bayan dakin da ake buga gwanjon akwai akwatuna (suitcase) guda 20 da sauran wasu jakunkuna.

Wasu sababbi ne wasu kuwa sun ji jiki, amma dai dukkaninsu suna hankalin masu son sayen nan ne.

A ranar wata Talata nan kusa, na ga tarin tarkaci da suka hada da tarin lema da kwagiri da kekunan yara kai har ma da kunzugun yara duk an tara kusa da akwatunan.

Ga dai tarkace nan iri daban-daban wadanda ko dai an rasa masu su ko kuma jami'an tsaro sun kwace su a yayin shiga jirgi ko kuma dai an manta su a zauren matafiya kafin a shiga jirgi.

''Abin sha'awa ne irin kayayyakin da mutane ke dawowa da su idan sun je hutu'' in ji ma'aikaciyar kamfanin buga gwanjon Christine Sachett wadda sama da shekara 40 tana wannan aiki, take gaya wa masu son sayen gwanjon.

A wasu kasashen kamfanonin jiragen saman suna lalata kayan ne. Amma a Biritaniya suna tura su kamfanonin buga gwanjo, in ji Nick Gates darektan wani kamfanin sadarwa na filin jirgin sama a Birtaniya.

Idan wani fasija ya bayar da rahoton batan kayansa, sai a shiga amfani da na'urar tsarin gano kayayyaki a duniya, wadda duk wani babban kamfanin jirgin sama ke amfani da ita.

Za ta yi kokarin gano jaka ko akwatin mutum ne ta hanyar lalubo takardar lambar da aka makalawa kayan da launin jakar da kuma irin jakar a cikin katafaren rumbun da aka tara bayanan kayan da aka manta da su a jirgin sama na duniya.

Idan aka samu kayan sai a kawo wa mai shi. Amma a wani lokaci da wuya a cikin nema 3,000 a dace da daya.

Hakkin mallakar hoto alamy

''Kamfanonin jiragen sama suna dagewa wajen neman masu kaya har tsawon kwanaki dari daya, wanda bayan kwanakin idan ba a dace ba sai a ayyana kayan a matsayin batattu. In ji Nick Gates

Ya ce, '' ya zuwa wannan lokacin kamfanin ya yi duk iya kokarinsa na gano mai kayan. Za ta iya kasancewa saboda babu wata takarda mai lamba ne ko wani abu a cikin kayan da za a iya gano mai shi.

To daga nan fa abin da za a yi da kayan ya dogara daga tsarin kasar.''

A Biritaniya inda ake gwanjon kayan, sai ka yi abu da hanzari wato ka zabi kayan da kake so da wuri kuma fa ba tare da kasan abin da yake ciki ba.

A kamfanin Greasby, da farkon farawa za ka ga ana taya wasu kayan a kananan farashi.

Kayan da sun hada da na sata, wadanda 'yan sanda suka kama da kayayyakin kamfanoni da suka rufe ko kuma kayayyakin da suka yi wa fasinjoji yawa sai dole sun zubar da su a wajen awo.

Bayan wani dan lokaci sai hada-hada ta kankama ta taya kayayyakin har a kai ga sallamawa.

Yawanci ana fara tayin ne da £10 (fan 10), har a rika karawa da fan biyu ko uku.

Da yawa cikin kayayyakin ana gama cinikinsu ne cikin dakika 30 dole ne sai ka yi da sauri in ba haka ba wani ya riga ka.

Ko da yake masu saye za su iya duba jakunkunan wadanda suke a kulle, kafin a fara buga gwanjonsu to amma ba dama ka leka cikinsu.

Duk da yadda mutane suke nuna sha'awa da zakuwa da cinikin abu ne mai wuyar gaske ka samu kaya masu dan karen tsada kamar agogon Rolex ko Gucci da makamantansu.

Saboda irin wadannan kayayyakin su ana fitar da su daga cikin jakunkunan a yi gwanjonsu daban a wurin.

Amma dai ana barin tufafi da takalma da makamantansu masu tsada a cikin kayan.

Wannan ba yana nufin cewa harkar ba ta da riba ba ne fa. Domin kamar yadda wadanda suka zo sayen kayan suka ce, za ka iya samun riba sosai idan ka dace daga akwatin tufafi daya idan ka sayar.

Amma burin masu sayen shi ne su dace da kayan da aka bari kafin fasinja ya tashi ba wanda ya dawo ba.

Ko da yake dai su ma na fasinjan da ya dawo (masu datti) ba abin da zai gagari sabulun wanki a jikinsu.

Hakkin mallakar hoto Brendan Cole
Image caption Kayan da fasinjoji suka manta da su a filin jirgin sama wadanda za a yi gwanjonsu a kamfanin Bristol Commercial Valuers and Auctioneers na Biritaniya

Wata mai shirya fim Meli Iconic-Alonzi da ta fito daga Acton Town na Landan, sau hudu tana zuwa gwanjon, kuma ta yi nasarar sayen akwatuna biyu daya a kan fan 18 daya kuma a kan fan 30.

Ta ce tana sayen yawancin kayan ne domin shirinta na fim ko kuma ta saya wa abokanta da ke aiki a fannin kwalliyar tufafin fim.

Ta kara da cewa, to amma fa ba ka da wata tabbas a kan abin da za ka gani a akwatin da ka saya.

Ta yi bayanin cewa,'' a baya na taba sayen akwatunan da ke cike da tawul-tawul masu araha wadanda ko da wuraren kayan agaji ka kai su ba kowa ne zai so ya karba ba.''

''ba ka da damar duba cikin akwatunan abin rabo ne kawai.'' Ta ce.

To amma wata budurwa mai shekara 17, wadda zuwanta na farko ke nan, ta yi dace da samun takalma da tufafi masu tsada samfurin Chanel.

''Ban san abin da ya sa mutane suke barin irin wadannan abubuwa masu tsadar gaske ba'' in ji ta.

Wani wurin kuma da ake kai kayayyakin da fasinjojin jiragen sama ke mantawa shi ne kamfanin buga gwanjo na Bristol Commercial Valuers and Auctioneers.

Tsarin da ake bi a can ya bambanta inji wani darekan wurin Sam Ewing.

A nan kamfanin yana barin masu sha'awar sayen kayan su duba su kafin a buga gwanjonsu.

Sannan kuma suna ware kayan ne daraja-daraja kamar kayan laturoni daban kayan karau ma daban.

Kayayyakin da aka manta da su ko jami'an tsaro suka kwace su kamar manyan wayoyin salula da belet-belet da agoguna da barasa mai tsada kamar shamfen (champagne) da ire-irenta da katan-katan na taba su ma ana gwanjon nasu.

Hakkin mallakar hoto Brendan Cole
Image caption Mai buga gwanjo na kamfanin Commercial Valuers and Auctioneers na Bristol, Sam Ewing

Daga cikin kayayyakin gwanjon a nan har da wani tsohon zoben namiji na aure wanda ga alama mai shi ya manta shi ne cikin gaggawa kafin ya hau jirgi kuma yana da kankanta da wuya a gano shi.

Alex Fennel daga Bristol ya kashe fan 750 wajen sayen akwatuna, wadanda yake sa ran sayar da kayan da ke cikinsu ta intanet a linki biyu ko ma uku na farashin da ya saye su.

''Ni wannan wani kasuwanci ne a wurina. Abin shi ne za ka iya dace ka samu kaya masu daraja, ko da yaushe kana fatan dace da wani abu,'' ya ce.

''A wani lokacin kananan kaya 'yan ciki za ka samu masu datti (singileti ko duras ko fatari ko rigar nono)''

Duk da yadda buga gwanjon ke jawo mutane masu sha'awarsa ba da wuya a ce an ci gaba da yinsa har abada.

Domin an samu raguwar yawan kayan da suke bata a filin jirgin sama a yanzu.

Saboda fasahar da ake amfani da ita a filayen a yanzu kusan rabin yawan kayan da suka bata a shekaru takwas da suka gabata, su ne suka bata a yanzu.

Kuma duk da haka ma dai a yanzun idan kana yawan tafiye-tafiye ta jirgin sama, ka san cewa zuwa wani dan lokaci akwatinka ba za ta kara kasancewa a hannun kamfanonin buga gwanjo ba.

Duk da haka kuma dai kafin a kai ga wannan lokacin ma, akwai hanyar da ba za ka rasa kayanka ba idan za ka yi tafiya ta jirgin sama nan gaba.

Ka bi ta Osaka da ke Japan ta filin jirgin sama na Kansai. Tun da aka bude wannan filin jirgin sama a 1994 ba samu rahoton batan ko da kaya daya ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Did an airline auction off your luggage?