Karamin sani kukumi

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ji da kai na kai mutum ga borin kunya da nadama?

Masana tunanin dan-adam sun nuna cewa mutane ba sa iya yi wa kansu adalci idan ana maganar kokari a fagen ilimi zuwa iya barkwanci. Wadanda ba su kai kowa iyawa ba su suke ganin sun fi kowa iyawa.

Ga binciken Tom Stafford:

Kana ganin kai kwararre ne ko? Kuma kana da wayo da dabara da iya bayar da dariya duka. Ba shakka haka kake kamar yadda ni ma nake.

Amma ba ka jin wannan zai zama abin takaici idan ya kasance ba mu kai yadda muka dauki kan namu ba?

Masana tunanin dan-adam sun nuna cewa ba kasafai muke sanin gazawarmu ko kuma jahilcinmu ba.

Watakila wannan shi ne dalilin da ya sa wadansu mutanen da ba su da cancanta suke da ban takaici tare kuma da dora wa kanmu girman kai, da kai kanmu inda ba mu kai ba.

A 1999, Justin Kruger da David Dunning, daga Jami'ar Cornell, da ke New York, sun gudanar da jarrabawa domin su gano cewa ko mutanen da ba su da kwarewa a kan wani abu, ba su da kuma masaniya a kan wannan rashin ilimi nasu (ko wadanda ba su sani ba kuma ba su san ba su sani ba).

A farkon rahoton bincikensu masanan sun bayar da misalin wani dan fashi da makami na bankin Pittsburgh, McArthur Wheeler, wanda aka kama a 1995 jim kadan bayan fashin da ya yi a bankuna biyu da rana tsaka, ba tare da ya yi bad da kama ba(rufe fuskarsa).

Lokacin da 'yan sanda suka nuna masa hoton bidiyon fashin da ya yi, sai ya musanta da cewa ''Amma ai na yi shashatau'' (da ruwan lemo da ya shafa a fuskarsa).

Gogan naka ya yi amanna cewa idan ka shafa ruwan lemo a fuskarka na'urar daukar hoto ta tsaro ba za ta iya ganinka ba.

Kruger da Dunning, sun kuma kawo misalin wani abin dariyar kamar wannan, inda suka bukaci kwararrun masu barkwanci su ware wadanda suka fi a tsakanin wasu labaran ban dariya 30.

Sannan kuma sai aka sa wasu dalibai masu karatun digiri na farko 65, su ma su fitar da labaran da suka fi ban dariya a tsakanin wadannan 30 din.

Bayan duka bangarorin biyu kowa ya yi nasa, sai masanan biyu suka auna kokarin daliban da na kwararun masu ban dariyar.

Masanan biyu sun kuma tambayi daliban kan yadda suke ganin kokarinsu a wannan jarrabawa idan da za su kwatanta da kokarin yawancin mutane.

Kamar yadda kai ma za ka yi tsammani, yawancin mutane suna ganin kwarewarsu ta iya gane labarin da ya fi ban dariya ta wuce ta yawancin mutane.

Sakamakon wannan jarrabawa ya kasnce mai ban sha'awa idan aka duba yadda wadanda aka yi wa jarrabawar suka yi.

Wadanda suka dan dara yawancin mutane a kwarewarsu ta gane labarin da ya fi ban dariya, sun yi daidai a kan yadda suka dauki kansu.

Wadanda suka fi kokari a jarrabawar su ne wadanda suke daukar kansu sun dan wuce yawancin mutane da 'yar kwarewa ne kadan a wannan ilimi(wato ba su dauki kansu cewa sun fi kowa sani ba).

Su kuwa daliban da ba su tabuka wani abin a-zo-a-gani-ba a jarrabawar su ne wadanda suke ganin sun san abin fiye da kowa ko kuma fiye da yawancin mutane. (wato ba su san matsayin kwarewarsu ba).

Masanan biyu sun kuma gudanar da irin wannan jarrabawa, amma a wannan karon sun yi ta ne a fannin tunani da dabara da kuma nahawu(grammar).

Wadannan fannoni na ilimi suna da amsa ta zahiri, ma'ana kamar lissafi suke idan ka yi daidai an sani idan ba ka yi ba an sani, ba ja-in-ja.

A wannan jarrabawar ma sakamakon da aka samu shi ne, wadanda ba su yi kokari ba su ne wadanda suke ganin sun sani fiye da yawancin mutane.

A wani nazari da jarrabawar da aka sake yi a gaba, harwayau, wadanda suka fi kowa rashin kokarin nan a jarrabawar har yanzu ba su gane su ne na baya ba, kuma duk da cewa an bayyana musu sakamakon abokan jarrabawarsu.

Fassarar da Kruger da Dunning suka yi wa wadannan nazarce-nazarce da suka yi ita ce, iya yawan daukar da mutum yake yi wa kansa ta iya wani abu ta dogara ne da daidai yadda ainahin kwarewarsa take ta iya aikata abin.

Saboda haka wadanda suka fi kowa rashin kokari suna asara biyu ne.

Ma'ana, bayan ba su da cancanta, haka kuma ba su da tunanin da za su iya sanin rashin cancantarsu.

A wata jarrabawar muhimmiya kuma ta karshe da Kruger da Dunning suka tsara, sun horad da wadanda ba sa kokarin nan a fannin dabara da tunani.

Jarrabawar ta sa sun dan samu cigaba a kan yadda suke iya tantance matsayinsu, wanda hakan ya nuna cewa matsayin kokarin mutum yana da tasiri kan yadda shi mutum yake daukar kansa.

Wani karin binciken da aka yi ya nuna cewa, wannan matsala ta ''ban iya ba kuma ban san ban iya ba'' ''ko ban sani ba kuma ban san ban sani ba'' tana faruwa a rayuwar mutane ta yau da kullum, ba wai a gwaji ba kawai.

Misali, maharban suke baya wajen ilimi a kan makaminsu ko bindigarsu su suka fi rashin sanin daidai a kan makamin nasu.

Haka kuma likitocin da suka fi sauran likitoci rashin sanin tsarin tambayar maras lafiya, su suke ba ya a wurin fahimtar rashin kwarewarsu.

Tasirin da wannan matsala (Dunner-Krugger effect) shi ne abin da masana tunanin dan-adam ke kira (metacognition), ''tunanin tunani (thinking about thinking).

Haka kuma abu ne da ya kamata mu tsaya mu natsu mu yi tunani a kai.

Watakila tasirinsa ne zai bayyana maka dalilin ya sa wasu daga cikin abokanka da abokan aikinka suke jijji da kai suna daukar kansu sun fi kowa sani.

To kai ma dan dakata tukuna kafin ka fara daukar kanka cewa ka san wani abu ko kafi wani sanin wani abun, tuna da wani abu daya kacal.

Kamar yadda ba lalle ka dauka hakan ba, kai kanka za ka iya kasancewa kana ta tunkaho a cikin mutane ba tare da sanin rashin saninka ko jahilcinka ba.

Akwai mutane kashi uku; Wanda bai sani ba amma ya san bai sani ba (wannan aka ce makaho ne ka yi masa jagora).

Sai wanda ya sani amma bai san ya sani ba ( wannan aka ce barci yake sai ka tashe shi).

Sai kuma na karshe wanda wannan nazari yayi magana a kansa sosai, shi ne mutumin da bai sani ba kuma bai san bai sani ba (wannan aka ce wawa ne ka rabu da shi).

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The more inept you are the smarter you think you are