Yadda salon tafiyarka zai jefa ka hadari

Hakkin mallakar hoto Stig Nygaard Flickr
Image caption Hadarin ya fi yawa idan kana tafiya kai kadai a lungu musamman da daddare

Salon da wasu mutane suke yi idan suna tafiya a kasa zai iya jefa su cikin hadarin wani bakon mutum ya kai musu farmaki.

Ko da yake mutum zai iya rage hadarin hakan idan ya sauya yanayin tafiyarsa.

Tom Stafford ya yi nazari a kai:

Yanayin tafiyarka na nuna wa wasu yadda kake, ko kuma a ce salon tafiyarka na iya bayar da kai, kamar yadda 'yan magana ke cewa wai ''naka shi ke bayar da kai'' in ji gafiya da aka kama ta a jela.

Amma fa muna wannan magana ne idan a ce wani mai mugun nufi na lura da kai.

Ko da yake idan ka san rauninka a wurin tafiyar har kuma ka sauya hakan zai iya sa hadarin wani ya far maka ya ragu.

Wasu mutanen sukan fada hannun miyagu a kai a kai saboda irin yanayinsu wajen tafiya wanda ke nuna rauninsu a fili.

A shekarun 1980 wasu masana tunanin dan-adam biyu daga New York, Betty Grayson da Morris Stein sun shirya yadda za su gano abubuwan da miyagu ke lura da su a yanayin mutane kafin su kai musu hari.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane na tafiya a kan titi a New York lokacin zubar dusar kankara

Masanan sun dauki hotunan bidiyo na mutane suna tafiya a titunan New York, sannan suka kai su wani babban gidan yari na East Coast.

Sun nuna wa wasu miyagun masu aikata laifuka, su 53, wadanda an yanke musu hukunci a kan laifuka kan baki da suka kama daga kai farmaki da kisan kai, aka tambaye su yadda suke ganin saukin kai hari kan kowane mutum na cikin bidiyon nan.

'yan fursunan nan sun bayar da bayani daban-daban kan mutanen ta yadda za su iya far musu.

Akwai mutanen da a cikin bidiyon yawancin fursunonin suke ganin za su fi saukin a kai musu farmaki.

Hakkin mallakar hoto AP

Kamar yadda watakila za a yi tsammani yanayin ya bambanta, inda mata suka fi zama cikin wannan hadari a kan maza.

Su ma tsofaffi yawanci sun fi kasancewa a cikin hadarin fiye da matasa.

To amma hatta a tsakanin matasa wadanda ake ganin suna da dan dama-dama wajen iya kauce wa hadarin farmakin, akwai wadanda sama da rabin fursunonin suke ganin za a fi iya kai musu hari. Kusan sun raba su gida-gida har kashi goma.

Daga nan ne kuma sai masanan suka bukaci kwararrun 'yan rawa su yi nazari a kan hotunan bidiyon su fayyace yanayin kowane mutum na ciki bisa wani tsari da ake kira Labana, wanda 'yan rawa da 'yan fim da sauransu suke amfani shi wajen fassara motsin jikin mutum dalla-dalla.

Sun bayyana yanayin tafiyar wadanda ake ganin sun fi zama cikin hadarin farmaki da cewa babu tsari a salon nasu fiye da wadanda ba sa cikin hadarin.

Ko da yake manyan masanan sun dauki tafiya a matsayin mafi muhimmanci sosai cikin abubuwan da miyagu ke amfani da su wajen nazarin yanayin mutum, binciken nasu yana da rauni ta cewa hotunan bidiyon suna dauke da wasu muhimman bayanan daban.

Misali tufafin da mutane ke sanye da su ko yadda suke karkatar wa ko tsayar da kansu.

Bayan shekara 20 ayarin wasu masanan karkashin jagorancin Lucy Johnson ta Jami'ar Canterbury da ke New Zealand ya gudanar da wani binciken da ya fi wancan.

Masu binciken sun yi amfani da wani tsari ne inda aka dauki hoton bidiyon mutum yana tafiya sanye da bakaken kaya da ba a ganin komai a jikinsa sai gabobin jikinsa inda aka sanya wani haske ko launi mai daukar ido da ake iya gani daga nesa.

Idan aka kunna hoton bidiyon za ka ga tafiyar gabobin mutum amma ta wannan launi mai daukar ido kawai, ba tare da ganin sauran sassan jiki ko ma yatsu ba.

Bincike ta wannan tsarin ya nuna cewa za mu iya nazarin yanayin mutum daga motsin gabobinsa, musan hatta namiji ne ko mace.

Wannan ya tabbatar da cewa idan ka hangi mutum daga nesa ko da ba ka ga fuskarsa ba za ka iya gane shi idan ka san shi.

Ta wannan tsarin binciken masanan sun nuna cewa ko da an kawar da duk wasu sauran bayanai, duk da haka za a iya gane yanayin wasu mutanen idan za a iya kai musu farmaki fiye da wasu.

Wanda hakan na nufin an gane yanayinsu daga yadda suke tafiya ke nan.

To amma fanni mafi ban sha'awa na tsarin binciken Farfesa Lucy Johnston sai a nan ya zo, inda ta yi tambaya cewa, ko za mu iya sauya yadda muke tafiya domin rage yawan rauninmu da ake gani daga salon tafiya?

A dauki hoton bidiyon wasu mutane da suka amince a yi gwaji da su, kafin a basu horo kan yadda mutum zai kare kansa daga farmaki, aka kuma dauke wani bidiyon nasu bayan sun samu horon.

An yi amfani da tsarin nan na bakaken kaya da ba a ganin jikin mutum sai dai gabobinsa kawai, wajen nazari a kan mutanen bayan horon.

Sakamakon da wadanda suka yi nazari a kansu (ba fursunonin nan ba), suka bayar ya nuna cewa horon kare kan nasu daga farmaki da aka yi musu bai sauya yanayin tafiyarsu ba.

A gwaji na biyu kuwa an ba wa wasu mutanen horo ne a kan yadda ya kamata su yi tafiya inda aka fi ba da fifiko a fannonin da masu bincike suka san ya shafi yadda rauninsu yake wajen fuskantar farmaki.

Wato abubuwan da suka shafi daidaita tsarin tafiyarsu da kuma irin karfin da jikinka ke nunawa yayin da kake tafiya.

Wannan ya sa aka samu raguwa sosai a raunin da a da suke nunawa a yanayin tafiyarsu, wato kenan a yanzu ba lalle ba ne a iya kai musu farmaki kamara baya.

Kuma har bayan wata daya da aka sake bincikensu an ga haka suke.

Akwai masu ganin cewa kwakwalwa tana tsarawa tare da tafiyar da motsi ko tafiya ne kawai.

Saboda haka ina ganin ka da mu yi mamaki idan aka ce yanayin tafiyarmu zai iya nuna yadda muke (wato zai iya bayar da mu ko tona asirinmu na iya kare kanmu)

Haka kuma ba abin mamaki ba ne a ce wasu mutane za su iya nazarin tafiyarmu.

Walau su san ko za mu iya cin gasar kade-kade da wake-wake ko kuma muna yaudara ne kawai.

Idan ka san yadda mutum yake tafiya a da, za ka iya sanin yanayinsa da jin abin da yake cewa ko ma ka san kanshinsa.

Tafiya da motsin mutum su ne alamu na farko na tunanin mutane saboda haka sai mun kware tare da nazarinsu da sauri.

Wannan nazari na bincike ta amfani da duhu ko bakaken kaya da mutum zai sa, ba a ganinsa sai wasu gabobinsa kawai da ke nuna alamun tafiyarsa daga nesa, babban misali ne na yadda aka yi amfani da sakamakon bincike daki-daki har aka kai ka gano yadda mutumin da yake cikin hadarin fadawa hannun wani mugu a titi zai iya rage wannan rauni nasa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How the way we walk can increase risk of being mugged