Amfanin ciwo a gareka

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Nazarce-nazarcen da aka yi kan tunanin dan-adam sun nuna cewa tsawon lokacin wahala ko ciwo da mutum ya gamu da shi, ba shi ne ke tabbatar da shi ciwo a wurin mutum ba, sai dai yadda ciwon ya zo karshe.

Kuma wannan zai iya koya mana darasi mai muhimmanci a game da komai da yake tattare da wahala ko ciwo kama daga tiyatar asibiti zuwa hutun shakatawa, in ji Tom Stafford.

A wane lokaci ne za a ce maganin da ya fi dacewa da ciwo shi ne wani ciwon?

Lokacin da kake cikin aikin gwajin da mutumin da ya samu lambar yabo ta bajinta ta Nobel, kuma daya daga cikin kwararrun masana ilimin tunanin dan-adam ya wallafa, wannan shi ne lokacin.

Wannan masani shi ne Daniel Kahneman, wanda ya yi aikin gwajin da ya kira da suna,'' Lokacin da aka fi son karin ciwo maimakon ragi : A Kara da ciwo mai sauki a karshe'' (When More Pain Is Preferred to Less: Adding a Better End).

A gwajin da Kahneman da abokan aikinsa suka yi, sun duba irin ciwo ko rashin jin dadin da wadanda suka gudanar da binciken a kansu suka ji ne.

Sun sa mutanen su sanya hannayensu biyu a ruwan sanyi sau biyu (kowane hannu sau daya).

A gwaji daya sun sanya hannun ne a ruwan da ke da sanyin maki 14 a ma'aunin Selshiyus (14C) har tsawon dakika 60.

A daya gwajin sanyin ruwan shi ma maki 14 ne a ma'aunin Selshiyus (14C) kuma sun sa hannun har tsawon dakika 60, amma kuma a hankali aka kara makin sanyin ruwan (aka rage sanyinsa ke nan) ya kai maki 15 na ma'aunin na Selshiyas (15C) amma tare da kara zaman hannun a ruwan na dakika 30.

A dukkanin gwajin biyu zafi ko rashin dadin da mutanen suka ji daidai ne a cikin dakika 60 ta farko, kamar yadda ma'auni ya nuna wanda aka ajiye musu su yi alama idan suka ji tsananin ya karu.

Kamar yadda ma'aunin ya nuna yawanci dukkanin mutanen sun fara jin tsananin ne daga farko-farko inda ya rika ci gaba a hankali.

To lokacin da suka ji ruwan ya dan rage sanyi na wannan karin dakika 30 din sai tsananin da suke ji ya tsaya a wannan matsayi ko ma ya fara raguwa.

Daga nan sai masu gwajin wato masanan suka tambayi wadanda aka yi gwajin da su, idan da za a sake yi musu wannan gwaji, wanne za su so a maimaita.

Kusan kashi 70 cikin dari na mutanen sun zabi a maimaita na dakika 90 din ne.

Duk da cewa wannan yana da karin dakika 30 na wannan takura ko rashin jin dadi (ciwo) na sanyi.

Mutanen sun kuma ce gwajin wanda ya fi dadewa bai kai dayan wahala ko tsananin sanyi ba, kuma ya fi saukin jurewa idan aka kwatanta su. Wasu ma cewa suka yi ai bai kai dayan dadewa ba ma.

Idan kana ganin wannan wani sakamako ne kawai na gwajin dakin binciken kimiyya ba abu ne da zai kasance a yanayi na gaskiya ba, to saurara.

Kahneman ya ga irin wannan sakamakon a tambayoyin da ya yi wa wasu marassa lafiya da aka yi wa binciken hanjinsu(Colonoscopy examination), wanda bincike ne da duniya ta yarda cewa mutane ba sa jin dadi a lokacin da ake yi musu shi.

A binciken, ana daukar hoton cikin hanjin maras lafiya ne ta hanyar zura masa wata na'ura mai kamar girman dan yatsa a takashinsa.

Marassa lafiyar da Kahneman ya yi wa tambayoyin, an yi musu wannan bincike ne na sa na'ura a takashinsu daga minti hudu zuwa minti 69, to amma tsawon lokacin da aka yi musu binciken na asibitin bai nuna hasashen yadda suka ji ba bayan an gama musu.

A maimakon haka karfi ko tsananin dadi ko annashuwa ko rashin jin dadin abin a lokacin da ya fi yawa ko ya kai kokoluwa da kuma matsayi ko yawan wannan rashin jin dadi da suka ji a kusan karshen gwajin su ne suka bayyana yadda suka ji.

Wannan ya kara tabbatar da abin da Kahneman ya ayyana cewa yadda muke daukar wani abu na jin dadi ko maras dadi ko damuwa ko ciwo ya dogara ne da yadda muka ji shi a lokacin yana tsananin rashin jin dadin da kuma yadda muka ji a karshensa(Peak-End rule).

Amma ba wai ainahinn tsawon lokacin da dadin ko rashin jin dadin ko wahalar ko kuma ciwon ya dauke mu ba.

Wannan sakamako ne ma ya sa Kahneman yake ganin me zai hana likitoci su kara tsawon lokacin tiyata mai zafi domin marassa lafiya su rika tuna dadin aikin, duk da cewa hakan na nufin kara musu zafin tiyatar ne.

Wasu kuma na tambaya ne ko wannan na nufin abu mafi amfani a game da hutu (holiday) shi ne cewa ya hada da lokuta masu dadi, amma ba wai dadewar lokacin hutun ba.

To amma ina ganin abu mafi muhimmanci da za ka koya a wannan bincike wani abu ne daban.

Maimakon a ce tsawon lokacin da dadi ko ciwo ya dauka ba shi ne yake da muhimmanci ba sai dai yadda karshensa ya kasance, ni a wurina abin da yake shi ne, yana nuna mana muhimmancin yadda za mu kula da yadda muke sarrafa lokacinmu ne.

Idan har hutun karshen mako da ya zo maka da wani abu na alheri ko mai dadi da ya sa ka manta da komai zai kasance maka kamar hutun mako biyu gaba daya,

ina ganin ke nan sirrin rayuwa mai dadi da farin ciki zai iya kasancewa a ce ka tsara lokacinka ta yadda za ka rarraba shi gida-gida da za ka more masa.

(A ce kowane gida na lokaci ka yi wani abu mai muhimmanci da dadi), maimakon a ce ka dauki lokacin gaba daya kana abubuwa daya bayan daya a hade ba tare da ka tsaya ka huta ba har ka kai ga jin wani dadi guda daya a karshe kawai, bayan duk wahalar da ka sha a baya mai tsawo.

Abin da nake bukata na yi yanzu kawai shi ne na dauki hutu na jarraba wannan nazari nawa.

Ko ka yarda da wannan magana ta Tom?

Idan kana son karanta wannan a harshen ingilishi latsa nan Why feeling more pain may be better for you