Me ya sa muke camfi a wasanni?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kolo Toure da Yaya Toure da Drogba

Yadda nazari a fannin tunanin dan-adam a kan tattabaru masu jin yunwa ya bayyana camfe-camfe da wasu ibadu da mutane ke yi.

Ga bayanin da Tom Stafford ya yi mana:

Kafin fara duk wani wasa tsohon fitaccen dan kwallon kafa na Holland Johan Cruyff sai ya dan bubbuga cikin mai tsaron ragarsu (gola).

Gwanar wasan kwallon tennis ta daya a duniya, Serena Williams a duk farkon wasanta sai ta tambara kwallon sau biyar a kasa.

Jennifer Aniston kamar yadda rahotanni suka ce, duk jirgin saman da za ta yi tafiya a cikinsa, sai ta taka wajensa da kafarta ta dama kafin ta shiga.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tiger Woods

Kama daga taba katako domin samun sa'a zuwa tafiya a kusa da tsani domin kauce wa bacin rana, dukkanninmu muna da wasu abubuwa ko 'yan camfe-camfe da muke yi, wadanda idan ka tsaya ka natsu ka duba sai ka ga ba su da wata ma'ana.

Kuma ba ko da yaushe ba ne muke yin su domin samun sa'a.

Na tsaya sai da butata ta tafasa kafin na zuwa ruwan da zan yi shayi, maimakon na fara zuba ruwan kafin tafasa.

Ni ban san dalilin da ya sa nake son yin hakan ba, na dai tabbata hakan ba zai sa shayin ya zama daban ba.

To tun da haka ne, me ya sa, ni da sauran mutane muke son maimaita wani abu ko wata dabi'a tamu ta daban?

A tattare da wadannan dabi'u da suke kamar marassa ma'ana ko na rashin hankali, wato dabi'ar tafasa buta, tambara kwallo a kasa ko bubbuga ciki akwai wani abu da yake nuna mana abin da ya sa dabbobi suka yi nasara a fafutukarsu ta sauya kamanni.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Serena Williams

Muna kiran wabi abu da muke yi ba tare da tunanin me ya sa muke yin shi ba dabi'a.

Wannan takamaimai shi ya sa dabi'u suke da amfani, wato abubuwa ne da ba sa bukatar bata kwakwalwa ko yin tunani.

Kwakwalwarmu tana da tsari na samun ilimin yin wasu sabbin ayyuka na kullum (dabi'a), kuma wani abu da ya sa mu da wasu halittu muka yi nasara shi ne damar kirkirar wadannan dabi'u.

Hatta tattabaru ma za su iya samun dabi'u na camfi, kamar yadda masanin tunanin dan-adam B.F. Skinner ya nuna a wani gwaji ko abu da ya tsara.

Da farko Farfesa Skinner zai kawo tattabara ne a cikin keji ya ajiye kafin ya fara lacca a aji.

A kejin akwai wani abu da kwayar hatsi ke fadowa daga cikinsa duk bayan dakika 15

Da farkon laccar Skinner zai sa mutanen da ke wurin su lura da yadda tattabarar ta ke a kejin, ma'ana 'yan tsalle-tsalle da kaikawon da take yi, kafin ya lullube kejin ko ya rufe shi gaba daya.

Bayan minti 50 sai ya fito da kejin ko ya yaye wannan malullubin da ya rufe kejin da shi.

Daga nan sai ka ga kowace tattabara tana wani abu ko dabi'a ta daban.

A wani kejin za ka ga tattabarar tana jujjuyawa daga dama zuwa hagu (sabanin yadda hannun agogo ke juyawa daga hagu zuwa dama), sau uku kafin ta leka dan kwandon da kwayar hatsin nan ke fadawa ciki.

A wani kejin kuma za ka ga tattabarar tana mika kanta sama can kuryar hannun hagu.

A takaice kowacce daga cikin tattabarun ta samu wata dabi'a ko al'ada da za ta yi ta yi kusan a ko da yaushe.

Bayanin Skinner a kan wannan sabuwar dabi'a a fayyace yake kamar yadda dabi'ar ta ke ta daban.

Ko da yake mun san cewa kwayar abincin nan za ta fado ko da tattabarar ba ta yi wannan abin da take yi ba, amma ita tattabarar ba ta san da haka ba.

To a nan ka dauka kai ne tattabarar nan; kwakwalwarka (ta) abubuwa kadan ta sani game da duniyar mutane (kejin nan), ko kuma wannan abu da yake sakin kwayar hatsi ko abinci dun dakika 15.

Kana kai kawo a cikin kejin nan, sai ka ce bari ka yi wani dan juyi haka sau uku daga dama zuwa hagu, kana cikin haka sai kawai ka ga kwayar hatsi (abinci).

To idan kana son haka ta kara faruwa, wato ka sake ganin wata kwayar hatsin, me za ka yi?

Amsar ita ce za ka maimaita abin da ka yi yanzun nan ne. Kuma kana cikin sake yin abin sai abin mamaki ga kwayar hatsi ta sake bayyana.

To daga nan ne fa Skinner yake ganin camfi ya samo asali.

Camfi kuma ya karbe iko daga dabi'a saboda kwakwalwarmu tana kokarin maimaita duk wani abu da ya gabaci nasara, ko da kuwa ba ma ganin yadda abin ya ke tasiri a lamari.

Wato duk abin da ya kasance muna yi kafin wata nasara ta same mu, sai mu dauka yin wannan abin shi ne sanadin nasarar tamu.

Mun kasance cikin yanayi na zabar abu biyu, tsakanin ko mu yi nazari a kan gano yadda duniya ke aiki kuma mu yi lissafin abu mafi kyau da za a samu daga gareta(wanda shi ne abu na hankali da ya dace a yi), ko kuma maimaita duk abin da muka yi kafin wata nasara ko alheri ya same mu.

Ba shakka za mu fi zabar abu na biyu ne, wato shi ne, mu maimaita abin da muke yi kafin wani alheri ya same mu.

Kirkirar dabi'a

Shi kuwa Tony Dickinson, masanin tunanin dan-adam na Jami'ar Cambridge ya kara zurfafawa a kan binciken na dabi'a.

Farfesan ya horar da beraye ne kan yadda za su rika danna wata sanda domin samun abinci, kuma su yi wani abin daban(kamar jan sharka) idan ruwa suke so.

Berayen daga nan za su iya yanke shawarar abin da suka fi so(ruwa ko abinci).

Kafin gwajin idan ka ba su ruwa, sai su danna sandar da za ta sako musu abinci, idan kuma ka basu abinci da farko sai su ja sarka domin samun ruwa.

To amma wani abu na daban mai mamaki na faruwa idan berayen suka cigaba da yin wannan abu da aka horad da su a kai har ya wuce lokacin da suka kware.

Abin mamakin shi ne sai su manta yadda kowane abu daban da za su yi domin samun abin da suke bukata (ruwa ko abinci).

Bayan wannan horon da aka yi musu har ya wuce yadda ya kamata, idan ka ba beran abinci, kafin gwajin sai su ci gaba da danna sandar nan domin abinci ya fado, duk da cewa fa yanzun nan aka ba su abinci.

Beran ya kirkiro wata dabi'a, abin da yake yi saboda kawai akwai damar yin hakan, ba tare da tunanin abin da hakan zai samar ba.

A wurin masanin tunanin dan-adam, da yawa daga cikin al'adun mutane sun yi kama da dabi'un da tattabarun Skinner suka koya ko kuma berayen Dickinson.

Al'adu da dama da ba su da wani tasiri a kan duniya, sun zama jiki a rayuwarmu ta yau da kullum.

Idan lada ko kyautar da mutum zai samu tana da girma kamar a gasar wasanni, kwakwalwarmu na samun karin matsin lamba domin ta lakanci kowace dabi'a da za ta iya haifar da nasara.

Wasu al'adun za su iya taimaka wa dan-wasa ya saki jikinsa ba tare da wata fargaba ba, kafin da kuma bayan wasan, a matsayin wata al'ada da ta zama jiki a wurinsa wadda kuma ya yi amanna da tasirinta.

Tsohon zakaran kwallon golf na duniya, Tiger Woods, ko da yaushe yana sa jar hula a ranar karshe ta wata gasa, saboda ya ce launi ne na karfinsa.

A wasan baseball kuwa, Wade Boggs, cewa ya yi, ya fi dukan kwallon da karfi idan ya ci naman kaza da daddare kafin safiyar da zai yi wasa.

An taba fara wasa, bayan hutun rabin lokaci ba tare da dan wasan kwallon kafar nan Kolo Toure ba, saboda ya ki ya fito daga wurin hutunsu.

A bisa camfinsa, shi ne dan wasa na karshe da zai fito daga dakinsu na sauya kaya (dressing room).

To amma a wannan rana ya tsaya ne har sai an gama yi wa wani dan wasan magani.

Muna kafewa a kan wadannan dabi'u da al'adu ne saboda mu ko kuma bangaren kwakwalwarmu na dabbobin da, ba ya son yin kasadar sanin abin da zai iya faruwa idan muka sauya dabi'ar.

Al'adun sun dore tare da bunkasa da cigaba duk da alamun rashin ma'anarsu saboda sun kafu a sassan kwakwalwarmu da bisa tsarin halitta ba sa tunanin dalilin yin abu.

Abin da suke yi kawai shi ne su maimaita abin da ya yi kyau a baya.

Wannan ya bayyana dalilin da idan mutum yana da wani camfi nasa hakan ya kara tabbatar da kasancewarsa mutum.

Yana daga cikin abin da muka gada a matsayinmu na dabbobi masu basira, rikon wata dabara ko camfi ko al'ada da ta yi tasiri ko da kuwa ba ta da wata ma'ana ga aikin mutum.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Sporting superstitions: Why do we have them?