Kudi ba zai iya sai ma ka farin ciki ba

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kana jin idan ka samu nasarar mallakar wasu makudan kudade wadanda ko a mafarki ba ka taba tunanin samunsu ba hakan zai sa ka zama cikin farin ciki har abada?

Tam Stafford ya bayyana mana dalilin hakan:

Da yawanmu za mu dauka haka lamarin yake cikinmu har da wani mai tsaron kanti a Amurka wanda ya ci dala miliyan 338 a cacar lotiri (lottery), wanda wannan shi ne kudi mafi yawa na hudu da aka taba ci a tarihin cacar.

Dukkanin shaidun da aka tattara sun nuna cewa samun garabasar wasu makudan kudade ba zai kawo wani sauyi a rayuwar mutum ba.

Duk da yadda mutum yake kallon dadin da ke tattare da barin aiki kuma ya kasance yana iya sayen duk abin da ya ga dama, cin wannan caca ko samun makudan kudade na fitar hankali ba tabbaci ba ne na samun cikakken farin ciki.

Wani bincike ya gano cewa mutanen da suka ci wannan caca ta makudan kudade ba su kai wadanda suka shige ta ba amma kuma ba su ci komai ba farin ciki.

Abin da ake gani shi ne idan dai har kana da kudin biyan muhimman bukatunka na rayuwa, mallakar makudan kudade babu wani farin ciki da zai sa ka fiye da mallakar 'yan kadan.

Wani ma'auni na wannan matsayi shi ne, za ka ga shi wanda ya ci wannan caca ko ya samu makudan kudaden, nan da nan za ka ga ya sauya yanayin rayuwarsa ta yadda za ta dace da matsayin dukiyarsa.

Wani bayanin kuma shi ne, shi farin cikinmu ya danganta ne da yadda muke kallon matsayinmu da kuma na abokanmu.

Misali, wane da muka gama makaranta daya da shi aikina ko dukiyata ta fi ta shi ko matsayina ya fi na shi.

To idan ka samu makudan kudade ko ka ci wannan caca ta kudade masu yawa, za ka ga yanzu ka fi makwabtanka matsayi.

Saboda haka komawa wani makeken gida a wata unguwa ta manyan mutane zai sa ka ji dadi da farin ciki.

To amma da zarar da leko ta tagar sabon gidan naka sai ka ga sabbin makwabtanka na wannan unguwa, ai su kuma gidajensu sun fi naka.

Dukkanin wadannan abubuwa ba shakka suna taka rawa, to amma babban abin mamakin shi ne, me ya sa ba ma iya sanin abin da zai ba mu cikakken farin ciki na gaskiya.

Za ka dauka cewa za mu iya hasashen wannan matsala ba tare da wata tantama ba.

Wadanda suka ci makudan kudade a caca ko kuma suka samu kudaden ta wata hanyarsu ta kasuwanci ko ma dai ta yaya ne za ka ga sun sauya yanayin rayuwarsu kama daga irin tufafi da abin hawa da muhalli da suke da shi hatta abokai ma sai su sauya tare kuma da ganin cewa sun wuce matsayin makwabta da abokan harkokinsu na da.

To amma me zai hana su kashe wannan dukiya da suka samu dare daya ba zato ba tsammani ta hanyoyin da za su sai musu farin ciki?

Wani bangare na matsalar shi ne, shi farin ciki ba abu ne da za a iya auna shi a zahiri ba kamar tsawo ko nauyi ko kudin da mutum yake samu ba, wanda cikin sauki za a ce ga yawan lambarsa.

Shi farin ciki a takaice wani yanayi ne da ya kunshi abubuwa da dama da suka shafi dan jin dadi mai gushewa da kuma wani sauyi da ake gani na harkokin mutum idan aka kwatanta da dimbin shekarun baya.

Saboda haka ba abin mamaki ba ne idan a wani lokaci mun kasa gano hanyar da za ta kai mu ga farin ciki mai yawa.

Tunaninmu maras inganci na nufin zabin da muke yi na abubuwanmu na yau da kullum ba ya dacewa da ainahin abin da muke bukata na tsawon lokaci.

A takaice abubuwan da muke zaba na biyan bukatarmu ne ta dan gajeren lokaci kawai, saboda ba ma tsayawa mu yi tunanin abin da ya dace da mu.

To shi farin ciki kamar yadda muke maganar kwatanta shi a zahiri, za mu ga cewa idan ma ka yi kokarin auna shi, sai hakan ya karkatar da mu daga sanin abin da zai iya sa mu farin ciki.

Wani nazari mai muhimmanci da Christopher Hsee na makarantar harkokin kasuwanci ta Chicago da abokan aikinsa suka yi, ya nuna yadda hakan za ta iya faruwa.

Hsee ya yi gwaji ko nazarin nasa ne a kan zabin dan wani abu mai sauki:

Ya bukaci mutane ne kan su zaba tsakanin aikin minti shida da za a ba su ladan galan daya na askirim na Vanilla (Vanilla Ice Cream) da aikin minti bakwai wanda shi kuma za a ba da wani nau'in askirim na daban (pistachiao)wanda ya fi na vanilla.

A ka'ida kasa da kashi 30 cikin dari na mutanen sun zabi aikin minti bakwai saboda sun fi son daya nau'in askirim din a kan vanilla.

A wurin malamai masu nazarin farin ciki wannan ba abu ne mai wahalar fassara ba, domin wadanda suka zabi wannan nau'i na askirim ba vanilla ba akwai yawan abin da ya karfafa musu gwiwar zabin aiki mafi tsawo.

An yi wani kwatanci na gwajin, wanda shi kuma aka bukaci wasu mutanen su zaba tsakanin irin wadannan askirim biyu amma kuma a wannan karon akwai bambancin yawan makin da za su samu.

A nan zabin shi ne tsakanin aikin minti shida a samu maki 60 ko kuma aikin minti bakwai a samu maki 100.

Sai dai a nan an sa ka'idar cewa idan mutum ya samu maki 50 zuwa 99 za a ba shi askirim na vanilla wanda bai kai wancan dayan daraja ba ke nan.

Amma kuma wadanda suka samu maki 100 za a ba su daya askirim din ne mafi daraja.

A nan za a ga duk da cewa wancan aikin na farko da kuma wannan na biyu kusan daya suke, to amma sanya tsarin la'akari da yawan makin da mutum ya samu ya sa an samu bambanci a zabin aikin da mutum zai yi.

Hakan ya sa mutanen da suka fi yawa suka zabi su yi aikin minti bakwai a kan na minti shidan domin su samu maki 100, saboda idan suka zabi aikin minti shida duk kokarinsu ba za su samu askirim din da ya fi daraja ba, domin matuka maki 99 za su samu.

A kan wannan gwaji ko jarrabawa da wadansu da aka yi, Hsee ya ayyana cewa mutane na kokarin samun maki mafi yawa domin su samu jin dadi da farin ciki mafi yawa.

Makin da aka yi amfani da shi a nan abu ne da zai ba mu damar auna ko kirkirar jin dadi.

Kuma saboda makin abu ne da ke da saukin aunawa da kwatantawa, lamba 100 aba ce da ta fi 60, wannan ya shiga hankalinmu fiye da irin askirim din da muka fi jin dadi.

Saboda haka nan gaba ga wanda yake cacar lotiri (lottery), idan za ka yanki tikitinta saboda yawan kudin da za a ci ko zabar aiki ta hanyar yawan albashinsu, zai fi maka kyau ka kuma yi tunanin yawan farin cikin da za ka samu daga abin da za ka ci a cacar ko aikin zai ba ka maimakon kawai ka duba yawan kudin da za ka samu.

Kudi ba ya sai maka farin ciki kuma wani dalili da ya sa hakan shi ne, watakila saboda shi kansa kudin yana kautar da hankalinmu daga ainahin abin da muke jin dadi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why money can't buy you happiness