Shan miyagun kwayoyi: Gaskiyar lamari

An gaya mana cewa bincike ya tabbatar miyagun kwayoyi kamar hodar iblis ta koken da hiroin suna kama mai amfani da su kai tsaye.

To sai dai abin ba haka yake da sauki ba, domin wasu gwaje-gwaje masu sauki da aka yi a cikin shekara talatin da ta gabata sun bayar da bayanai na daban.

Tom Stafford ya duba mana yadda lamarin yake:

Miyagun kwayoyi na da ban tsoro. Kalmar hiroin da koken kadai na sa mutane su ji tsigar jikinsu ta tashi.

Ba wai alaka da manyan laifuka da illa ga lafiya ba kadai ne abubuwan da ke sa a kyamaci wadannan abubuwa hatta yadda suke zubar da kima da mutuncin mai amfani da su abin dubawa ne.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

An gaya mana cewa idan mutum ya kuskura ya jarraba daya to shikenan ya kamu.

Wannan ga alama gaskiya ne kamar yadda wani gwaji da aka yi a kan dabbobi ya tabbatar.

Nazarce-nazarce da aka yi da yawa sun nuna cewa beraye da birai suna fifita mofin ( hodar heroin da ake yi a dakin gwaji na kimiyya) a kan abinci.

Idan aka shirya yanayin gwaji da ya dace za a ga yadda wasu berayen ma sukan yi amfani da miyagun kwayoyi da kansu har ta kai su ga mutuwa.

Da farko idan ka duba sai ka ga kamar kawai abu ne na cewa dabbobin dakin kimiyya ne suka bugu da miyagun kwayoyin da suke bukata.

Hakkin mallakar hoto b

Abu ne mai sauki ta wannan hanya ta kimiyya mai ban mamaki ka ga yadda karfin wadannan miyagun kwayoyi ke raba mu da hankalinmu su tafiyar da harkokinmu bisa tasirinsu.

To amma akwai karin bayanin wasu abubuwan game da wannan labari na kimiyya na gaske, ko da kuwa ba a yi maganarsa ba sosai.

Sakamakon wasu nazarce-nazarce 'yan kanana da aka yi shekara 30 da ta wuce ya bayyana wani abin ne daban kuma.

Ya kuma nuna yadda cikin sauki yanayin dabba zai sauya bisa tasirin yanayin muhallin da ya fi kasancewa a cikinsa.

Muhimmiyar shedar da aka rasa ita ce, jerin gwaje-gwaje da aka yi a shekarun 1970 a abin da aka kira dandalin beraye (Rat Park).

A wadannan gwaje-gwaje da aka yi a lokacin an gano abubuwa da dama da suka shafi tasirin amfani da miyagun kwayoyi.

A nazarin da ya yi wani masanin kimiyya na British Columbia ta Kanada, yana ganin beraye sun fifita shan sinadarin mofin (morphine) ne a kan ruwa a nazarin da aka yi a baya saboda yanayin wurin da aka sa su (wato gidansu).

Domin gwada wannan nazariyya ta shi, sai ya gina wani wuri mai girman murabbu'in kafa 95 domin zaman tarin beraye maza da matansu.

Wannan wurin da ya gina ba kawai girmansa ba wanda ya linka har sau 200 girman kejin da ya kamata a sa beraye a yi gwaji da su ba, wurin an tsara shi kamar wani gida na sosai da kayayyaki da sauransu.

Baya ga wannan ga kuma kayan abinci iri-iri, sannan kuma watakila mafi muhimmanci ma shi ne dukkanin berayen suna wuri daya ne.

Beraye wasu irin halittu ne masu mu'amulla da junansu sosai. Zamansu a wani dan keji tamkar wani kurkuku ne a wurinsu , wanda zai hana su aiwatar da wasu halaye nasu da suka saba.

To idan muka dawo maganar wancan gida da masanin kimiyyar ya samar da berayen (Rat Park) za mu ka wuri ne da aza a iya cewa da za su wala su yi rayuwarsu yadda suka saba.

A nazarin Alexander ya gano cewa berayen da aka sa su a keji suna shan sinadarin kwayar mofin (morphine) linki 20 fiye da wadanda aka sa su a gidan nan da ya samar.

Masanin ya gano cewa berayen da aka sa su a wancan babban gida za a iya sa su sha karin sinadarin mofin idan aka hada shi da sukari.

Sai dai a wani gwajin da aka yi an ga cewa ba wai sun kara yawan shan mofin din ba ne, saboda sukarin yana sa su manta da dacin mofin din su yi ta sha har ya bugar da su, suna kara sha ne domin suna son sukarin.

Kuma tun da an gauraya ruwan sukarin da mofin to ka ga sai su kai ga shan mofin din da zai bugar da su a dalilin neman shan sukari.

Lokacin da aka sanya sinadarin naloxone, wanda ke hana tasirin mofin a ruwan shan nasu mai hade da mofin, yawan abin da berayen suke sha bai ragu ba, sai dai ma karuwa ya yi.

Wanda hakan ke nuna cewa suna son su raba kansu da illar mofin din da suka riga suka sha, kuma ga sukarin ma da suke so a ruwan.

Sakamako bai cika ba:

Sakamakon na da matsala saboda idan mutum ya fara amfani da wata muguwar kwaya to abin ya kama shi ke nan yadda zai sake tsarin kwakwalwarsa.

Lokacin da aka sama wa berayen gwaji na Alenxander wani aiki maimakon kawai su zauna a cikin kejin da ba komai sai suka yi watsi da amfani da ruwan kwayar mofin, suka fifita wasa da junansu da kaikawo a wannan keji nasu maimakon su bugu da ruwan na mofin.

Domin kara tabbatar da shedarsa ta danganta shan muggan kwayoyin ga yanayin rayuwa da aka samu kai, wasu ayarin na Alexander sun gudanar da wani binciken inda aka tilasta wa berayen da aka rena a keji shan ruwan kwayar mofin a kwanaki 57 a jere.

Idan har akwai abin da zai sake tsarin kwakwalwar mutum( daga shan kwaya daya) to wannan zai iya.

To amma da aka fitar da wadannan beraye daga cikin keji aka mayar da su wancan babban wurin da Alexander ya samar, sai suka zabi su sha ruwa maimakon su cigaba da shan ruwan mofin a duk lokacin da aka ba su damar zaba.

Sai dai jikinsu ya dan nuna alamun sauyin ruwan da suke sha, wato na barin ruwan kwayar mofin.

Za ka iya kara nazari a kan binciken na gidan beraye (Rat Park) a rahoton binciken kimiyyar na ainahi.

Ba a dai gabatar da sakamkon binciken sosai a littattafan kimiyya, kuma an dakata da binciken bayan 'yan shekaru saboda ba wanda ya samar da kudin ci gaba da nazarin.

An yi ta sukan tsarin da aka bi wajen gudanar da binciken kuma dan kokarin da aka yi na kwaikwayonsa ko sake jarraba shi ya samar da wadansu sakamakon masu karo da juna.

Amma dai duk da haka nazarin ya nuna cewa bayani ko yardar da aka yi cewa shan miyagun kwayoyi yau da gobe na sa a kamu da dabi'ar shan kwaya magana ce da ba ta tabbata ba sosai.

Abin da zai sa ta'ammali da miyagun kwayoyi ya kama mutum, har ya zama jiki a wurinsa ya wuce abin da aka gani a kwaya daya ko wasu kwayoyi komai karfinsu kamar koken da hiroin.

Zabin da kake da shi na kwayoyin wanda yanayin mu'amullarka da kuma muhallinka ka iya yin tasiri a kai, na taka muhimmiyar rawa kari kuma da irin matukar dadin da mai amfani da kwayar yake jin cewa yana samu, duka wadannan abubuwa ne da za a yi la'akari da su.

Ga masanin tunanin dan adam kamar ni, ina ganin cewa ko a kan maganar kamuwa da dabi'ar amfani da miyagun kwayoyin za a iya amfani da nazariyya ta binciken wasu abubuwan ba sai lalle a ce sai wadda ta shafi kwayoyi ba kadai.

Haka kuma binciken na gidan beraye (Rat Park) shi ma ya nuna cewa idan aka bayar da fifiko wajen yayata tasirin miyagun kwayoyi a kan kwakwalwa ba a yi la'akari da tasirin kamuwa da kwayoyin ba a kan mu'amullar mutum da sauran abubuwan da suka shafi mutumin, to daga nan sai mu ce kimiyya ta kauce hanyar da ya kamata ta fadakar da mu ilimi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Drug addiction: The complex truth