Yadda za ka sauya tunanin mutane

Hakkin mallakar hoto Getty

Dabi'ar dan-adam ta dogara ne ga maimaita abu ko yin sa yau da kullum da yawan amfani da abu ko wani tsari da camfe-camfe wanda har ta kai an san irin yanayin mutum ya zama za a iya amfani da wannan yanayi nasa a yaudare shi ko a juya shi yadda ake so ko kuma a sauya masa tunani.

Idan kasan sirrin sanin yanayin mutum to za ka iya amfani da hakan ka juya shi yadda kake so.

Misali a kwanan nan a wani rubutu da muka gabatar mun bayyana muku yadda za a iya gane mai karya ta hanyar sa shi ya bayar da bayanai masu yawa maimakon dogaro ga yanayin fuskarsa ko jikinsa idan yana magana.

Akwai wasu sauran hanyoyin sanin halayya ko zuciyar mutum ta yadda za ka iya amfani da hakan ka juya shi ko ka sauya tunaninsa.

1. Ka dan taba mutum a kafada sannan ka kalli idonsa, hakan na nufin za ka iya ba shi shawara.

2. Bude ido sosai abu ne da ake dangantawa da rashin tabbas yayin da mutum yake wani yanayi na yanke shawara: Idan mutum ya kasance ba shi da tabbas a kan matsayin da zai dauka, za ka ga kamar hankalinsa ya tashi abin da zai sa idonsa ka ga ya bude. Domin karin bayani kana iya duba rubutun da muka yi mai suna: ''Labarin zuciya a tambayi fuska''

3. Dabarar da 'yan-sane suke yi wa mashaya ita ce, sai su rika rangaji kadan kadan suna musu magana. Daga nan sai bugaggen shi ma ya rika rangajin wai ya saka wa wannan abin da yake masa shi ma, a garin rangajin nan sai mai mayen ya fadi. Dan-sanen zai yi kokarin taimakon mai mayen wai ya tashe shi daga nan sai ya sace masa kayansa.

4. Mazan da suke da yawan kwayoyin halitta na jima'i (testosterone) za ka ga suna da fuska mai fadi da kashin kumatu manya, kuma irin wadannan mutanen sun fi zama masu saurin fushi na son nuna iko.

5. Launin ja, launi ne da ake dangantawa da son mallakewa da fusata. Misali za ka ga 'yan damben zamani na boksin da suke sanye da jajayen kaya, kashi biyar bisa dari an fi danganta su da yin nasara a kan wadanda suka sanya kaya shudi.

6. A wasan canke da ake amfani da alamar dunkulallen hannu da 'yan yatsu biyu da kuma tafin hannu wato Rock, Paper, Scissors kamar yadda ake kiransa a Ingilishi, an fi kyautata zaton maza su zabi alamar karfi wato dunkulallen hannu (rock), yayin da alamar yatsu biyu (scissors) ba abu ne da yawancin mutane maza da mata suke zabarsa ba.

Saboda haka idan kana wannan wasa na canke hanya mafi sauki a wurinka sai ka zabi tafin hannu (paper), wanda hakan zai sa akalla ko ba komai ko dai ka yi nasara ko kuma canjaras.

Wata dabarar kuma ita ce ta furta abin da ka zaba a fili, domin abokin wasan naka ko canken zai dauka yaudara kake ma'ana ba da gaske kake ba abin da ka fada ka zaba, daga nan sai ya yi wani zabin wanda ba zai kai shi ga nasara ba.

7. Masu sayar da kaya musamman a kanti sun lakanci hanyar sarrafa tunanin jama'a.

Za ka ga sun sanya wa wani kaya wanda akwai wasu irinsa a wurin farashi fiye da na sauran. Misali idan aka jera na'urorin wanki guda uku a wuri daya aka sanya farashinsu kowanne dala 200, a kusa da ukun nan kuma sai aka ajiye wani mai farashi dala 400, wannan mai farashin da yawa zai sa ka ga kimar wadancan ukun.

To gaskiyar abin da yake a nan ita ce, wannan ya nuna ba mu san ainahin kudin na'urar wanki ba.

8. Dariya aba ce da ke kara tabbatar mana da zumunci a dangantaka a tsakani, ko da abu ya kai a yi dariya a kansa ko da bai kai ba.

Idan kana dariya tare da mutane kana nuna musu cewa kana kaunarsu, ko ka yarda da su, ko kuma kana tare da su.

Bincike ya nuna cewa dariya na sa mutum ya saki jiki da kai har ma ya gaya maka sirrinsa idan a gaba.

Saboda haka idan kana son ka shawo kan mutum har ya gaya maka abin da ke zuciyarsa, wata hanya ita ce ta yin dariya ko murmushi idan ya fadi magana da nufin ya sa ka dariya ko da kuwa maganar ba ta kai a yi mata dariya ba. Kana iya nazari a kan wannan idan ka duba rubutunmu mai taken, ''Me yasa muke kyalkayala dariya haka kawai?''

9. Zakin muryar mace yana bambanta lokacin al'adarta. Zakin yana kaiwa karshensa yayin da yanayinta na daukar ciki ya karu. Wannan ya nuna yadda yanayin halittarmu yake bayyana kansa a saukake ta wasu bambance-bambance na dabi'unmu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How to read emotions and influence people