Me ya sa bakin labari ya fi jan hankali?

Hakkin mallakar hoto Getty

Me ya sa idan ka duba labaran jaridu ko talabijin ko ka saurari rediyo sai ka ji ba abin da suka fi ba wa fifiko sai mummunan labari ko na bala'i ko na rashawa ko wata gazawa?

Watakila saboda hankalinmu ya fi karkata ne wajen labarai masu tayar da hankali ne ba tare da mun lura da hakan ba in ji masanin tunanin dan-adam Tom Stafford.

Idan kana karanta labarai wani lokacin sai ka ji kamar ba wani labari a duniyar nan da ake bayarwa sai na an mutu ko an lalace da ire-irensu.

Me ya sa kafafen yada labarai suke bayar da fifiko ko mayar da hankalinsu kan labarai marassa dadi maimakon masu dadin ji?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kuma me wannan karkata ga mugun labari ke nunawa a game da mu masu sauraro?

Wadannan irin labarai ba su kadai ba ne abubuwan da ke faruwa. Watakila 'yan jarida sun fi mayar da hankali ne a kan munanan labarai kamar wani bala'i na yanzu-yanzu domin sun fi daukar hankali a kan wani cigaba na sannu-sannu.

Ko kuma watakila masu tattaro labarai suna ganin rahotanni a kan wani dan siyasa mai almundahana ko wani abu maras kyau da ya faru sun fi labarai masu sauki daukar hankali.

Amma wani dalili da zai iya sa hakan kuma shi ne mu kanmu masu sauraro ko karanta labarai mun sa 'yan jarida sun karkata wajen irin wadannan abubuwa.

Za ka ji mutane da yawa suna cewa mun fi son labari mai dadi: amma da gaske hakan suke nufi?

Domin bincika wannan lamari masana Marc Trussler da Stuart Soroka sun yi wani gwaji a Jami'ar McGill ta kasar Kanada.

Masu binciken biyu ba su gamsu da nazari da binciken da aka yi a baya ba kan yadda mutane suke daukar labari.

Suna ganin ba a kiyaye da ka'idoji ko sanya ido sosai kan yadda aka yi nazarin ba, ko wadanda aka yi binciken da su sun yi san rai ko kuma sun san ana lura da su.

Masanan sun yanke shawarar bin wata sabuwar dabarar daban wajen binciken.

Yaudara:

Tambayar dabara

Trussler da Soroka sun gayyaci wadanda za a yi nazarin da su ne daga jami'arsu suka shiga dakin bincike domin nazarin yadda idonsu yake lokacin karanta labari.

Dsa farko an bukaci mutanen su zabi labarai a kan siyasa wadanda za su karanta daga shafin intanet, domin na'urar daukan hoto ta rika dauka tare da auna yanayin motsin idonsu.

Bayan wannan matakin na farko, sai kuma aka sa musu hoton bidiyo na dan lokaci kadan( su sun dauka wannan shi ne matakin gwajin na sosai, ba su san an yi hakan ba ne kawai domin cikon lokaci), daga nan sai aka sa su amsa tambayoyi a kan irin labarin siyasar da suke son karantawa.

Sakamakon binciken da kuma labaran da mutanen suka fi karantawa masu muni ne.

Mutanen sun fi zaben labarai marassa dadi da suka shafi rashawa da koma-baya da munafurci da sauransu maimakon labarai na cigaba ko na tsaka-tsaki wadanda suke lami.

Mutanen da su ka fi sha'awar labaran al'amuran yau da kullum da siyasa sun fi karkata ga son jin labarai marassa kyau.

Kuma abin mamakin duk da wannan, idan aka tambaye su sai su ce sun fi son jin labarai masu kyau.

Yawancinsu ma sun ce kafofin yada labarai sun fi mayar da hankali ne a kan bakin labari.

Martani mai hadari

Masu binciken sun gabatar da wannan nazari a matsayin cikakkiyar shedar abin da masana tunanin dan-adam suka bayyana da bukarmu ta gaba daya ta son ji da kuma tuna mummunan labari.

Nazarin ya nuna cewa ba wai kawai abin da ya danganci jin dadin da mutane suke yi ba ne daga wani mummunan abu da ya shafi wani mutum.

Bayan wannan mun kasance yanayi na son jin bakin labari yana sa mu dauki matakin gaggawa a kan wata barazana.

Bakin labari na iya kasancewa wata alama ta bukatar mu sauya abin da muke yi domin mu kauce wa hadari.

Kamar za ka yi tsammani daga wannan nazari, akwai shedar da ke nuna cewa mutane suna saurin mayar da hankali a kan kalmomi marassa kyau.

Ka jarraba wani a dakin gwaji na kimiyya ka gani, da ka nuna kalmar ''sankara'' ko ''bam'' ko ''yaki'' nan da nan za ka ga ya motsa ba kamar a ce ka ambaci kalmar ''jariri'' ko ''murmushi'' ko ''dadi'' ba(duk da cewa wadannan kalmomi masu dadi kusan ana jinsu a ko da yaushe).

Muna kuma iya gane kalmomi marassa kyau da sauri a kan masu kyau, har ma kuma mu yi hasashen cewa kalma za ta kasance maras dadi kafin mu tabbatar da abin da kalmar za ta kasance.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mun fi zura ido mu ga kalmomi marassa kyau a kanun labarai

To kenan za mu iya cewa sa ido ko lura da muke yi kan wata barazana shi ne dalilin da zai bayyana abin da ya sa muke san jin bakin labari? Watakila a'a.

Akwai wata fassarar da Trussler da Soroka suka bayar ta shedarsu.

Masanan sun nuna cewa muna mayar da hankali a kan bakin labari ne sosai saboda muna daukar cewa duniya gidan dadi ce fiye da yadda take a zahiri.

Kuma idan muna magana a kan rayuwar mu kanmu sai mu dauka cewa mun fi yawancin mutane, kuma mu sa ran komai ya tafi daidai a karshe.

Wannan kyakkyawan tsammani ko kallo da muke yi wa duniya shi ya sa labari maras dadi yake zuwa mana da mamaki kuma muke ganinsa kamar wani abu na daban.

Saboda haka abin da ke jan hankalinmu ga mummunan labari ya iya kasancewa ya fi tantamar 'yan jarida (zargin samun wani mummunan abu a cikin wani abu ko da mai kyau ne a zahiri) sarkakiya ko kuma dai bukatar jin bakin labarin kawai.

Kuma hakan, a wata ranar ta mummunan labari, ya ba ni dan kwarin gwiwar cewa mutum zai yi nasara.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Psychology: Why bad news dominates the headlines