Hanyoyi biyar na kauce wa zama sakarai

Hakkin mallakar hoto Getty

Hatta mutanen da suke daukar kansu masu wayo da dabara da kuma kwarewa fiye da sauran jama'a sukan iya zama wawaye.

David Robson ya bayyana yadda za ka iya kauce wa hanyoyin da za a yi maka kallon sakarai.

Idan kana tantamar maganar cewa hatta mutumin da yake dauka cewa yana da wayo zai iya zama wawa, ka tuna da lokacin da mutumin da ya fi wayo a Amurka ya yi kokarin kashe talo-talo da wutar lantarki.

Benjamin Franklin yana kokarin yin wata gwaninta ce ta sanya wutar lantarki a cikin wani kofi na gilas a matsayin wani batiri na zamanin da.

Bayan da ya yi nasarar hakan, sai kuma ya ga cewa zai kara burge mutane sosai idan ya yi amfani da wutar batirin ya kashe tare da gasa talo-talonsa.

Yayin da yake kokarin nuna wa mutane wannan abin mamaki, sai wani abu ya dan dauke masa hankali, ya yi wani dan karamin kuskure, inda ya taba daya daga cikin kofinan masu lantarki yayin da a daya hannunsa yake rike da sarka.

''Wadanda suke wurin sun ce abin da ya faru kamar walkiya kuma karan da suka ji kamar an harba karamar bindiga ne,'' kamar yadda ya rubuta daga baya.

''Daga nan sai na ji abin da ban san yadda zan iya bayyana shi ba; wani duka na duniya gaba daya ya ratsa jiki na baki daya daga kai zuwa kafa, cikina da wajena, wanda bayan shi abin farko da na lura da shi, shi ne jikina yana ta jijjiga.'' (yana bayyana yadda wutar lantarki ta girgiza shi).

Wannan ya nuna karara cewa idan kana da basira hakan ba yana nufin ka fi hankali da tunani ba ke nan.

Ko da yake abu ne mai sauki a yi dariya kan wannan halayya ta Franklin, sauran misalan da zan gabatar masu ban tausayi da sa tunani ne.

Wani likitan tiyata na Amurka Atul Gawande ya yi rubutu sosai a kan manya-manyan kura-kurai a aikin likita na wannan zamanin.

Duk da kwarewar da suke da ita likitoci masu tiyata za su iya kuskuren salwantar da rai ta hanyar sakaci, kamar su manta da wanke hannunsu ko amfani da kaya masu tsafta.

A harkar kasuwanci gajeren tunani zai iya sa mutum ya yi wata raguwar dabara da za ta iya durkusar da kamfani baki daya.

Sabuwar hanyar da za a yi tunani:

Rober Sternberg na Jami'ar Cornell ya ce matsalar ita ce, ba a shirya tsarin iliminmu ba ta yadda za a koya mana yadda za mu yi tunanin da zai amfani kowa da kowa ba.

'' Jarrabawar da muke yi a makarantu (SAT, A-levels) a Ingila kawai hanyoyi ne na sanin matsayi a makaranta,'' ya ce.

''Za ka ga mutanen da suka samu kyakkyawan sakamako a makarantun amma sun gaza a shugabanci.

Za ka ga wasu kwararrun injiniyoyi ne amma ba su da natsuwa ko hankali kuma ba sa bin ka'idar aikinsu.

Wasunsu sun samu mukamin shugaba ko mataimaki na kamfanoni da kungiyoyi amma ko alama ba su cancanta ba.''

To me za a yi a kan haka? Sternberg da wasu masu irin tunaninsa na fafutukar ganin an kawo sauyi na samar da sabon tsarin ilimi wanda zai koya wa mutane yadda za su rika tunani da kyau tare da tafiyar da sauran harkoki na ilimi da aka saba yi.

Tunaninsu zai iya taimaka wa dukkaninmu, komai basirarmu ta yadda za mu rage zama sakarkaru:

1. Ka san rauninka

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kamar a wasan fim na Hanna Barbera, kana ji a zuciyarka cewa kai ka fi yawancin mutane iyawa da wayo? Dukkanmu ba mu na yin hakan ba. Abu ne da muke yi na yaudarar kanmu(illusory superiority). Kuma kamar yadda ake gani a wannan wasan talabijin wadanda ba su kai kowa iya ba ne suke jin haka.

A hujjarka za ka iya gabatar da sakamakonka na makaranta cewa lalle ka fi yawanci, to a nan sai a ce kana fama da wata matsalar ta daban, ta san-rai na tabbatarwa (confirmation bias) . Har yanzu ba ka yarda ba?

To a nan kuma masana tunanin dan-adam za su ce kana fama da matsalar san-rai na hana ganin rauni(bias blind-spot), yana yi na kin amincewa da gazawar tunaninka.

Gaskiyar magana ita ce kowannenmu na fama da wata matsala ta gazawa wadda ke tare da mu da kuma ba lalle mun san da ita ba, wadda kuma take rufe mana komai kama daga yadda za mu sayi gida zuwa ra'ayi ko fahimatrmu kan rikicin Crimea.

To amma kyaun abin shi ne masana tunanin dan-adam na kokarin gano cewa za a iya koya wa mutane yadda za su gano matsalolin.

Akwai hanyoyi kusan dari da za ka jarraba sai ka fara da wadannan tukuna.

2. Ya kasance a shirye kake ka amince da kuskurenka.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Amincewa da kura-kuranka na da amfani

''Ka da mutum ya ji kunyar cewa a kan kuskure da yake, wanda zai iya cewa ta wata sigar yau na fi fahimtar lamarin a kan jiya,'' Kamar yadda mai waken nan na karni 18 Alexander Pope ya rubuta.

A wurin masana tunanin dan-adam na yau, wannan tunani ana daukarsa budaddiyar zuciya (open-mindedness).

Baya ga wasu abubuwan, tana nuna yadda cikin sauki za ka iya fuskantar duk wani abu na rashin tabbas, da yadda cikin sauri za ka sauya ra'ayinka bisa dogara ga sabuwar hujja ko sheda.

Wannan dabi'a ce da ke da wuya wasu su iya dauka ko koya duk kuwa da cewa tana haifar da da mai ido a karshe. Misali Philip Tetlock na Jami'ar Pennysylvania a yanzu yana sa mutane gama-gari su yi hasashen wani yanayi na siyasa mai sarkakiya a na dambarwar shekara hudu. A nan ya gano cewa wadanda suka fi yin hasashe mai kyau sun dogara ne ga wannan dabi'a ta yarda da kuskurensu.

Ana samun mutum da saukin kai a fagen ilimi ta hanyoyi da dama; amma kashin bayan hakan shi ne yarda da iya matsayin iliminka.

Da wane dalili ka dogara ma'ana mecece hujjarka? Ya za a iya tantance hujjar? Wana karin bayani za ka nemo domin kara tabbatar da matsayinka? Ka duba wasu misalai na irin wannan yanayi domin kwatantawa?

Kana iya ganin bin wannan tsari daki-daki kamar wani mataki ne na 'yan koyo ko karami.

To amma da wannan tsari mai sauki, da yawa daga cikin mutanen da Tetlock ya yi wa wannan jarrabawa sun yi galaba da hasashensu a kan kwararrun masu hasashe da ke da basira, wadanda kila ba lalle ba ne su yarda da rashin saninsu.

3. Ka yi musu da kanka - kuma ka yi gaskiya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Idan kai ba ka saba yarda da raunin hujjarka ba duk da ka san cewa ta wani ta fi taka karfi, akwai hanyar da za ka bi domin raba kanka da wannan san rai: Ka duba hujja ko dalilin da ya fi naka ka dauke shi a matsayin naka ka rika kalubalantar ainahin naka dalilin wanda kasan yana da rauni. Ta wannan musun da kake yi da kanka a zuciyarka za ka yi nasarar kawar da yawancin wannan san rai naka, kamar ci-da-zuci da sauransu, da hakan sai ka yi nasarar karyo da zuciyarka ta yadda za ta yarda ka amince da dalilin da ya fi naka.

Wata hanyar makamanciyar wannan kuma, ita ce ka sa kanka a matsayin wani ka yi tunanin dalilinsa. Wannan zai yi amfani musamman idan kana fama da matsaloli na kanka;kamar a labarin Sarki Solomon a Injila, mun fi dabara idan muna ba wa wasu shawara fiye da idanmuna fama da matsalolin da suka shafemu.

4. Ka yi tunanin '' idan da kuma a ce.....''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Daya daga cikin manyan matsalolin da ke tattare da tsarin ilimin da Sternberg ke korafi a kai ita ce ba a koya mana yadda za mu yi amfani da tunaninmu a abin da yake na zahiri ko kuma mu zama masu kirkira.

Duk da cewa mun daina bin tsarin karatun hadda kawai, malamai da dama har yanzu ba sa koyar da ilimin da ake bukata wajen tafiyar da al'amuran rayuwa na gaske.

Wata hanya ta samun ilimin hakan ita ce ka rika sake tunanin wasu muhimman abubuwa da suka faru.

Daliban tarihi za su iya dubawa su yi rubutu a kan misali, da ya duniya za ta kasance, misali, idan da Jamusawa sun yi nasarar yakin duniya na biyu?

Ko kuma, ''Da me zai faru idan da Burtaniya ta rushe tsarin mulkin mulukiyya a karni na 17?'' .

Idan kai ka dalibin tarihi ba ne, za ka iya rubutu kan tunanin abin da zai kasance''Ranar da shugaban kasa ya ajiye aiki'' ko ''Ranar da matata ta bata'' duka wadannan za su iya sa ka a hanya. Za ka ga hakan kamar ba wani abu bane, amma abin shi ne wannan zaitilasta maka ka yi tunanin wasu abubuwan da za su iya faruwa ka yi tunanin hanyar da za a bi domin warware matsala.

Kananan yara suna koyon irin wannan tunani a wasan kwaikwayo da suke yi wanda yake taimaka musu koyon komai kama daga dokokin kimiyyar lissafi (physics) zuwa dabaru na mu'amulla.

Ba ma bukatar mu yi kamar yadda yara suke yin wadannan wasanni na kwaikwayo a matsayinmu na manya, to amma za ka cewa za ka iya bunkasa tunaninka a lokacin da kake kokarin shawo kan wata matsala da ta zo maka ba tsammani.

5. Ka da ka rena jerin yawan ka'idojin da za ka kiyaye

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kamar yadda hadarin jan wutar lantarki da ya samu Franklin ya nuna, wani abu ya dauke maka hankali ko kuma hankalinka ya kasance ba ya kan abin da kake yi zai iya kasancewa dalilin faduwar wanda ya fi mu kwarewa.

Idan kana fama da yanayi ko abin da ya kunshi matakai da dama,abu ne mai sauki ka manta wata ka'ida, wanda wannan shi ya sa Gwanade ya kasance mai ra'ayin ganin mutum ya rubuta matakan yin aikinsa daya bayan daya a matsayin hanyar tunatarwa.

Misali a asibitin John Hopkins an rubuta jerin wasu muhimman matakai guda biyar na tunatar da likitoci hanyoyin tabbatar da tsafta, wanda hakan ya rage yawan yada cuta na kwana goma daga kashi 11 cikin dari zuwa sifili.

Irin wannan jerin dokoki da aka yi wa masu tukin jirgin sama na tunatar da su muhimman matakan da za a bi wajen tashi da sauka ya rage yawan mutuwar matuka jirgin sama na Amurka da rabi a lokacin yakin duniya na biyu.

Kamar yadda Gawande ya bayyana, wadannan fa kwararru ne wadanda suka san fasaha sosai amma duk da haka 'yar takardar tunatarwa mai dauke da jerin ka'idojin aikinsu ta ceto rayukan da dama daga cikinsu.

Ko da wana irin aiki kake yi abu ne mai muhimmanci ka kiyaye da wannan shawara kafin ka dauka cewa ai abu ne da riga na sani.

Ka gwada wadannan matakan za ka wayi gari ka ga cewa ka fara gano wata baiwa da kake da ita wadda ba ka san kana da ita ba.

Idan kana neman wanda zai karfafa maka gwiwa ka duba Sternberg, wanda a lokacin da yake yaro ya fadi jarrabawar gwajin basirarsa wanwar kuma ba shi da wani kokari a darussan boko.

'' Dukkanin malamaina sun dauka cewa ni sakarai ne ni ma kaina na dauka cewa ni sakaran ne.'' In ji shi.

Da zai yi watsi ne da makaranta inda a ce daga baya bai hadu da mutumin da ya karfafa masa gwiwa da cewa amfanin tunani ko kwakwalwa ba ya tsaya ba ne a kan iya wassafa matsalolin da ba ganinsu kake yi a zahiri ba kamar yadda yake a tsarin karatun boko.

Inda mutumin ya karfafa masa gwiwa kan ya horad da zuciya ko kwakwalwarsa a wasu fannonin, wato ya fadada tunaninsa.

A sanadiyyar wannan taimako da ya samu a yanzu Farfesa ne a Cornell.

''Basira ba maunin jarrabawar karfin tunaninka ba ce, hanya ce kawai ta gano abin da kake so a rayuwa da gano yadda za ka samu abin'' ya ce, ko da kuwa hakan na bukatar ka amince da wani sakarcinka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan A five-step guide to not being stupid