'Zan iya hasashen yanayi da hancina'

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani mutum ya samu kansa a yanayi na wata larura da a duk lokacin da za a iya yin ruwa zai ji alamun hakan ta hanyar jin kaurin hayakin itace da warin yawu.

Helen Thompson ta gana da mutumin da za a iya kwatantawa da na'urar auna yanayi.

Max Livesey yana bakin hutunsa na shekara ne a lokacin kawai ya ji yana jin kaurin hayakin ganyayyaki ko itace.

Ya duba harabar otal din da yake iya dubawarsa amma bai ga alamun inda wannan kauri yake fitowa.

Bayan 'yan makwanni sai ya ji kaurin ya karu daga na katako kuma zuwa na yajin albasa.

Abin ya kai har yake ganin cewa ba abin da zai sa wannan wari haka sai dai ko idan da akwai tarin wata nau'in kyanwa (skunks) da ke tsarta wani yawu mai wari idan wani abu ya kawo mata hari.

''Sai na fara jin idanuwana na ruwa, kuma ina jin wani makaki a makwogarona,'' ya ce.

Livesey (ba sunansa na gaskiya ba kenan), wanda yanzu ya kai shekara 72 kwararre ne a fannin manhajar kwamfuta da farko ya danganta wannan yanayi na kauri da wari da ya ji a kan dakin otal.

Hakkin mallakar hoto Getty

To amma bayan ya koma gida sai ya ci gaba da jin wannan kauri yana kuma karuwa.

Daga nan sai Livesey ya yanke shawarar zuwa ganin kwararren likita a cibiyar magani da bincike kan jin kanshi da wari da kuma dandano da ke Chicago, Alan Hirsch.

Bayan gwajin da ya yi masa, likitan ya gano cewa Livesey ya samu matsala a bangaren yanayin jin kanshi da warinsa.

Likitan ya gano cewa wannan ba wani abu ba ne sabo musamman ma ganin Livesey na da cutar nan ta karkarwa (parkinson), wanda kuma daman matsalar jin kashi ko wari wata alama ce ta cutar.

Wannan ana gani na faruwa ne saboda cutar na bannata kwayoyin halittar da ke aikin tura sakon kanshi da wari ne daga hanci zuwa kwakwalwa.

To amma me yasa mutumin yake jin wannan kauri wanda kuma a zahiri ba daga wani abu ko wuri yake fitowa ba?

Dukkaninmu a wani lokaci mu kan ji wani kanshi ko wari na wani abu duk da cewa ba mu ga wannan abin me waannan kanshi ko wari ba.

To idan kuma aka samu yanayi da kwayoyin halittar da ke aikin kanshi da wari a hancinmu suka samu matsala sai mutum ya rika jin wannan kanshi ko wari na bogi (kamar yadda mutumin da yake da matsalar jin magana ya kan iya jin wani kara na bogi a wani lokaci).

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES

To idan muka koma kan maganar Livesey, a kwana a tashi sai ya fara jin wani abu sabo a game da wannan matsala ta shi yadda jin wannan kauri na hayakin itace ke karuwa a duk lokacin da aka kusa yin ruwan sama.

Haka kuma abin zai ci gaba da karuwa har a yi ruwan.

A wani lokacin sai ya ce zai iya hasashen za a yi ruwan saman sa'oi goma kafin ruwan.

Likita Hirsch ya ce wannan ne karon farko da ya taba ganin irin wannan matsala ta hanci da ta hadu da yanayi.

Sai dai ba wannan ba ne karon farko a tarihi da cutar dan-adam ta samu alaka ko kulla dangantaka da yanayi ba.

Gwiwowina na ciwo......ina ganin za a fara ruwa

Sama da shekaru dubu biyu da suka wuce, Hippocrates ya lura da alaka tsakanin 'yan cutuka ko rashin jin dadi da mutum kan ji wani lokaci a jikinsa da yanayi.

A shekara ta 1887, masu bincike sun fara nazari kan wannan dangantaka kuma suka gano alaka mai girma sosai tsakanin yanayin zafi da sanyi da lema da kuma ciwon gabobin jiki a wurin mutanen da ke fama da wannan matsala.

Tun daga wannan lokacin a ka kara tabbatar da dangantaka tsakanin yanayi da irin ciwon kan nan na barin kai daya.

Haka ku akwai alaka tsakanin yanayi da ciwon da mutane masu fama da larurar kankamewar tsokar wani sashen jiki (sclerosis) kan yi.

Hirsch ya ce wani abu kuma da ba a sani ba sosai shi ne yadda aikin hancinmu na karfin jin kanshi ko wari yake raguwa idan aka samu sauyi na yanayin karfin iska da ken dannowa kasa daga sama(pressure).

Misali idan mutum ya hau jirgin sama karfin wannan iska ko nauyinta ya ragu sai jin kanshi da warinsa ya ragu.

Tun da karfin wannan iska da ake samu kafin ruwan sama ya sauka tana rage aikin hancin Livessey na jin kanshi da wari, hakan zai iya sa ya rika jin wannan kaurin hayaki da za mu iya cewa na bogi, wanda kuma shi a wurinsa alama ce da ke nuna za a yi ruwa.

Za ta iya kasancewa wannan matsala ta jin kauri da Livesey ya gamu da ita ta zama cewa dace ne ake yi take karuwa kafin a yi ruwan sama kawai maimakon wasu lokutan.

Ko kuma za ta iya kasancewa daman ya riga ya dan san wani abu game da hasashen yanayin.

To amma Livesey bai yarda da hakan ba, domin a lokaci da dama bai ma ga hasashen yanayin ba amma kuma yake iya hasashen yanayi maras kyau.

Hirsch ya kuma yi amanna cewa akwai alaka tsakanin yanayi da irin wannan larura da mutum zai rika jin wari ko kanshi ko kauri kuma wani abu na bogi( da zai rika yi wa mutum gizo).

Ya bayar da misalin yadda ake ganin irin wannan matsala a kan misali masu hawan dogayen tsaunuka idan aka sa su atisaye a wani wuri da ba karfin iska kamar irin wurin da suka saba za su iya jin wannan yanayi na jin wani abu na bogi.

''Haka su ma masu yin tattaki na dogon zango a yankin da yake tudu sosai a Antaktika ( Antarctica) mun ga irin wannan matsala a tare da su,'' in ji Hirsch.

Tun lokacin da ya hadu da Livesey, likita Hirsch ya yi wa wasu mutanen da suke da irin wannan larura magani:

Ya ce, '' Duk wanda muka gani kawo yanzu kusan a ce yana da matsalar jin kanshi da wari kuma yana nuna mana yadda abin yake karuwa ko karfi kafin a yi ruwan sama.

Wannan matsala ce wadda da wuya a iya gudanar da bincike a kanta ba tare da samun wani ra'ayi ba.

A wani gwaji guda daya Hirsch ya yi kokarin tasowa masu wannan larura matsalar ta hanyar sa su a lifta (lift) ko na'urar da ke kai mutane sama a dogayen benaye, a cibiyar John Hancock da ke Chicago.

Wannan gini ne mai bene hawa 100 ko kafa 1,127.

Ko da yake Livesey bai ji wani sauyi a kan yanayin nasa duk da hawa wannan dogon bene da ya yi, amma Hirsch ya ce hawan ya sa matsalar ta jin kanshi ta tasowa wasu daga cikin marassa lafiyar, wanda shi yana ganin tana da dangantaka da bambancin nauyin iskar wuri (pressure).

Abin takaicin shi ne babu wani magani na dindindin na wannan matsala.

A 'yan shekarun da suka gabata Livesey ya kara wani magani mai suna L-dopa cikin jerin magungunan da yake amfani da su na ciwonsa na karkarwa (parkinson) a sanadiyyar hakan cikin 'yan watanni wannan matsala ta jin kaurin hayakin ita ce ta ragu.

Amma a kwanakin nan larurar ta dawo, ko da yake an yi fama da matsalar yanayi a Chicagon.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shinshina furanni zai iya sa ka daina jin warin da kake ji

Wata dabara ta rage wannan matsala ta Livesey, ita ce ta yadda zai rika kara karfin sauran kwayoyin halittar hancinsa na jin kanshi da wari.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, kamar yadda Hirsch ya shawarce shi ya riga shinshina turare kala uku sau uku a duk rana, kuma kanshin turarukan uku da yake ji suka maye wannan na kaurin hayakin itacen da ke taso masa.

''Ga alama abin yana taimaka masa,'' in ji likitan, ''amma kuma kila ba haka lamarin yake ba saboda dai muna fatan ganin hakan ne kawai sai muke ganin kamar abin yana aiki.''

A yawancin lokaci yana ma mantawa ne kawai da kanshin turarukan, ka ga kamar ma bai damu ba yana dariya yana ciye-ciyensa.

Matsalar jin kaurin ta Livesey ba wata mai ciwo ba ce amma tana sa damuwa, likitan ya ce.

''Idan ta taso masa sosai sai ya rika jin wari kamar na kashi, wannan abin damuwa ne da dauke hankali.''

Ya ce wani lokaci kauri ko warin yakan sauya amma ko da yaushe ba shi da dadi.

''Matsalar takan jawo min wasu matsalolin kamar idona ya rika ruwa,'' ya ce, ''akwai mutanen da na ji an ce su kanshin furanni suke ji. Zan so in san wanda yake jin wannan, gaskiya zan so a ce ni ma haka nake!''

Ban san ko wani ya taba tambayarsa ya yanayi zai kasance ba. Sai dai kawai ya yi dariya idan ka tambaye shi hakan.

Sai ya ce maka, ''a'a hasashen ba dari bisa dari ba ne. Ni ba hukumar kula da yanayi ta kasa ba ne. Idan dai suka tambaye ni ce musu nake su je su duba na'urarsu ta iPad!''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan 'I can predict the weather with my nose'