Yadda fuskarka ke bayyana sirrinka

Hakkin mallakar hoto Getty

Matsayin fuskarmu bai tsaya ga kyau ba kadai, domin tsari da girma har ma da launin fuskar kan iya bayar da muhimman bayanai a kan dabi'armu da lafiyarmu kai har ma da yanayinmu na saduwa (jima'i).

David Robson ya bincika wannan lamari:

Za ka yi tsammanin sai kwararren masanin falsafa ya kutsa can cikin ruhinka ya iya hasashe ko fahimtar halayyarka da wasu abubuwa da suka shafi lafiyarka da sauransu.

Amma malaman falsafa na zamanin da na Girka ba sai sun kai ga haka ba domin su daga kamanninka kawai za su iya hasashe a kanka.

Aristotle da almajiransa ko mabiyansa har littattafai suka rubuta a kan hanyar da kamanninka za su iya nuna halayyarka.

'' Gashi mai laushi na nuna alamar tsoro yayin da mai karfi ko kauri ke nuna alamun mutum mai karfin hali,'' a yadda suka rubuta.

''Rashin kunya ko rashin mutunci ana ganin alamunsa ne a mutumin da ka ga idonsa budadde mai haske da kuma 'yar zirin fatar da ke rufe idonsa ta kasance ja'' Kamar yadda littattafan uku suka bayyana.

Babban hanci ko hanci mai fadi shi yana matsayin alamar ragwanci ko kasala kamar yadda ake gani a saniya ne.

Masana falsafar sun kuma bayyana lebe mai kauri a matsayin wata alama ta wawanci, ''kamar jaki'', su kuwa mutanen da ka gan su da baki ko lebe siriri su ke kasancewa masu alfahari kamar zaki.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masanan Girka na zamanin da suna ganin mutumin da za ka ga yana hura hanci kuma kofar hancinsa babba ce wannan malalaci ne

A yau ana nuna cewa ka da mu yanke hukunci kan yadda littafi zai iya kasancewa daga ganin bangonsa kawai.

Duk da yadda ake nuna cewa ka da mutum ya bayar da fifiko wajen yin la'akari da kamanni a yanke hukunci ko bayar da fassara, masana tunanin dan-adam sun fara gano cewa fuskarka na iya bayyana sirrin can cikinka.

Ko da ka murtuke fuska kamar fuskar shanu da ake cewa, to kamannin fuskarka ka iya bayyana yadda yanayinka yake da lafiyarka da kuma basirarka.

Kirar gadara da nuna iko

Carmen Lefevre ta Jami'ar Northumbria ta bayyana cewa, tsarin shi ne kamar yadda yanayin halittarmu yake da kwayoyin halittar da yawansu duk suna da tasiri wajen girmanmu.

Kuma wadannan abubuwa harwayau suna da tasiri wajen tsara halayyarmu.

Ka duba girma ko tsarin kashin fuskar mutum, idan yana da fadi da gajarta ko kuma yana da tsawo da sirantaka.

Malamar jami'ar ta gano cewa mutanen da suke da yawan kwayar halittar balagar namiji da jima'insa (testosterone), su ne masu fadin fuska da babban kashin kunci ko kumatu.

Haka kuma masu wannan siffa suna da yanayi na nuna iko da saurin bacin rai da fada a wani lokaci.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan alaka ta siffar fuska da kuma halayya ta watsu tsakanin mutane har ma da birai

Domin a tsakanin irin wani biri da ake kira ''capuchin'' da Ingilishi za ka ga masu fadin fuska sun fi nuna iko da gadara a cikin sauran birai danginsu.

Haka kuma a cikin kwararrun 'yan wasan kwallon kafa, ana ganin tasirin wannan siffa.

Kamar yadda Keith Welker na Jami'ar Boulder da ke Colorado ya nuna kwanan nan.

A nazarin da ya yi a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ta 2010, yanayin fadin fuskar mutum na iya sa a yi hasashen yawan laifin da dan wasan tsakiya zai iya yi da kuma yawan kwallon da dan wasan gaba zai iya ci.

(Idan kana son auna fadin fuskar kai da kanka, za ka iya. Idan ka auna nisan da ke tsakanin kunne zuwa kunne sai ka kwatanta da nisan da ya kama daga saman idonka zuwa lebenka na sama.

Yawanci bambancinsu idan aka raba yana kamawa biyu ne. Na Abrahama Lincoln 1.93 ne.)

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Abraham Lincoln

Harwayau fadin fuskar zai iya ba ka damar sanin dalilin dan siyasa na yin wani abu.

Lefevre ta yi amfani da wasu mutane wajen nazari, inda ta auna tsoffin shugabannin Amurka a kan wasu abubuwa da suka shafi halayya daban-daban kamar burinsu da kuma irin matakin da suka dauka na cimma burin ko wata manufa.

Babban kumatu

Kamar yadda watakila ka sani, za a iya sanin matsayin lafiyarka da ma tarihin lafiyar taka ta hanyar nazarin fuskarka, kuma bayanin da za a samu zai ba ka mamaki.

Yawan teba ko kibarka ta fuska misali ka iya bayar da bayani mai gamsarwa a kan lafiyarka fiye da yadda za a gano daga nauyinka.

Mutanen da ke da fuska maras fadi ba kasafai suke kamuwa da cuta ba, kuma idan har sun kamu to ba ta musu tsanani.

Haka kuma ba sosai suke gamuwa da cutar damuwa ba, wanda watakila saboda ana ganin lafiyar kwakwalwa tana da alaka da kyawun jiki gaba daya.

Ta yaya girman kumatunka zai iya bayar da bayani a kanka?

Benedict Jones na Jami'ar Glasgow yana ganin wata sabuwar fahimta da aka gano ta aikin maiko a jiki za ta iya taimakawa wajen bayyana hakan.

Ya ce, ''Lafiyarka ba ta dogara ne da yawan maikon da ke jikinka ba ne, sai a ce a ina maikon yake a jikinka''.

Mutanen da ke da kiba daga kugunsu da duwawu amma a samansu (gangar jiki) ba su da kiba(pear-shaped) sun fi lafiya a kan wadanda suke da kiba a gangar jiki daga kugu zuwa kasa kuma ba su da kiba(apple-shaped). In ji (Benedict Jones) malamin jami'ar.

Masanin ya ce yawan kibar da mutum yake da ita a saman jikin (kirji), ana ganin tana fitar da wasu kwayoyi ne da za su iya cutar da muhimman kayan cikin mutum.

Watakila cikar fuskarka ita ke nuna yawan maiko ko kibar da ke sassan jikinka masu hadari, in ji Jones.

Ko kuma a ce shi kansa maiko ko kibar ta fuska hadari ce ita kanta a bisa wani dalili.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Irin wannan birin da ake kira Capuchin mai fadin fuska ana ganin shi ma kamar mutum yana da fada da bacin rai

Bayan wadannan alamu na siffa, hatta dan bambanci na launin fata zai iya bayyana wani abu game da sirrin lafiyarka.

Jones da Lefevre sun jaddada cewa wannan ba shi da nasaba da launin kabilar mutum fa, sai dai yanayin rayuwarsa kawai.

Suka ce mutumin da yake da launi ko fatarsa ta kasance tana da launi rawaya-rawaya ko ruwan dorawa da kuma dan ruwan zinare to wannan yana da lafiya sosai.

Abin da ke sa wannan launi (carotenoids) ana samunsa ne a lemon zaki da jajayen 'ya'yan itatuwa da ganyayyaki.

Wannan sinadari yana taimaka mana wajen samun garkuwar jiki mai karfi, kamar yadda Lefevre ta ce.

''Amma idan muka ci da yawa sai sinadarin ya kwanta a fatarmu ya sa launinta ya zama ruwan dorawa.

Muna nuna su ta fatarmu ne saboda ba mu yi amfani da su ba wajen yakar cutuka ko rashin lafiya.''

Wannan launi na lafiya da ka samu ta wannan hanya yana taimakawa wajen kara maka kyau fiye da yadda za ka je kanti a sauya maka launin fata.

Idan aka ga fatar mutum ta dan yi launin ja ko ruwan hoda alama ce ta cikakkiyar lafiya ( jini na kewayawa a jikin mutum yadda ya kamata).

Kuma hakan zai iya kasancewa alama ce ta mace za ta iya daukar juna biyu.

Jones ya gano cewa mata sukan dan sauya launi su yi ja idan suna kusan karshen al'adarsu, watakila saboda kwayoyin halittarsu na jima'i na sanya jijiyoyin jini na kumatu su dan kara budewa (jini ya karu a kumatun).

Watakila wannan na daya daga cikin sauye-sauyen da ake samu na jiki da da kuma dabi'a wadanda suke sa mace ta dan kara kyau idan ta shiga lokacin da za ta iya samun juna biyu.

Ka yi tsaf

Kamar yadda Jones ya nuna wadannan duka sirri ne da suke boye a fili, amma kuma sai a sannu muke gano su.

Ko ba komai wannan ya taimaka wajen dawo da kimar ilimin fassara yanayin mutum da halayyarsa ta hanyar nazarin fuskarsa, wanda ya gamu da koma baya tun kalaman sukan da Aristotle ya yi a kai.

Sarkin Ingila Henry na takwas (Tudor King Henry VIII), shi ma bai yarda da nazarin ba har ma ya hana wadanda ya kira farfesoshi na bogi cin moriyar nazarce-nazarcen da suka yi.

Al'amarin ya sake gamuwa da wani koma bayan a karni na 20 lokacin da aka danganta shi da kuskuren nan na ilimi da ake cewa hawa da gargadar kan mutum ka iya taimakawa wajen bayyana hasashen dabi'ar mutum.

To amma yanzu wannan nazari ya fara samun tagomashi, inda za mu ka abubuwa da dama na ban mamaki da ke boye a hotunan fuskarmu da muke dauka.

Wani abin shi ne a yanzu ga alama muna iya hasashen basirar mutum da kyau daga nazarin fuskarsa, ko da yake ba a san takamaimai abubuwan da ake lura da su ba wajen yin hakan ya zuwa yanzu.

Wasu kuma a yanzu suna iya gane mutum idan dan ludai ne.

Muna iya gane yanayin mutum ko dan luwadi ko mai wace irin dabi'a ne ta dangantakar saduwar jinsi a cikin dakika daya ko da kuwa ba shi da wata alama ta fili da aka san masu wannan dabi'a da ita.

Duk da haka wannan abin mamaki ta yadda muke iya yin hakan

Wasu karin bincike-binciken da nazari za su iya sa mu gano yadda muke iya wannan hasashe da kyau.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Haka kuma abu ne mai ban sha'awa ganin yadda alaka take tsakanin yanayin mutum da yanayin yadda yake rayuwarsa da kuma kamanninsa duka suke sauyawa daga matakin girma ko shekaru zuwa shekaru.

Wani nazari ya duba yadda tarihin yanayin mutane yake da yadda suke bayyana, inda ya bi diddigin wasu mutane daga shekarun 1930 har zuwa shekarun 1990.

Masanan sun gano cewa ko da yake mutanen da ke da fuska irin ta yara ba su da dabi'ar nuna iko da isa a lokacin da suke matasa, amma idan suka girma sai su dauki wadannan dabi'u.

Wato kamar suna ramako ke nan na abin da ake tsammani su yi a baya saboda kamanninsu, wanda ba su yi ba.

Haka kuma dai masanan sun kuma gano shedar yadda mutanen da suka girma suke bayyanar da wasu halaye da aya kamata a ce sun yi lokacin suna yara amma ba su yi ba a lokacin.

Misali matan da suke da kyau da kuma mu'amulla a lokacin da suke matasa zuwa shekaru 30 a hankali sai kyawun nan nasu ya fara bayyana, idan suka kai shekara 50 sai a ga sun fi kyau fiye da yadda suke lokacin suna 'yan mata, wadanda kuma a lokacin mu'amullarsa da maza ba ta kai ta yanzu ba amma kuma sun fi kyau a lokacin ( saboda farkon balagarsu).

Abin da zai iya jawo wannan shi ne a yanzu sun san yadda ya kamata su kula da kansu adonsu da jikinsu kuma yanzu sun fi da karfin hali.

Hakkin mallakar hoto Getty

Bayan duk wannan, wani nazari na baya-bayan nan ya nuna cewa akwai wasu abubuwa da dama a game da kamanninmu ba wai kawai kasancewar fuska a matsayin kashi da launin fata ba.

Masana kimiyyar sun bukaci mutanen da suke nazari da su, su sanya tufafin da suka fi so sannan su dauki hotunan fuskokinsu.

Duk da cewa ba a ganin kayan nasu a hoton, amma masu nazari sun ce hotunan sun fi sauran hotunan da mutanen suka dauka lokacin da ba su sanya wadannan kayan da suka fi so ba.

Fuskokinmu ba kawai tsari ne na halittarmu ba, domin duk da cewa ba za mu iya sauya kwayoyin halittarmu ba, amma idan muka gano daraja da kimar kanmu za mu ga fuskokin namu kila sun bujiro da wasu abubuwan da suka ma fi amfani.

Idan akan son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How your face betrays your personality and health