Karar da ba ka taba ji ba a duniya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kana jin irin karar da nake ji? Ba na jin haka. Haka dai mutane ke jin wata kara ta daban wadda ba ka san irinta ba, kuma kowa da yadda yake jintaa daban. In ji David Robson.

''Kun san an gaya muku ku nuna sanin ya kamata ka da ku yi ihu?'' Abin da Sophie Meekings ta gaya wa masu sauraronta ke nan a wani daki na karkashin kasa na wani gidan shan barasa na Landan. '' To yanzu za ku iya yi min kara ko ihu idan kuna so, amma dai ko kun yi ba shi da wani amfani saboda ba zan iya jinku ba,''

Ita dai Meekings kusan a ce tana wasa ne kawai da wadannan kalamai da take yi musu, saboda bebiya ce kuma da sai ta dage sosai ta san ma hirar da ake yi a kusa da ita.

Abin tattaunawa a kan maganarta shi ne yadda mutane ke jin magana da kuma amo ko karar da muke ji wadda ba mu san takamaimai yadda za mu iya bayyana ta ba a wani lokaci.

Domin nazari a kan darasin sai ta kunna wata kara iri daban-daban, wadda na daga karar da ban taba jin irinsu ba a duniya.

Abin da ya ba ni mamaki shi ne yadda cikin sauki wannan kara ta raba kan masu saurare.

Karar da ta kunna daya bayan daya ta nuna yadda muke yin fassara da fahimtarmu daban-daban kan abu daya, wanda a takaice hakan ke nuna yadda kowa ne mutum ke yi wa duniya rin fassararsa.

Ana gaya mana cewa gani bai zama yarda ba lalle, amma ban taba sanin cewa haka kuma jinmu shi ma yana da wuyar sha'ani da fahimta da kuma yaudara ba shi ma.

Fitowata daga wannan dakin karkashin kasa sai na fara tunanin wai shin ma nawa ne daga cikin wannan kara da naji a dakin take ta gaskiya, ta yaya zan iya ganewa ma ba kwakwalwata ce kawai ta ke min wasa ba ma?

Tun daga wannan lokaci nake ganin na samu sauyi kan yadda nake jin kara da bayyana abin da na ji.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwakwalwarmu ta kan yi hasashen yadda sauti yake,saboda haka abin da ka ji ba lalle haka yake ba

Saboda na zaku in san me Meekings take nufi da wannan nazari ko bincike a kanmu, sai na same ta a dakin bincikenta na kimiyya a kwalejin Jami'ar Landan bayan mako biyu.

A nan ta dan kara min bayani a kan maganarta da kuma nazarin da ta sanya a gaba.

Duk da yadda malamanta na makaranta da na jami'a da suke ganin za ta karu sosai daga larurarta (kuramta), idan ta zabi yin karatu a fannin kimiyyar ji (auditory neuroscience) abin da da farko ba ta yarda ba, za ta amfana sosai.

Amma daga baya wani daga cikin malaman ya shawokanta ta amince da hakan.

''Ya yi min romon-baka da cewa zan iya gano wani ilimi kan yadda mutane ke jin abubuwa, ''ta ce. ''Kuma sai na yi tunanin hakan, na ce watakila haka ne fa.''

A yau binciken da take yi yawanci ya shafi yadda muke fahimtar kara ne a lokacin liyafar da jama'a suka taru ake bushasha.

Abin da ta gano shi ne ko da mutane suna wata tattaunawa, duk da haka a wannan lokaci kwakwalwarmu tana sauraren hirarraki ko maganganun da ake yi a can bayanmu da hakan ke taimka wa maganarmu tana kasancewa ko kutsawa a daidai lokacin da aka yi dan shiru a wadancan maganganu na bayanmu.

A yanzu tana gudanar da binciken kwakwalwa ta gano yadda muke iya hada wadannan abubuwa ko karin aiki ba tare da mun bar zancen da muke yi ba, ko mun rude da wanda muke yi din (wato yadda muke iya tauna taura biyu a lokaci daya).

Wannan sha'awa tata kan yadda kwakwalwa ke iya sarrafa sautuka ita ta sa ta kawo batun yadda kunne ke jin wasu sautuka na daban a wani taron barkwanci na kimiyya.

Ta ce, ''Mutane ba su san cewa irin karar da nake ji ba kila ta bambanta da wadda suke ji.''

Za ka ga misalin farko da Meekings ta bayar ka dauka abu ne mai sauki kawai amma daga bisani za ka ga ya nuna yadda lamarin yake sosai.

Za ka iya jin tagwayen sauti har guda hudu. A cikin kowa ne daya za ka iya tantancewa wanne ne ya fi kara wanne ne ba shi da kara kamar dayan?

Da ta kunna mana sautukan a wannan daki na karkashin kasa a Landan, sai ta ce mana mu daga hannu idan mun ji karar ta karu haka kuma mu daga hannu idan mun ji ta ragu.

Sai aka samu yawan mutunen ya kasance daidai wato ba bangaren da ya fi wani.

Abin mamakin shi ne abin da kai kake ji ba shi ne abin da na gabanka ko kusa da kai yake ji ba.

''Abu ne mai wuya domin muna son dukkaninmu mu ji abu iri daya a duniya,'' in ji Meekings.

Wato dai a zahiri babu amsar da take daidai. Kowanne daga cikin sautukan ya kunshi abubuwa ne da dama, saboda haka abu ne da ba zai yuwu ba ka ce wanda ya biyo baya ya fi kara ko bai kai karar na farko ba.

Sai dai ita kwakwalwa ba ta son abin da zai sa ta kasa tantancewa, saboda haka sai ta yi hasashen da take gani ya yi mata.

Abin mamaki kuma kamar yadda wani bincike da Diana Deutsch ta Jami'ar California ta San Diego ta yi ga alama amsarmu ta dogara ne ga karin harshe ko kuma harshenmu (yare).

Saboda misali, mutanen California sun fi zaben abin da ya saba wa mutanen Ingila.

A kan wannan dalilin take ganin yanayin maganarmu ta lokacin yarinta watakila yana tasiri ko kuma shi ke sa yadda muke daukar amon sautin kida.

Deutsch ta gano cewa masu amfani da hannun dama suna jin sauti mafi kara ne ta kunnensu na hannun dama, yayin da su kuma masu amfani da hannun hagu suka fi jinsa ta kunnen hagu, ko kuma ta kunnuwan biyu a lokaci daya.

Wannan kyakkyawan misali ne na yadda bambancin da mutane daban-daban suke da shi a kwakwalwarsu ke iya haifar da bambanci kan yadda muke fahimtar abu, ba tare da cewa mun san yanayin fahimtarmu ya bambanta da na mutumin da yake kusa da mu ba.

Wadannan kura-kurai su ne bambance-bambancen da suke tabbatar da ka'idar.

Yadda kwakwalwa ke iya sarrafawa da tsara hankalinmu na taimaka mana mu san yadda duniyarmu take, saboda haka ne ma muke iya jin kalmar ''tsaya'' duk da hayaniyar da ake yi da ruguntsumi a titi a misali.

Meekings ta kwatanta wannan ruguntsumi ko hayaniya da taliya, ta yadda kwakwalwa ke iya gane duk wani sauti, kamar yadda kake iya ganin kowa ne sili daya na taliya.

''kai kamar wani mai bincike ko gano sauti ne a kullum saboda a kullum kana cikin wannan hayaniya kamar abincinka na taliya, wanda kuma kake iya gane kowa ne sauti da kyau ba ma tare da ka san kana yi ba.'' In ji masaniyar.

In ba don irin wannan baiwa ko aiki na kwakwalwar mutum na iya tace sauti ba, da ita kanta Meekings ba za ta iya amfani da iliminta na nazarin motsin leben mutum ba ta kara fahimtar abin da take ji da taimakon 'yar na'urar kara jin magana da take sanya wa a kunnenta ba.

A ko da yaushe tana cikin wannan abu ne ita ma kamar yadda sauran mutane masu lafiyar kunne su ma suke yi.

Ta ce, ''bincikena ya sa na kara mutunta kunnuwana, saboda irin abubuwan da nake samu kwakwalwata na kokarin bayyana su da kyau,''

Sautin maras kan gado da mukan ji, tana ganin zai iya sa mu kara jin dadin wannan abin mamaki.

''Idan ka ji wadannan sautuka masu wuyar fahimta ko wadanda ba ka san kansu ba balle gindinsu daga nan ne kake sanin cewa kana wani abu na ban mamaki mai sarkakiya.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The strangest sounds in the world