Burtaniya: Allah daya gari bamban

Hakkin mallakar hoto Dougie Wallace INSTITUTE

A wani sashe na birnin Glasgow ana sa ran mutum namiji ya rayu tsawon shekara 54 kawai amma takwarorinsa na yankin Kensington da Chelsea a Landan ana tsammanin su kai shekara 84 kafin su mutu.

Daukar hotunan da ke nuna irin wannan bambanci shi ne abin da mai daukar hoto Dougie Wallace yake da sha'awar yi.

Tom Seymour ya duba wannan labari.

Duk namijin da ya yi gam-da-katar (gamo-da-katari) ya rayu a yankin karamar hukumar Kensington and Chelsea na birnin Landan, to za a iya cewa kakarsa ta yanke saka idan mai son tsawon rayuwa ne, domin ana kyautata masa tsammanin zai kai shekara 84 kafin ya bar duniya.

Yankin ya fi kowane wuri a Burtaniya tunkaho da cewa mutane sun fi tsawon rayuwa a cikinsa.

To yayin da wannan yanki yake tunkahon zama na daya wurin samun rayuwa mai tsawo a Burtaniya ita kuwa unguwar Calton wadda ke da tazarar kilomita daya daga birnin Glasgow kusan sabanin hakan ake samu a can, domin yaran da aka haifa suka tashi a can ba a sa ran za su wuce shekara 54 a duniya.

Wato dai rayuwa a wannan yanki na babban birnin na yankin Scotland a Burtaniyan har ma ta fi muni a kan rayuwa a Pyongyang ta Koriya ta Arewa inda rayuwar maza ta kan kai shekara 71 ko kuma ma Iraki mai tsawon rayuwar sheakara 67.

Duk da cewa mata sun fi tsawon rayuwa to amma duk da haka wannan bambanci yana nan kuma sosai, domin yarinyar da aka haifa kuma ta tashi a yankin na Calton tsawon shekara 74 ake sa ran za ta iya kaiwa, yayin da takwarorinta na yankin Kensington and Chelsea za su iya kaiwa shekara 87.

Hakkin mallakar hoto dougie wallace institute
Image caption Yana shammatar mutane ne ya dauki hoton kuma kafin su farga ya sulale

Mai daukar hoto Dougie Wallace wanda ake kira da suna Glasweegee ya girma ne a abin da ya ke kira dakunan Galsgow.

Shi dai mutum ne da ke da sha'awar daukar hotuna na mutane a yanayin da ba sa tsammani na kafin su farga.

Zai je kusa da mutane kyamara a hannu daya fitilar kyamarar (flasha) a hannu daya ya gaishe su girma-girma, kafin su san ma me ya faru har ya yi gaba.

A shekara daya da ta wuce ya yi ta amfani da wannan dabara wajen daukar hotuna a wadannan wurare biyu wato yankin Kensington and Chelsea a Landan da kuma can garinsa Glasgow (Calton).

Yana daukar wadannan hotuna ne a wannan lokaci domin ya gano abin da ya sa rayuwa a wasu wurare na Glasgow har ma ta fi muni ga lafiyar mutum fiye da a fagen yaki.

Kuma mai zai sa a ce a wani yankin kuma da ke da nisan kilomita 644 kawai daga wannan wuri rayuwa ta fi ta can tsawo, kuma ba ma tsawo kawai ba ta ma fi abubuwa da dama.

''Bambancinsu ba kawai ya tsaya ba ne a tsawon shekarun rayuwa, a'a abin ya wuce haka,'' in ji Wallace kan bambancin mutanen Kensington da Glasgow.

Ya ce, '' hatta yanayin kyawun dinkin tufafinsu da kayayyakin ado da za ka ga sun sa da yadda matansu suke kwalliya, kai hatta yanayin fuskarsu idan ka gani akwai bambanci.''

Hakkin mallakar hoto dougie wallace institute
Image caption Dougie Wallace ya shammaci wata tsohuwa a yankin attajirai na Kensington and Chelsea a Landan

Al'amarin Calton daban yake, in ji shi. To amma abu ne sananne daman a game da tarihin yankin domin daman unguwa ce ko kauye da aka na leburori da sauran ma'aikata a zamanin bunkasar masana'antu.

To yanzu kamar yadda alkaluman hukumomin yankin suka nuna sama da kashi 40 cikin dari na mutanen da suke iya aiki 17,982 a yankin ba su da abin yi.

Fiye da al'ummar kowa ne yanki a Burtaniya mutanen Calton da dama na iya kashe kansu ko su fada hannun miyagun bata-gari ko kuma su mutu sakamakon wani lamari da ke da nasaba da shan barasa.

Sama da kashi 50 cikin dari suna shan taba. Shagunan abincin tafi-da-gidanka da gidajen giya da na caca da kamfanoni masu bayar da bashi da ruwa mai yawa duk ga sunan birjik a titunan garin.

Wallace ya ce,'' za ka ga illar da ke tattare da wannan koma-baya a zahiri ajikin mutane''

''Mutane suna saurin tsufa. Za ka gan su duk fuska ta tauye fata ta yi yaushi, hakora sun zube, a hotunan mutanen da na dauka. Yara sun yi teba.''

Lokacin da ya dauki hoton mutane a wani jirgin kasa da yake wucewa ta Hackney a Landan, Wallace ya ce ba shi da tabbas a kan irin mutanen da zai gani a hotunan.

''Amma a Glasgow abin ba haka yake ba, ya ce. Can za ka ga fuskoki cikin damuwa da wahala da fatar da talauci.''

Duk da dangantakar da yake da ita da damuwa kan mutane da kuma al'adar da ya taso a cikinta, Wallace ya ce shi kansa ya baiwa kansa mamaki lokacin da ya fara daukar hotunan yankin Knightsbridge.

Hakkin mallakar hoto dougie wallace institute
Image caption Wani fasinjan bas a Calton

Ya mayar da hankalinsa ne a wurin da ya kira Harrodsburg, inda babban kantin kayan masarufin nan na masu hali Harrods yake da sauran wurare na masu wadata suke kamar dandalin Sloane Square da kuma otal din Ritz a Piccadilly.

Daga nan ya gano cewa yana son kare wadancan mutanen da suke cikin waccan rayuwa ta al'ada daga sabuwar rayuwa ta zamani.

''Hotunana sai suka zama abin bayyana rayuwar bushasha ta manyan duniya da suka mayar da birnin Landan kudin ajiye na asusun duniya na ko-ta-kwana'' in ji shi.

Da yawa daga irin mutanen yankin Kensington and Chelsea wadanda Wallace yake daukar hotonsu ba tare da sun sani ba '' 'yan Burtaniya ne da aka fi gani masu hali,'' ya ce, wadanda za ka ga wasu tsofaffin mata ne masu kudi da maza da suka ci ado da 'yan mata ''da suka yi kwalliya kamar gimbiyar Oxford''.

Hakkin mallakar hoto dougie wallace institute
Image caption Wallace ya dauki hotunan ire-iren yawancin mutanen Landan masu hali

Yana kuma daukar hoton attajiran baki na yankin, wadanda suka zuba jarinsu a yankin daga kasashen waje, wadanda watakila sun dawo Landan da zama ko kuma ba su dawo ba.

Hatta a shekara ta 2012 lokacin da tattalin arzikin Burtaniya ya gamu da matsala, Wallace ya ce an kashe tsabar kudi har fam miliyan dubu 83 a kan harkar gidaje a Landan.

A yankin Kensington and Chelsea inda yawanci kudin sayen gida ya kan kai fam miliyan 2.29, kashi 75 na sabbin masu sayen gidaje 'yan kasashen waje ne, kuma kashi 40 cikin dari na gidajen ba kowa a cikinsu a yawancin watannin shekarar.

Hakkin mallakar hoto dougie wallace institute

A Harrodsburg, Wallace ya dauki hotunan samari cikin motocin alfarma ''samfurin Bugatti masu kyale-kyalen gwal da dutsinan ado na Swarovski, a jikinsu,'' da mata kuma suna fama da jakunkunan hannu masu tsadar gaske wadanda sun ma yi musu nauyi a hannu.

Bayan wannan ma ga kuma lokacin sayayyar azumi da ake kira Ramadan Rush na lokacin bikin Sallar Idi.

Wadannan hotuna ya ce, sheda ce, ''ta sauyin da birninmu yake samu.'' Kuma ba sauyi ba ne da ke yaduwa a kowa ne bangare na Burtaniya.

''Ka je Glasgow ka ce wa mutane Burtaniya na sake bunkasa,'' in ji Wallace. ''Za ka ji yadda za a yi maka ihu ( gwalewa).''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Photographing Britain's life expectancy gap