Hanyar bunkasa haddarka

Hakkin mallakar hoto Getty

Wace hanya ce ta fi sauki wajen koyo? David Robson ya hadu da wasu masana kimiyya da gwanayen hadda da suke fafatawa domin gano dabarun hadda da sauri.

Ga bayanin da ya hada rubuta mana.

A lokacin da na hadu da manyan masana hadda na duniya sai na ji dadi da da kuma daukaka.

Ben Whatley misali ya ba ni labarin sanannen mahaddacin nan Matteo Ricci mai bisharar katolika na karni na 16, wanda shi ne dan Yammacin duniya na farko da ya yi babbar jarrabar aikin gwamnatin China.

Jarrabawar na da wahala sosai, domin ta kunshi hadda da tilawar wasu baituka na wakokin Sin na asali, wanda wannan aiki ne ja da zai dauke ka tsawon rayuwa.

''Kashi daya cikin dari ne na wadanda suka yi jarrabawara suke ci, amma duk da haka Ricci ya yi nasara bayan shekara 10, duk da cewa bai taba iya harshen Sinanci ba kafin wannan lokaci.''

Ko kimiyyar sanin tunanin dan-adam za ta iya gano mana hanyar sarrafa zuciyarmu?

Burin Whatley kenan. Tare da hadin gwiwar tsohon zakaran hadda Ed Cooke, tuni ya tsara wata manhajar koyon hadda da ya sa mata suna Memrise da Ingilishi.

A yanzu kuma sun hadu ne da masu bincike daga Kwalejin Jami'ar Landan domin yin wata gasa da za ta kai ga samo hanyar da ta fi dacewa wajen bunkasa dabarunsu na hadda.

A taron an bukaci kwararrun masana hadda na duniya da su jarraba hanyoyin da za su samo hanyoyi mafiya sauki da kuma tasiri wajen haddace sabbin bayanai ko ilimi.

A kan haka ne na halarci taron donin ganin yadda za a yi zagayen farko na tantance wadanda suka fi.

Gasar ta bayyana hanyoyi masu ban sha'awa na ganin yadda kwakwalwarmu take aiki.

Ko kai dalibin jami'a ne da ka dukufa hadda domin jarrabawarka ta karshe ko kuma kana kokarin koyon harshen Faransanci ne domin yawon bude idanu za ka samu sauki ta hanyoyin da suka gano.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ko sabbin dabaru za su iya saukake wahalar koyo

Jarrabawar mai sauki ci idan ka kalle ta a haka in ji Rosalind Potts ta Kwalejin Jami'ar Landan wato UCL.

''Muna son mu san idan a sati daya kana nazarin wasu kalmomi 80 ta yaya za ka haddace su ka yi tilawarsu bayan mako daya.''

Karin kalubalen aikin ma shi ne dukkanin kalmomin 80 na harshen Lithuania ne.

Duk da cewa akwai manyan masana kimiyya na duniya da suka shiga gasar, wasu dabarun ba su yi wani tasiri ba.

''Wannan ya nuna yadda yake da wuya a yi amfani da hanyoyin kimiyya a harkar koyarwa ta gaske,'' inji David Shanks shi ma daga UCL din.

Zaman da zai gunduri mutum misali yana daya daga cikin matsalolin gasar.

An samu wani da barci ya dauke a yayin zamn sa'a dayar na hadda, duk da cewa an biya su da 'yan kayayyakin ciye-ciye domin su shiga jarrabawar.

''Hakan na faruwa,'' in ji Yana Weinstein daga Jami'ar Massachusetts ta Lowell wadda ita ma tana cikin alkalan gasar.

Ba tare da la'akari da wadannan 'yan matsaloli ba ayari da dama daga cikin wadanda suka yi jarrabawara sun karu, domin sun iya linka akalla yawan abin da a da suke iya hadda ce wa.

Maimakon mayar da hankali a kan hanya ko dabara daya, sai suka hada wadannan hanyoyin ko dabaru wuri daya:

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Idan ka fadi jarrabawa sau daya za ka fi tunawa a gaba

1) Yarda da rashin sani. Jarraba kanka na daya daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen bunkasa hadda.

Ni a ganina hanyar da ta fi ban mamaki da kuma amfani a wannan dabara ita ce, wadda za ta tilasta wa dalibai su yi hasashen ma'anar kalmomin na harshen Lithuania.

''Ba shakka za su fadi a karon farko,'' in ji Shanks, amma duk da haka bincike ya nuna cewa kuskuren farko a gaba yana sa a iya hadda ce kalmomin. ''Hakan ya fi tasiri kan a ce ka taba nazarin kalmar.''

Sanin jahilcinka kadai, ga alama yana sa zuciyarka ta tashi tsaye ta ga ba ka sake jin wannan kunya ba, wanda hakan ya sa kokarinka na hadda ya linka idan aka kwatanta da ayarin wadanda ba su gwada dabarar ba.

Wannan ya zo kusan daidai ko kari a kanilimin tunanin dan-adam na idan abu ya kasance mai wahala kadan,zai sa ka mayar da hankali sosai a kansa domin gaba ( kar ka kasa yinsa).

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Kana bukatar jarraba yawan abin da kwakwalwarka za ta iya dauka

2) Dabarun kai-kawo a dandalin haddar. Za ka iya bata lokaci cikin sauki ta hanyar yawan nazari A kan haka da yawa daga cikin wadanda suka shiga gasar suka tsara dabarun sanin yadda ka fi tuna kowacce daga cikin kalmomin 80, yadda da zarar ka fara mantawa sai ka bi wannan dabara ka tuna.

Manhajar 'memrise' na da daya daga cikin wannan dabara da za ka iya amfani da ita ya zuwa yanzu. Za kuma ka iya dogaro a kan zuciya ko tunaninka (sai lokacin da zuciya ta raya maka) ka tsara lokacin koyonka, ka dauki tsawon lokaci kafin ka rika jarraba haddar taka kana gyra kura-kuranka.

Wani daga cikin masu gasar shi kuwa ya jarraba dabarar bayar da hutu ne na dan lokaci ga masu yin jarrabawar a lokacin haddar kalmomin, inda yake ba su damar kallon wani hoton bidiyo na wurin da ruwan kogi ke zubowa daga sama, a takaice domin sanya bayanin ya nitse.

Idan kana nazari abu ne mai amfani ka rika daukar dan lokaci kana hutawa domin wannan wahalar zama ka da ta fi karfin iya damar da jikinka ke da ita ta yin abu.

3) Nazarin kashi kashi. Za ka ji kamar ka rarraba abubuwan zuwa gida-gida ka rika koyonsu daya bayan daya.

Saboda haka ne wani daga cikin ayarin ya tsara kalmomin zuwa gida-gida.

Amma kuma wani ayarin daban ya ga cewa kawai ya kewaye kowacce kalma da tawada ya fi tasiri wajen haddace su.

Whatley ta nuna cewa gwanayen hadda da suke haddace takardun karta wannan dabarar su ma suke yi, sai su rika juya wa cikin sauri, maimakon bin su gida-gida suna nazari.

Idan ba ka gane wanna tsarin ba, to bincike ya nuna cewa za ka iya amfani da dabaru daban-daban wajen nazarinka. Ya fi dacewa ka dauki lokaci kana nazarin darussa da ilimi da dama maimakon ka mayar da hankali a kan darasi daya kawai. Ka kalli abin ta fuskar cin abinci daban-daban maimakon abinci daya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cakuda darussan da kake nazari na da amfani

4) Bayar da labari. Duk wata dabara ta bayyana yadda abu yake za ta iya taimakawa wajen hadda.

Wani daga cikin masanan ya bukaci daliban da su kirkiri labari da kalmomin da suke koyo.

Cooke da Whatley sun ji dadin yadda suka ga wani ayari ya yi dabarar danganta kalmomin da wasu abubuwa a dakin.

A tsarin da suka yi za a iya nuna maka daki a danganta kalmar 'lova' da gado. Daga nan za ka iya tunanin matarka tana kwance a kan gado.

Da zarar ka tsara karatunka ta wannan hanya za ka iya tuna tsarin da kake bi ka tuna duk wata kalma ba tare da wata wahala ba.

Wannan ita ce dabarar da mai bishara Matteo Ricci ya yi amfani da ita ya koyi harshen sinanci sosai, haka kuma ta haka Ed Cooke ya iya haddace lambobi bibbiyu har guda 2265 a kasa da minti 30.

Tsarin kwamfuta na ayarin da ya bullo da wannan dabara zai iya saukaka hanyar. '' Idan wannan ya zama zakara a gasar, zai zama wani babban abu mai muhimmanci da aka gano,'' in ji Cooke.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Danganta abubuwa na zahiri da kuma na almara kan iya bunkasa hadda

A wasu ayyukan na baya na yi amfani da dabarar haddace abubuwa wajen koyon wasu kalmomi 1000 na harshen Denmark.

Duk da cewa ta taimaka mini haddace kalmomin amma hakan ba I sa na iya amfani da kalmomin ba a yayin tattaunawa ta yadda za su iya zuwa min a lokacin da nake bukatar amfani da su, a jirgin sama ko a wurin cin abinci.

Cooke ya yarda da cewa ai hakan matakin farko ne. ''Da dama daga ire-iren wadan nan abubuwa ne da nake kira matakin sabo yayin da kakr kokarin haddace su,'' in ji shi.

Yunkuri ne kalmar tana nan muddin dai kana bukatarta.''

Ya ce wannan mataki mai amfani sosai da za a iya amfani da shi wajen koyon abubuwan da ba ma harshe ba kadai kamar lissafi da tarihi da sauransu.

Bayan da aka zabi ayari biyar daga cikin wadanda suka halarci gasar, yanzu suna kokarin sanya dabarun a shafin intanet manhajar Memrise.

Wannan zai ba su damar zabar dabarar da ta zamo ta daya da za a ba wa masu ita kyautar dala 10,000.

Dalilin sanya su a wannan manhaja shi ne domin inganta ita kanta manhajar da sabbin dabaru.

Su kuwa Potts da Shanks hakan zai taimaka musu sanin hadakar dabarun da za su fi amfani a rayuwa ta yau da kullum wajen koyo.

Alkalan gasar na fatan gudanar da ita kowace shekara domin samarwa da kuma inganta dabarun haddar ilimi.

Babban kalubalen wadannan kwararrun masana kan hadda ba kawai su saukaka hanyar koyo ba ne kawai.

Kamar yadda kowa ne dalibi ya sani babban abin da ke kawo cikas ga koyo shi ne dauke hankali.

Muna bukatar karin tarin wasu gasannin kafin mu shawo kan wannan matsala.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How to supercharge the way you learn