Ko akwai illa ka boye bacin ranka?

Hakkin mallakar hoto spl

Kana cikin bacin rai? Ka da ka gimtse abin a ranka, fito da shi fili, ka da ka bar shi a zuciyarka, ka gane?

Kamar yadda Claudia Hammond ta gano, shedar na da sarkakiya sosai.

Sau nawa kake jin shawarar cewa ka da ka bar wani abu na bacin rai ya yi ta kona maka zuciya domin amfanin lafiyarka?

Akwai maganar da ke cewa barin abu a zuciyarka ya yi ta damunka, illa ce ga lafiyarka, ko kuma akalla zai iya jawo maka cutar gywambon ciki.

Daga lokaci zuwa lokaci kana karanta rahotannin da ke cewa hakan zai iya zama illa ga zuciyarka.

Amma idan ka duba irin tarin shedar da aka samu a tsawon shekaru, me hakan ke bayyanawa a kan danne zuciyarka?

Game da gyambon ciki, ko ka yi ta tafarfasa a daki ko kuma ka yi ta dahuwa cikin ruwan sanyi, duk da haka za ka iya samun cutar.

Yayin da ake tunanin damuwa ita ce babbar matsalar da ke haddasa gyambon ciki, babu wata sheda karara da ke nuna ya dogara kan ka bayyana damuwarka ko ba ka bayyana ba, domin yanzu an san yawancin cutar kwayar cutar baktiriya ce (heliobacter pylori) ko yawan amfani da wasu magungunan zafin kirji ne ke haifar da gyambon.

Idan ana maganar zuciya ne shedar ta zama daban-daban.

A wani nazari da aka yi a jami'ar North Carolina a shekara ta 2000, an bai wa marassa lafiya 13,000 takardun tambayoyi, inda a ciki suka bayyana yanayin abin da zai iya kai su ga bacin rai, kuma aka bi diddiginsu bayan 'yan shekaru.

Ko da yake bugun jininsu (BP) ba shi da wata matsala, wadanda suka bayyana cewa suna da saurin zuciya ko bacin rai a kai a kai, suna da hadarin kamuwa da cutar bugun zuciya linki uku a cikin 'yan shekarun fiye da sauran marassa lafiyar, ko da kuwa an yi la'akari da wasu abubuwan kamar shan taba da cutar sukari da teba

Haka kuma, Mark McDermott na jami'ar East London ya gano cewa mutanen da suke bayyana bacin ransu sun fi gamuwa da cutar zuciya a kan wadanda suke yin gum.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Wasu rahotanni sun nuna cewa barin damuwarka a rai na iya illa ga zuciyarka
Bayyana kanka

Ana ganin wannan duka abu ne da zai iya tabbata, musamman ganin cewa akwai hanyoyin bayyana bacin rai da za su iya zama matsala.

Idan ranka ya baci,fuskarka za ta yi ja (amma bature), za ka ciccije baki kuma zuciyarka za ta yi ta bugawa kana shirin fada ko guduwa.

Jikinka zai yi shiri ta hanyar kwaso sinadarin maiko daga wasu jijiyoyinka ko da kana bukatar karin karfi.

Sai dai kuma idan ba ka yi fadan ba wannan maikon zai kwanta a hanyoyin da jini ke bi daga zuciya, wanda kuma hakan zai iya haifar da ciwon zuciya.

A duk lokacin da bugun zuciyarka ya karu wata tsokar jikinka za ta iya samun 'yan raunuka a bangon jikin jijiyoyinka da jini ke bi daga zuciya, wanda shi ma kuma ai iya haifar da cutar zuciya.

A haka wannan dan rauni da ke samun bangon jijiyoyin da jini ke bi daga zuciya ba wani abu ba ne, amma idan ya ci gaba da faruwa yau da kullum, illarsa za ta yi yawa.

Zuciyar da take da cikakkiyar lafiya za ta iya maganin wannan, amma idan daman mutum yana da ciwon zuciya, a wani lokaci, karuwar bugun zuciyar da ke iya samuwa kwatasam, zai iya sa maiko ya kakkama jikin jijiyoyin da jini ke bi daga zuciya har ma ya iya toshe hanyar.

Idan hakan ya hana jini zuwa zuciya abin da zai faru shi ne zuciyar sai ta buga, idan jini bai je kwakwalwa ba kuma sai mutum ya gamu da cutar mutuwar jiki.

Sai dai sauran wasu nazarce-nazarce da aka yi ba su nuna wata alaka tsakanin bacin rai da cutar zuciya ba.

Ko kuma cewa mutanen da suke da cutar bugun jini ga alama sun fi iya danne zuciyarsu.

Matsalar ita ce bincike ya auna cutar zuciya da kuma bayyana bacin rai ta hanyoyi masu yawa daban-daban, wanda abu ne mai wuya a iya kwatanta su.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Raunin da ke da nasaba da bugun jini a jikin jijiyoyin kai jini na iya haddasa cutar zuciya

A kokarinsa na gano yadda lamarin yake Farfesa Giora Keinan daga Isra'ila ya duba ba yadda mutane suke yawan samun bacin rai ba kadai har da tsanani ko girman bacin ran.

Masanin ya gano cewa abin da ya fi kyau ka yi domin lafiyarka shi ne, ranka ya baci sosai, ka nuna bacin ran naka da kuma damuwa karara, amma kuma ya kasance a wani lokaci ne kawai za ka yi hakan.

Ya nuna cewa mutanen da suke yin wannan, su ne wadanda za su iya kasancewa kuma sun iya samun wata hanya ta magance damuwarsu.

Wannan zai rage yawan damuwar da suke gamuwa da ita kuma hakan zai inganta garkuwar jikinsu, abin da kuma zai kai ga bunkasar lafiyarsu.

Wata hanyar kuma ita ce komai ya danganta ga yadda ka bayyana bacin ranka.

A wani nazari da aka yi a Canada, an zabi magidanta 785, kuma aka rika bibbiyarsu har tsawon shekara goma.

A nazarin an gano cewa mazan da suke bayyana damuwarsu ta hanyar da ya kamata (cikin natsuwa), inda suke amfani da ita domin su ga an yi abin da suke so, da wuya su gamu da ciwon zuciya.

Haka ma kuma a cikin mata abin haka yake ba bambanci.

Amma kuma a cikin maza ko matan, dabi'ar nuna bacin rai ta hanyar dora laifi a kan wani ko wasu, kuma mutuma ya kafe cewa hakan da ya yi daidai ne, to yana kara haifar da ciwon zuciya.

Shirin fada

Ko da ba a kammala nazarce-nazarce ba kan cewa ran mutum ya baci abu ne mai amfani ga jikinmu ba, ba shakka bayyana wannan bacin rai naka zai ba ka wani dan sauki, ba haka ba ne? Watakila ba zai ba ka ba.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Wannan zai taimaka wajen kawar da bacin rai, haka ne?

Wasu masu masanan sukan ba wa mutum matashin kai ya nausa, amma kuma ba a ko da yaushe ba ne hakan yake da wani amfani kamar yadda ake dauka ba.

A gaskiya ma zai iya kara maka bacin ran ne.

A wani nazari, wasu mutane da suka rubuta wata kasida, sun sha suka da cin mutunci, wanda ya hada da wani da ke cewa, ''wannan ce kasida mafi muni da na taba karantawa''.

Daga nan sai aka ba rabin mutanen damar su huce takaicinsu ta hanyar naushin wani buhu (irin na atisayen damben zamani).

Suka ce sun ji dadin yin hakan, amma kuma da aka ba su damar su yi wa abokin hamayyarsu surutai a wani bangaren gwajin kuma sun kuntatawa mutanen da hayaniya fiye da yadda 'yan daya rukunin suka yi.

Wannan ya nuna kenan wancan bugun buhun da suka yi ta yi bai sa zuciyarsu ta yi sanyi ba sai dai ma kara tunzura su abin ya yi.

Haka kuma wadannan dai masu binciken suka sa mutane suka dauka cewa an ba su wata kwaya wadda za ta dakatar musu da bacin rai tsawon sa'a daya.

Bayan da aka bata musu hankali 'yan kadan ne suka damu su naushi wannan buhu, abin da ke nuna cewa, muna yin wadannan abubuwan ne saboda mun yi imanin cewa zai sa mu huce, duk da cewa kuwa ba lalle ba ne.

To me duka wannan yake nuna mana? Kawai yana nuna mana cewa ka zauna da bacin rai a zuciyarka, hakan ba wata illa yake maka ba sosai, kuma fadan (surutai) da kake yi wani lokaci kila yana da amfani, kuma maganar ba wai ta cewa kana dam uwa ba ne abin ji, a'a, abin jin shi ne yadda ran naka yake baci da kuma yawan lokacin da yake baci.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is it bad to bottle up your anger?