Hatta barayi na bin layi a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto Cultura RM Alamy

Jira a layi kusan abu ne da ke bata wa mutane rai a duniya baki daya, amma bincike ya nuna cewa yanayin yadda muke daukar layi ya danganta ne ga tsarin layin da dalilinsa da kuma inda muka fito.

Brendan Cole ya bincika mana

Ko a filin wasa na Wimbledon ne ko kuma a tashar jirgin kasa ta Waterloo mutanen Biritaniya sun yi fice wajen kokarin kafa layi da binsa kan ka'ida.

Hatta a lokacin tarzomar Lanadan ta shekara ta 2011, masu fasakantuna da wawashe kayan mutane sun rika bin layi a duk inda za su kwashi kaya.

''Daya daga cikin fitattun hotunana da na fi so an dauke shi ne a lokacin tarzomar Landan inda wasu masu wawashe kayan mutane suka yi layi a kofar wani kanti.

Kusan su 13 mazansu da mata, suka yi a waje, daya ya shiga ya gama debo abin da yake so ya fito wani kuma ya shiga, in ji Richard Larson farfesa a makarantar fasaha ta Massachusetts ( Massachusetts Institute of Technology).

Saboda yadda ya mayar da hanakali kan bincike kan bin layi abokan aikinsa malamai suke yi masa lakabi da Dakta layi.

Farfesa Larson ya ce, ''ba zan iya tunanin wani wuri in ba Landan ba inda za a ce masu wawason kayan mutane su zama wayayyun da har za su bi layi daya bayan daya suna shiga kanti diban kayan da ba nasu ba.''

Ba Larson ne kadai ba wajen ayyana 'yan Biritaniya a matsayin mutanen da suka fi yi layi cikin natsuwa a duniya.

Marubuci George Mike ya ce, ''Mutumin Ingila ko da shi kadai ne yakan kafa layi mai kyau na mutum daya.''

A kasidarsa mai suna 'The English People, George Owell ya rubuta cewa bako zai yi matukar mamaki idan ya ga yadda mutane suke kafa layi.

Ita ma a littafinta mai suna 'watching the English' marubuciya Kate Fox ta rubuta yadda mutanen Ingila suke nuna natsuwa idan suna bin layi.

Yawanci mutanen Biritaniya suna shafe shekara daya da sati biyu da kuma kwana daya na rayuwarsu a kan bin layi a kanti da kuma shekara daya da wata uku a layin ababan hawa.

Hakkin mallakar hoto Colin UnderhillAlamy
Image caption George Owell ya yi magana kan yadda mutanen Biritaniya suke son kafa layi a wata kasida da ya rubuta

Amma za ka iya gane inda mutum ya fito daga yanayin bin layinsa? Kuma mai ya sa wasu layukan a duniya kamar ba sa tafiya, wasu kuma suke tafiya da sauri duk kuwa da cewa kusan lokacin jiransu daya ne.

Larson da wasu da da yawa daga cikin masana kimiyyar zamantakewar mutane, sun yi amanna cewa daga yadda kake bin layi za a iya gane kai mutumin ina ne.

Farfesan ya ce a Amurka, yadda mutane suke bin layi kusan ya dogara ne ga birnin da mutum ya fito.

Ya ce, ''daya daga cikin abubuwan da na gano shi ne, za ka iya fahimtar abubuwa da yawa na al'adar mutum daga nazarin wasu 'yan dabi'unsa yayin da yake kan layi.''

Mutanen Boston da New York da kuma na Washington DC kowanensu na da yadda suke bin layi, in ji masanin.

''A Washington mutane sukan bi layi a jijjirgge a gefen titi, domin ma'aiakatan gwamnati ne wadanda suka san motar safa da ke daukarsu tana tsayawa a wurin da karfe 4:05 na asuba, saboda haka suke bin layi a tsanake.

Amma ban taba ganin irin wannan dabi'a ba a New York da Boston.''

Farfesa Joe Moran, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar John Moores ta Liverpool kuma marubucin littafin koyar da bin layi mai suna 'queuing for Beginners: The Story of Daily Life from Breakfast to Bedtime' ya ce Birtaniya ta samu wannan dabi'a ta bin layi ne a lokacin karancin kayan masarufi da sauran abubuwa na amfanin jama'a a shekarun 1940.

''Biritaniya na alfahari da wannan dabi'a ta mutanenta ta bin layi cikin natsuwa kuma tana jin dadin hakan.

Amma kuma shi layi ba abu ne mai dorewa ba, kuma maganar yadda za a ce kana bin layi da kyau ko natsuwa a layi abu ne da ya danganta da yadda kake daukar natsuwa. Domin halayyar wani a kan layi ita ce aidai din wani,'' marubucin ya ce.

Duk yadda masu bin layi suke da natsuwa, ko da yake masana kimiyya sun yarda cewa, idan har ana son layi ya yi amfani, sai an yi adalci.

In dai har za a bi ka'ida wajen sauraron mutane bisa yadda suke kan layi, wato a fara halartar wanda ya riga zuwa kafin na bayansa, to lalle kam ba za a samu hatsaniya ba.

Wannan shi ne dalilin da ya sa ake yin dogon layi daya a bayan igiya ko wani shinge, inda idan ka kai gaba, za a tura ka wajen wanda zai saurareka.

Ba wai wannan tsarin ya fi, wanda za a yi layuka daban-daban ba ne a gaban mutanen da suke saurarenku ba ko biya muku bukatarku ba, amma dai yana hana wanda ka riga zuwa ya riga ka samun biyan bukata.

Hakkin mallakar hoto Richard WaymanAlamy
Image caption Layuka irin wadannan a tsakanin shingea filin jirgin sama na Dublin na sa mutane jin dadi saboda ba za saurari wanda ka riga zuwa ba

Yana daya daga cikin manyan abubuwan da masana harkar layi suka ce dole a kawar idan ana son wadanda suke tsaye a layi su dan ji dadi.

Mun tsani mu ji abu ya gundure mu, ko mu ga cewa za mu dade fiye da yadda muke tsammani, balle ma kuma a ce wani ya zo kawai ya shiga gabanmu.

Za a iya maganin damuwa ko gundurar da mutane kan ji idan suna kan layi cikin sauki.

Korafin da mutane suke yi na dadewa suna jiran lifta (lift) a dogayen benaye a tsakiyar karni na 20 a New York ya sa aka sanya mudubi a wuraren jiran.

Za ka ga mutane suna amfani da su wajen gyara gashinsu ko kuma su ga wanda suke bayansu. Daga nan aka daina korafi kan jiran.

Idan har za ka samu wani abu kana yi a lokacin da kake jiran liftar ba za ka ji ma ka dade kana jira ba.

Yanayin yadda layin ya zo kanka shi ma yana da amfani, domin binciken da malamin makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta INSEAD, farfesa Ziv Carmon da kuma farfesa Daniel Kahneman na jami'ar Princeton suka yi, sun gano cewa idan a karshe ka ji dadin yadda ka kare layin, misali idan bayan korafi da surutun duk da ka rinka yi a karshe ya yi sauri za mu ji dadi ko da kuwa a yawancin lokacin mun kagu ko mun damu.

Abin da ke haifar da dogon layi misali shi ne, ''wurin ganin likita wasu mutanen za su shiga su fito da wuri, wasu kuma za a dauki tsawon lokaci ana duba su.

Saboda haka abin da za a iya gamawa cikin minti 15 sai ya kasance ya dauki sa'a daya.

To babban abin da ke haddasa layi shi ne yanayin yadda babu wani lokaci takamaimai na zuwa da kuma rashin tabbas na tsawon lokacin da za a dauka na sauraren mutum, '' in ji Larson.

A Landan a wurin karshen watan Satumba, an yi wani dogon layi a kofar kantin Apple na titin Regent, layin da ya dauki tsawon kwanaki a lokacin da za a kaddamar da sabuwar wayar iPhone 6S.

Ba layi ne na mutanen Biritaniya ba kadai, domin ya kunshi mutane daga sassan duniya daban-daban.

Wasu daga cikin mutanen suna cikin farin ciki ba su damu da wannan dogon jira ba.

Wani abu kenan game da layin da bai zama dole ba, wanda ya shafi zamani.

''Layuka na al'amuranmu na yau da kullum (na dole) suna damunmu, amma layin da ya shafi wani abu na nishadi ko jin dadinmu kawai ba ya damunmu.

Ka yi layi a kantin kamfanin sayar da wayar Apple ko kuma domin sayen tikitin shiga taron wake-wake abu ne na nishadi, wanda za ka iya yin alfahari da shi. Ba layuka ba ne na damuwa,'' in ji Larson.

Hakkin mallakar hoto age fotostockAlamy
Image caption Masu yawon bude idanu na jiran shiga wurin hasumiyar Eiffel Tower ta Paris

Wani bangare kuma na daban game da bin layi shi ne, a wani lokacin dogon layi yana damunmu. Ba don haka ba yana karfafa mana gwiwa mu bi.

''Idan layi dogo ne za ka ga ba ka son ka bi shi. Amma kashi kadan na wasu layukan masu tsawo, kamar na karancin kudi a Girka, tsawonsu yana kara sanya mu mu bi,'' in ji Larson.

Moran yana ganin layi a matsayin alama ta wani abu da mutane suke ba wa muhimmanci kuma a matsayin wata hanya ta ririta wani abin da ake karanci.

''A lokacin yakin duniya na biyu, lokacin da mutane suke bin layi domin samin man fetur da abinci, za ka ga sun bi layi ma ba tare da sanin layin menene ba.

Kawai sun dauka cewa idan dai ana bin layi to lalle akwai wani abu mai muhimmanci a can karshensa. Wannan alama ce da ke nuna yanayin tunanin mutane karara.

''Ga gangami, kuma kai kana ganin za a yi ba kai.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why we hate some queues more than others