Mutum mai zuciya biyu

Hakkin mallakar hoto Getty

Lokacin da aka sanya wa mutum wata sabuwar zuciya, sai tunaninsa ya sauya ta wasu hanyoyi. Me ya sa?

Amsar ta bayyana abu mai ban mamaki game da jikinmu in ji David Robson.

Duk dakika daya ko sama da haka Carlos zai ji wani dan tudu ya bigi cikinsa daga ciki. Wannan shi ne bugun abin da za a iya kira zuciyarsa ta biyu.

Wannan abin da ke zaman kamar zuciyarsa ta biyu, 'yar wata na'ura ce aka sanya masa a ciki domin ta rika taimaka wa wajen gudanar da aikin da zuciyarsa wadda ke da matsala, take yi, amma kuma Carlos (ba sunansa na gaskiya ba) ba ya jin dadin wannan motsi da na'urar ke yi.

Yana jin bugun da na'urar take yi kamar ya maye bugun zuciyarsa, yanayin da yake ji ya sauya yadda fasalin jikinsa yake, domin na'urar ta dan nuna alamun tudunta ne daga saman cibiyarsa, abin da ya sa yake jin kamar kirjinsa ya dawo kasa.

Wannan motsi ko bugu da Carlos yake ji na na'urar,wani abu ne na daban maras dadi kamar yadda yake ji domin bai saba da shi ba.

Amma lokacin da masani a kan kimiyyar motsin jiki (neuroscientist) Agustin Ibanez ya gamu da Carlos, ya duba shi, sai yake ganin akwai wasu abubuwan ma na daban da suka fi wannan motsi, da za su biyo baya, a jikin na Carlos.

Ibanez yana ganin sauya zuciyar mutumin da likitoci suka yi kamar sun sauya zuciyarsa ta tunani ne, domin yanzu yadda Carlos yake tunani da jin yadda abu yake da yadda yake yin abubuwa sun saba da yadda yake a da, sakamakon wannan na'ura da aka sanya masa a ciki.

Ya aka yi haka? Galibi mukan ce muna bin zuciyarmu, to amma su masana kimiyya sai a yanzu ne suka fara yarda da wannan magana.

Wannan dunkule na tsoka (zuciya) na taka rawa a yanayinmu da yadda muke tunani ta hanya ta sosai.

Abubuwa da yawa kama daga yadda kake jin tausayin wani idan wani abu ya same shi, da yadda kake tunani ko jin matarka na mu'amulla da wani namiji duka wadannan na farowa ne daga wannan tsoka da sauran jikinka.

To wannan mutumin da yake jin kamar yana da zuciya biyu, ya bai wa Dakta Ibanez wanda yake jami'ar Favaloro da ke Buenos Aires, dama ta musamman ya jarraba wadannan bayanai da muka yi game da aikin zuciya a tunanin mutum.

''CRANIAL STUFFING''

Aikin Ibanez ya gamu da tarin jita-jita kan rawar da zuciya ke takawa a tunani, domin ana ma ganin na zuciyar ya ma wuce na kwakwalwa.

Aristotle yana ganin babban aikin kwakwalwa shi ne ta kara armashin tunanin da ya taso daga zuciya, wadda ya dauka ita ce cibiyar ruhi.

A kan irin wadannan dalilan ne masu adana gawa a Masar a zamanin da, su ke tabbatar da ganin sun bar zuciya a kirji inda take, amma kuma su cire kwakwal daga kai.

Hakkin mallakar hoto spl

Yanzu kuma za mu kalli abin sosai ta bangaren aikin kwakwalwa ko da kuwa tunani ko batun ita zuciya ya cigaba da fuskantarmu. Ka duba irin yawan hanyoyin yadda muke bayyana ko kwatanta yanayinmu a yau.

William James, mutumin da ya samar da fannin ilimin tunanin dan adam kamar yadda muke da shi a yau, ya taimaka mana wajen daidaita wadannan tunani a karni na 19 ta hanyar nuna cewa yanayinmu (emotions) sakamako ne na sakon da ke kai-kawo tsakanin jikinmu da kwakwalwarmu.

Bisa nazariyya ko tunaninsa, kwakwalwa za ta iya tattara bayani kan barazana yadda ya dace, amma kuma saninmu da bugun zuciyarmu da tafin hannunmu da ke gumi shi ke fito da abin da yake ba a iya gani a zahiri a matsayin yanayinmu (emotion).

Fahimtar James ta kuma taso da wata tambaya mai muhimmanci, tambayar kuwa ita ce, idan yanayin sanin jikin kowa daban ne, shin wannan zai tsara yanayin abin da suke ciki ko suka shiga? Wannan abu ne da zai yi wuya a iya jarrabawa, amma masana kimiyya na shekara dari na gaba (wannan karni) yanzu sun dukufa kan wannan.

A nazarin an bukaci mutane da su kirga bugun zuciyarsu, daga yadda suke ji a kirjinsu kawai, ba tare da sun dora hannuwansu a kan kirjinsu ko jijiyar hannunsu ba domin sani.

Ka gwada haka kai kanka za ka fahimci cewa wannan abu ne mai wuyar gaske, domin mutum daya a cikin hudu zai kasa cin jarrabawar da kashi 50, wanda hakan ke nuna alamar cewa ba su san motsin da ke faruwa a cikin jikinsu ba; kashi daya bisa hudu ne kawai na mutanen suka yi nasarar sanin yawan bugun zuciyar tasu da kashi 80 bisa dari.

Bayan wannan jarrabawa ta sanin yawan bugun zuciyarsu, masanan sun kuma bai wa mutanen wata jarrabawar ta kwakwalwa (tunani).

Hakkin mallakar hoto Getty

Ta tabbata cewa James daidai ya ke. Mutanen da suke da masaniya sosai a game da jikinsu, sun fi nuna damuwa ko ji a jikinsu idan suka ga wasu hotuna masu tayar da hankali, sanna kuma sun fi iya bayyana yadda suke ji a game da wani abu.

Wani abu mafi muhimmanci kuma shi ne, su irin wadannan mutanen sun fi saurin gane yanayin wasu mutane daga fuskar mutanen, sannan kuma sun fi saurin kauce wa wata barazana, kamar jan wutar lantarki a dakin binciken kimiyya, watakila saboda wannan baiwa tasu ta jiki ta taru da yawa a cikin tunaninsu har take bayyana a duk abin da suke yi.

''Wannan sai ya yi saurin ba mu damar sanin amfani ko illar abu, ko zabin da za mu yi ko kuma abin da ya kamata mu yi a yanayin da muke ciki,'' in ji Daniella Furman ta jami'ar California da ke Berkeley.

Ma'anar wannan shi ne, mutanen da suke da masaniya sosai a game da jikinsu, sun fi bayyana yanayinsu na abin da ya faranta musu rai ko kuma ya bata musu rai a rayuwa.

''Ba lalle ba ne mu iya bayyana wata lama ta wani abu da ya dadada mana, amma kila za mu iya gane alamar abubuwan idan suka faru,'' in ji masaniyar.

Ma'aunin yanayin (emotion) mutum:

Wadannan alamu na jikinmu na sirri za kuma su iya kasancewa su ne ke sanar da mu wasu abubuwan da muke ji a tunaninmu (intuition), kamar yadda Barney Dunn na jami'ar Exeter ya nuna, bayan wani gwaji da ya yi wa wasu mutane na canke.

A gwajin, masanin ya bukaci mutanen da su zabi katuna (cards) daga gida hudu, kuma za su samu ladan kudi idan katin da mutum ya zaba ya yi daidai da wanda ya bayyana a fili.

Hakkin mallakar hoto Getty

An shirya abin ta yadda za ka iya yin nasara idan ka zabo daga gida biyu, kuma za ka fadi idan ka zabo daga sauran gida biyun.

Dunn ya gano cewa mutanen da suke iya sanin bugun zuciyarsu da kyau za su fi karkata wajen zabe daga wasu gidaje, yayin da su kuma wadanda ba sa iya tantance bugun zuciyar tasu za su yi zaben ne kawai kai tsaye ba tare da sun karkata wani bangare ba (ko ta yaya).

Su mutanen da suke sanin bugun zuciyar tasu ba a ko da yaushe suke nasara ba (cankar katin), idan suka tashi faduwa sun fi kowa haka kuma idan nasara ce tasu ta fi, amma dai abin da ake son sani a nan shi ne su wadannan sun fi bin abin da jikinsu ya nuna.

To al'marar za ta iya zama gaskiya kenan, cewa, mutanen da suke sanin yanayin da zuciyarsu take za su fi bin abin inda ransu ya karkata, ko mai kyau ne ko kuma akasin hakan ne.

Duka wannan ya sa Ibanez ya ke son sanin to me zai faru kenan idan a ce an sanya wa mutum wata zuciya taroba?

Idan har Carlos ya ji wani sauyi mai yawa, wannan zai nuna mana sabuwar shedar cewa zuciyarmu (tunani) ta wuce kwakwalwarmu.

Kuma wannan shi ne ainahin abin da ya gano. Lokacin da Carlos yake sauraron bugun zuciyarsa, misali na wannan na'ura ta cikinsa ya rika bi maimakon na ainahin zuciyarsa.

Wannan ya kuma sa sauya yadda yake daukar jikinsa, misali kamar ya dauka fadin kirjinsa ya karu, wannan ba shakka abu ne daman da za a yi tsammani.

Ta wani fannin ma sauya wurin zaman zuciyar tasa yana sa shi jin wani abu ko yanayi a jikinsa, ba kamar yadda a ce mutumin da aka sanya wa hannun roba ba.

Wannan sauyi ya shafi yadda yake jin tausayin mutane da kuma yanayin zamantakewarsa da sauran mutane.

Carlos ga alama ya daina jin tausayi idan ya ga hotunan mutanen da suka gamu da mummunan hadari.

Haka kuma ya samu matsalolin sanin dalilin da wasu suka aikata wani abuyanayin halin da wasu ke ciki da kuma yanke shawara, dukkanin wadannan na nuna yadda jiki ke da iko wajen samar da yanayin mutum (emotion).

Dunn ya ce wannan nazari ne mai ban sha'awa da kuma wuya.

''A LIFELESS SHELL''

Abin takaici, Carlos ya mutu sakamakon wasu matsaloli da suka taso a lokacin yi masa magani, amma Ibanez na fatan ci gaba da wannan bincike da sauran marassa lafiya.

A yanzu yana gwaji ne a jikin mutanen da ake aikin sauya musu zuciya gaba daya, domin ganin yadda za ta iya tasiri ga saninsu na aikin cikin jikinsu misali bugun zuciya.

Idan wasu jijiyoyin da suka tashi daga sashen kasan jikin, wanda ya hada da inda zuciya take, mutum zuwa kwakwalwa suka lalace, hakan zai datse aikewa da sako zuwa kwakwalwa wanda hakan zai shafi tunaninsa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Bayan wannan fanni da ya shafi sauyin zuciyar, masanin yana kuma duba ko wata matsala a tsakanin hanyar sadarwa tsakanin jiki da kwakwalwa zai iya sa mutum ya gamu da wasu matsaloli, kamar a ce maras lafiya ya rika jin cewa ba a cikin jikinsa yake rayuwa ba.

Wani maras lafiya da ke fama da irin wannan matsala ya ce, ''ji nake kamar ba ni da rai, kamar jikina ba shi da komai a ciki, tamkar kwanson da ba shi da rai,''

Maras lafiyar ya kara da cewa, '' Ji nake kamar ina tafiya a cikin duniyar da na sani amma ba na jinta.''

Ibanez ya gano cewa wadannan marassa lafiya suna nuna alamun matsala sosai, kuma hoton aikin kwakwalwarsu ya nuna, wannan ya faru ne sakamakon katsewar sadarwa zuwa sashen kwakwalwar da ke lura da sakonnin da suka shafi sanin yadda jikinka yake, da yanayin mutum da tausayin mutane da yanke shawara, da kuma sanin kai kanka.

Dakta Dunn wanda likitan tunanin dan adam ne, ya fi damuwa da alakarta da damuwa ko rashin kwarin gwiwa.

''A halin yanzu muna bin wasu hanyoyi na magani, inda muka sauya abin da maras lafiya yake tunani kuma muna da yakinin cewa nasara a kan dawo da yanayinsu kuma za ta biyo baya,'' ya ce. ''Amma kuma na gamu da cikas, inda marassa lafiyar suke cewa sun wadannan abubuwan a basirarsu, amma a yanayin jikinsu ba sa jinsu.''

Hatta bayan an horad da maras lafiya kan tunani mai kyau, duk da haka zai yi ta fama da yadda zai ji dadi (farin ciki).

Wannan kuwa matsala ce da Dunn yake ganin za ta faru ne saboda rashin kyakkyawan sanin yadda yanayin jiki yake, saboda rashin sako mai kyau daga sashen jiki na kasa zuwa kwakwalwa, kan abubuwan da suka shafi yanayin mutum da sauran abubuwa na jikinsa.

Ya bayar da misalin yadda idan kana kewayawa a wani wurin shakatawa, jikinka zai iya gaya maka duk wani bayani mai dadi da zai nuna hankalinka a kwance yake kana hutawa cikin kwanciyar hankali.

''Amma kuma wadanda suke fama da matsala ta damuwa ga alama suna kewayawa ne a wurin shakatawar ba tare da hankalinsu yana ma karkata ga abin da jikinsu ke ji ba,'' ya ce, ''Kuma daga nan sai su dawo su ce su kam ba su ji komai ba.''

Hakkin mallakar hoto spl

A jerin wadannan nazarce-nazarce, Dakta Furman ta gano cewa mutanen da ke fama da ciwon damuwa sosai ba tare da wasu matsaloli ba, su kan yi fama domin jin bugun zuciyarsu, kuma yawan rashin nasarar sanin bugun zuciyar zai sa su kasa bayar da wani bayani mai kyau ko mai dadi na rayuwarsu ta yau da kullum.

Kuma kamar yadda aikin Dunn a game da yanke hukunci zai nuna, mummunan yanayin sanin yadda jiki yake wato idan ba ka da ilimi ko sani mai kyau a kan sanin yadda jikinka yake, shi ma yana da alaka ga matsalar yanke hukunci.

Dakta Furman ta jaddada cewa za a iya samun matsaloli ko cutukan damuwa daban-daban., kuma rashin kyakkyawan sani na yanayin jiki ne zai iya haddasa wasunsu.

Ba a san ainahin abin da yake sa wasu mutaen suke da karancin sanin yadda jikinsu yake ba, amma Dakta Dunn na ganin abu ne da za a iya magancewa ta hanyar samun horo.

A yanzu yana duba yuwuwar amfani da wata hanya ta ba da horo kan sanin abu a zuciya, wanda zai sa mutum ya mayar da hankali kan abin da yake ji a jikinsa.

Ya ce kalubalen shi ne, ka yi kokari ka san jin abin ko da kuwa ba mai dadi ba ne, ba tare da ka mayar da martani na kai tsaye ba (cikin sauri ba tare da ka sani ba).

Daga nan ne za ka iya kokarin amfani da jikinka a matsayin ma'aunin yanayinka (emotion) domin ya gaya maka matsayin zuciyarka da kuma yanke hukunci kan abin da za ka yi a kai.

Wasu masanan kuma sun tsara wani gwaji ne na wasan kwamfuta, inda yake sa ka danna wani madanni bayan duk bugun zuciya hudu, kuma zai haska alamar jar wuta idan ba ka yi daidai ba, wanda hakan sako ne na cewa ka bunkasa sanin jikinka.

To yanzu me kake jira? Za ka iya morewa rayuwa ta yanayin jiki da kake so sosai, idan ka lakanci sanin yanayin jikinka , tare kuma da sanin yadda za ka rika yanke shawara mai kyau.

Abin da kawai za ka yi shi ne ka saurari bugun zuciyarka The mind-bending effects of feeling two hearts