Almara biyar da gaskiya game da jikinka

Hakkin mallakar hoto Science Photo Lab

Kama daga mutane masu siffar kalangu (X) zuwa ainahin asalin yadda wasu maza ke da nono irin na mata BBC ta yi bincike kan wasu daga cikin manyan abubuwan da aka yi musu gurguwar fahimta a jikin mutum.

Ga bayanin Linda Geddes

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Mutane masu teba suna da manyan kayan ciki wadanda ke bukatar karfi ko makamashi mai yawa su yi aiki

A jikin mutum, ainahin tsoka ko jijiyoyi suna dibar linki uku na karfin da kitse yake diba, amma kuma kwayoyin halittar sauran sassan jikin sun ma fi bukatar karfin.

Mutanen da suke da teba suna da kayan ciki da sauran halittun jiki manya da kuma kwayoyin halitta masu yawa domin tabbatar da ganin aikin jikin na gudana sosai, idan aka kwatanta da mutane masu siririn jiki.

Wannan na nufin jikin masu teba yana amfani da makamashi ko karfi da jikin yake da shi da yawa. Bayani daga mujallar kimiyyar abinci, Nutritional Sciences.

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption A da masana kimiyya sun dauka mutane masu manyan duwawu sun fi masu tumbi lafiya

Shin kana da siffar tuffa ne wato mai dirar zaki, wanda ke da girman jiki daga sama kasa kuma siriri ko siffar fiya (pear), kamar dalar gyada, wanda daga sama ba kiba amma daga katare zuwa duwawu da cinya yake da kauri?

A da gaba daya ana daukar mutanen da ke da dirar zaki ko siffar tuffa, wato masu kiba daga sama kasa kuma siriri, sun fi zama cikin hadarin ciwon zuciya da cutar sukari saboda maikon da yake gangar jikin tasu yana fitar da sinadaran da suke kara haddasa kumburi da kara yawan bugun jini kuma hakan ya haddasa yanayin da kwayoyin halittar jiki za su bijire wa sinadarin insulin wanda ke lura da sukarin da ke jikin mutum.

Sabanin hakan kuma maiko ko kitsen da yake tare a duwawunka aka ganin kusan ba shi da illa, amma kuma wani bincike na kwanan nan da aka yi a jami'ar California a Davis, ya nuna cewa wannan kitsen shi ma yana fitar da wadannan sinadarai masu cutarwa.

Ma'ana duk irin siffar jikinka idan kana da maiko ko kitse mai yawa matuka, to illa ce ga lafiyar mutum. Bayani daga Jami'ar California, Davis

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Siffar yawancin matan Biritaniya kenan; fadada

Ko da yake mata da yawa sun fi daukar kansu a matsayin masu siffar kalangu (hourglass or X-shaped),wato samansu da fadi tsakiya ba fadi kasansu ma da fadi, amma sakamakon da na'urar daukar hoton jikin mutum ta asibiti samfurin 3D ta bayyana ya nuna akasin hakan.

A lokacin da masu binciken da ke Manchester suka yi amfani da wadannan na'urori domin duba wasu matan Biritaniya 240, sun gano cewa kashi 63 cikin dari na matan suna da awo daya na fadin kirji da kugu da kuma kafada, sannan kugun nasu ba shi da girma. Wato kenan fadada ne kawai.

Kashi 13 cikin dari ne kawai suke da siffar kalangu, sauran (kashi takwas cikin dari) masu siffar dalar gyada ce ko fiya (pear), wato daga sama ba su da girma, amma kuma suna da fadi daga kugu zuwa kasa, masu siffar cokali ( siffar kalangu sosai) kashi bakwai, masu siffar zaki (V) wadanda daga kafada suke da fadi amma suke tsukewa zuwa kasa kashi shida ne, sannan kuma kashi uku kishiyar masu siffar zakin ne, wato daga kafada ba su da fadi zuwa kasa kuma suna kara fadi.

Haka kuma mata suna kara zama fadada yayin da suke girma ko kara shekaru, inda kashi 80 cikin dari da suka wuce shekara 56 suna cikin wannan rukuni. Binciken jami'ar Manchester ta Metropolitan

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Nonon mata da yake fitowa wasu maza,nono ne na sosai, da kwayar halittar mata ke sa ya fito

Ko da yake namijin da yake da nono kamar na mata za ka ga yana da tumbi da kuma malolo (a haba), to amma ba su kai malolo (saki) din da ake gani kamar sun kai ba.

A gaskiya ma a yawancin lokaci naman wurin nono ne yake jawo su.

Maza masu nauyi da ya yi yawa a wani lokaci suna samun wadannan abubuwa ne saboda kwayoyin halitta na kitse suna samar da kwayoyin halitta na mata (oestrogen), wadanda suke sa nono ya fito.

Kuma kasancewar kwayoyin halitta na namiji bisa ka'idar jiki (na namiji) za su hana wannan fitowa ta nono, yawan kwaoyin halittar na namiji na raguwa yayin da namiji yake kara shekaru. Bayani daga hukumar kula da lafiya ta Biritaniya.

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Maza masu jiki sun linka sirara uku wajen dadewa a saduwa da mata

Lokacin da masu bincike na kasar Turkiyya suka yi nazari a kan wasu maza 200, sun gano cewa wadanda suka fi jiki ko teba wadda take daidai da jikinsu (idan aka kwatanta da tsawonsu da nauyinsu) da kuma tumbi yawanci suna kaiwa tsawon minti bakwai da dakika uku a saduwa da mace.

Su kuwa mazan da suke sirara yawanci suna kaiwa minti biyu ne kawai a jima'in, sannan sun fi samun matsalar yin inzali da wurwuri.

Ana ganin dalilin watakila shi ne raguwar kwayoyin halitta na namiji, wadda ke da nasaba da teba mai yawa.

Sai dai duk da cewa maza masu girma za su iya fin dadewa a saduwa da mace, amma da farko zai iya kasancewa sai sun yi fama kafin su tashi mazakutarsu, domin nauyi da yawa yana da alaka da matsalar rashin tashin gaba. Bayani daga mujallar binciken rashin kwazon namiji International Journal of Impotence

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Five myths and truths about the body