Amfanin ilimin shatar shiga intanet

Hakkin mallakar hoto science photo library

A da mallakar kwamfuta na tafiya ne kafada da kafada da fahimtar ainahin yadda take aiki. Amma kuma hakan ga alama ya sauya, sai dai Tom Chatfield ya ce lokaci ya yi da za a koma 'yar gidan jiya.

Ga dalilinsa:

Akwai wani tsohon salon magana ko barkwanci da masu hada shirin kwamfuta ke yi a tsakaninsu wanda ke cewa, ''mutane iri goma ne kawai a duniyar nan, wadanda suka fahimci kashi biyu da wadanda ba su sani ba.''

Wannan ba abu ne da zai ba kowa dariya ba amma dai ya yi ma'ana. Abin kuwa shi ne, a yanzu muna duniya ce da ta rabu gida biyu, tsakanin wadanda suka san yadda kwamfuta take aiki a can cikinta da kuma wadanda ba su da wannan sanin.

Wannan ba abu ne da kawai muna tashi muka ga ya faru ba dare daya, abu ne da yake tattare da kalubale ko illa a rayuwarmu a gaba.

Idan aka duba shekara da shekaru na baya na farkon fitowar kwamfuta, idan aka ce wannan mutumin mai kutse ne a intanet ko kwamfuta abin alfahari ne maimakon takaici.

A da din, hakan na nufin kai kwararre ne da za ka iya kutse a cikin mukulli ko tsarin tsaron kwamfuta ka wargaza shi, ko ka sauya yadda yake aiki, ta yadda zai rika yin wasu sabbin abubuwa, ko kuma ma ka hana kwamfutar yin wani abu da ba daidai ba ne.

Kai wani ne da za ka iya ganin hatta cikin hanjin kwamfutar watakila ma ka kuma bunkasa yadda take aiki fiye da yadda aka yi ta.

A farkon shekarun 1970, Steve Jobs da abokin kafa kamfaninsu na Apple, Steve Wozniak, sun gano yadda za a iya kutse a hanyoyin wayar tarho na Amurka, ta yadda hatta ma wayar tarhon Paparoma ma za a iya kiranta a yi masana maganganun da aka ga dama ba tare da ansan wanda ya yi ba.

Wannan wani abu ne na batanci idan aka duba cigaban lokacin, wanda kuma alama ce da ke nuna cewa, kwararrun 'yan dagaji sun fa fara sanin hanyoyin barazana da kai hari kan manyan kwamfutoci na hukuma ko gwamnatoci.

Kamar yadda za ka yi tsammani tun daga wannan lokaci na shekarun na 1970, aka gyara tsaron hanyoyin wayar tarhon Amurkan, aka inganta tsaronsu ta yadda zai yi wuya a iya yi musu kutse.

Haka kuma aka kara samun gibin ilimin da ke akwai tsakanin wadanda suke amfani da kwamfuta da wadanda suke tsara aikin kwamfutoci, domin an kara tsaurara yadda manhajoji da kuma na'urorin kwamfutoci suke.

Yadda suka fara aiki a matsayin kamfanonin kwamfuta na gida na 'yan dagaji ko na yi da kanka, kamfanoni irin su Apple, sun zamo asali ko jagaba na samar da kwarewa ga masu amfani da kwamfuta cikin sauki.

Sun samar da manhajoji wadanda ba sa bukatar wasu madannai (keyboard) ko masarrafa (mouse) ta kwamfuta, ballantana ma a yi maganar wai sai ka san yadda fasahar kwamfutar ke aiki.

Zamanin sirrintawa

Wannan cigaban fasaha da aka samu wanda ya shiga rayuwarmu ko ya zama jiki a wurinmu ya kara sanya mu a duniyar da ke cigaba da rabuwa gida biyu.

Fasahar sadarwa, harka ce ta dimbin dubban miliyoyin dala a duniya, inda tarin kwararrun ma'aikata suke samar da kayayyakinta, wadanda muke amfani da su, kusan a kowane fanni, yau da kullum.

Sai dai kuma yawancin mu mutanen da muke amfani da wadannan abubuwa na fasaha fahimtarmu tare da lakantar yadda suke aiki (a can cikinsu) ta ragu sosai.

Wannan ba yanayi ba ne da zai iya sauyawa a dare daya ba, amma duk da haka akwai kungiyoyin da ke fafutukar kawar da wannan gibi.

A shekara ta 2014 ne wani asusu a Biritaniya ya kaddamar da wata 'yar karamar kwamfuta mai suna Raspberry Pi da yake sayarwa a kan fam 16 domin amfanin yara 'yan makaranta.

Ba kamar kwamfutarka ta tafi-da-gidanka (laptop) ko kuma 'yar kwamfutar hannu (tablet) ba wadda ko ina take a rufe ba, wannan 'yar mitsitsiyar kwamfuta mai girman kamar katin dibar kudi na banki (ATM), wadda hanyoyin wayoyinta suke kusan a fili, ta yi kama da kwamfutar farko (DIY), wadda irin su Steve Jobs da Wozniak suka kirkiro, kuma suke wasa da ita a lokacin farko na kirkiro kwamfuta.

Ita wannan 'yar kwamfuta tana bukatar a rika kokarin hargiza mata aiki ne ko hatsabibanci da ita ko kuma yi mata kutse, kuma wannan shi ne burin wadanda suka kirkiro ta (a koyi hatsabibanci da kwamfuta).

Ta haka tana karfafa wa mutane gwiwa su kara fahimtar yadda na'urar kwamfuta da sauran kayayyakin fasahar da ke hannunsu, suke aiki a can cikinsu.

A tsakanin kasashen duniya, wata karamar kungiya da ake kira Code Academy, ta kuduri aniyar kara wayarwa da mutane kai kan fahimtar yadda ake yin mabudin sirrin fasahohin na'urorin kwamfuta da mutane suke amfani da su.

Da mutane kusan rabin miliyan da suka yi rajista a farkon watanninta na farko da aiki a shekara ta 2011, kungiyar (Code Academy), wadda ke da aniyar koya wa duk mutumin da yake son lakantar sirrin mukullin fasahar ayyukan kwamfuta a kyauta, tana bunkasa sosai.

Abin da ta ba wa fifiko da farko shi ne koyar da harshen da intanet ke amfani da shi wato JavaScript, kuma ta gayyaci mutane a shekarar 2012 su tura mata email dinsu domin kammala darasi daya na sirrin na intanet kowace Litinin.

A fannin kwararru, abu ne mai sauki ka ga abin da ya sa ake bukatar ka lakanci yadda shi kansa aikin can cikin kwamfutar yake da muhimmanci.

Domin ayyuka da dama a yau suna bukatar karin kwarewa kan yadda ita kanta kwamfutar take aiki, ba wai sarrafa ta kawai ba.

Kuma duk daliban da suke da wannan ilimi suna da babbar dama a rayuwarsu a gaba.

To amma ganin cewa wasu 'yan kalilan ne daga cikin mutanen da suke yin rijista domin koyon fasahar sirrin kutse a intanet a kyauta, za su iya koyon wani dan abu daga cikin ilimin, anya kungiyoyi irin su Code Academy za su iya cimma abin da suke buri?

Ina ganin amsar wannan tambaya ita ce e! Domin koyon yadda ake sirranta aikin intanet ba kawai yana nufin kawai mutum ya iya shiga ko kutse ko gyara hada wani shiri ba ne.

A'a, abu ne da ya hada da koyon yadda za ka yi tunani a kan duniya ta wata hanya daban, domin akwai jerin matsaloli wadanda ke matukar bukatar kwararrun hanyoyi da dabaru na shawo kansu.

Kuma duk da cewa samun wannan ingantaccen ilimi da kwarewa a wannan fanni abu ne da kila zai zama mai wuyar samu, to amma ka ma koyi yin tunani kamar wanda yake neman kirkirar sirrin magance wata matsalar fasaha, zai iya nufin gane kuskuren hanya da tsarin da wani kwararren ya dauka kan wata fasaha, ko ma ka gane cewa dabarar da wannan mutumin ya dauka ba wadda za ta yi ba ce sam-sam.

Kamar lokacin da Neo ya fara bayyana abubuwan da ya fahimta a fim din Matrix na farko, koyon gano dabarun yadda fasahohin kayan da kake amfani da su suke, na nufin ka gane cewa abin da kake gane ba wani siddabaru ba ne na duniya da zai gagara a bude shi ba.

Kawai wani abu ne da wani ya yi amfani da tunaninsa ya tsara.

Kuma wannan shi ne bambancin da aka damu da shi fiye da duk wani bambanci tsakanin masu hada wannan siddabarun fasaha, wato wadanda suka kirkiro ta, da kuma wadanda ba su ne suka hada ta ba ( masu amfani da kayan fasahar kawai).

Ma'ana ka gane cewa na'urar da kake amfani da ita, na'ura ce kawai wadda kai ma za ka iya sauya yadda take aiki, ko ma ka yi kaca-kaca da tsarin fasahar da take amfani da ita, ka kawo wadda ta fi ta.

Kuma ko da a aikace ba za ka iya yin hakan ba (amma a tunaninka za ka iya kalubalantar tsarin), watakila wani zai iya yin hakan ko ma tuni har ma ya yi.

Wannan bayanin na karshe, wato damar iya amfani da kwarewar wasu da kuma sanin yadda za ka fara neman hakan, abu ne mai muhimmanci sosai.

Daga kamfanoni ko kungiyoyi marassa gaskiya zuwa masu aika wa da wasiku na karya, akwai mutane da dama da ba abin da suke kauna kamar su ga sun samu kwarewa a fasahar zamani ta intanet da mummunar niyyar sanin abin da yake a boye.

Yin tunani daban ba ya bukatar kwarewa wajen iya hada sirrin intanet ko fasaha.

Abin kawai da yake bukata shi ne, ka san cewa hatta manyan abubuwa ko ayyukan fasahar zamani suna da iyakarsu, kuma sun kunshi tunanin wasu mutane ne.

Sannan kuma abu ne da zai yiwu a sanya matakan tsaro ko sirrinta hanyoyin bude wasu fasahohin masu wuya su ma.

Misali a shekara ta 2010 wani bincike na hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, ya gano wata manhaja a wasu kwamfutoci na tafi-da-gidanka da aka ba wa daliban wata makaranta a Philadelphia, inda za a rika leken asiri ta na'urar daukar hoto da ke jikin kwamfutocin da kuma hanyar intanet din da suke amfani da ita.

Idan ba don aikin kwararrun masu bincike ba, da ba wanda zai gano wannan manhaja.

Kuma tun da aka gano wannan shirin kurar da ya tayar da muhawarar da aka yi ta yi a kai, suka sa aka dauki tsauraran matakan tsaro na kare aukuwar hakan a gaba.

Shirin Code Academy da ire-irensu ba su da wata hanya ta daban da za su iya sama wa mutane ko wata hanya ta fahimtar da mutane wannan ilimi a take.

Ko da yake ga yawancin mutane, shiga wannan shiri mataki ne na farko ko ba komai, na yin tambaya mai muhimmanci a kan duniyar da suke shiga ta intanet, kuma bincike ne mai 'yar wuya na dan wani dogon lokaci domin samun amsar da ta fi dacewa a cikinta.

Idan kuma har yanzu kana mamaki, to ka sani fa goma ita ce tsarar biyu a tsarin lissafin 'yan biyu. Ko kuma a wata sigar ka san biyar biyu fa ba ta goma.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Computer programming: Why we should all learn to hack