Yadda ba za ka kara manta sunan wani ba

Hakkin mallakar hoto Getty

Manta sunaye na daya daga cikin matsalar kwakwalwarmu, to amma akwai hanyoyin da za ka haddace su in ji m asanin tunanin dan adam Tom Stafford.

Wani ma'abocin karanta irin wadannan labarai na BBC, mai suna Dan ya yi tambaya cewa, ''Me ya sa muke manta sunayen mutane idan muka hadu da su da farko?

Ina iya tuna duk wasu bayanai game da mutum amma kuma in manta sunansa gaba daya.

Ko da kuwa bayan doguwar hira ko tattaunawa ne. Ba shakka wannan abin kunya ne matuka.''

Wannan amsa ta shafi koyon wani abu mai muhimmanci game da yadda kwakwalwa ke tuna abu.

Haka kuma za ta nuna maka hanyar da za ta taimaka maka ka kauce wa, abin kunya na yadda bayan ka yi kusan sa'a daya kana hira da mutum, a karshe sai ka nemi sunansa ka rasa. Ka manta.

Ta yadda za ka san yadda haka ke faruwa sai ka fahimci cewa, kwakwalwarmu ba wuri ne na musamman na adana abubuwa ba.

Kamar a ce wuri ne da ake da jakunkuna daban-daban na kowane bayani, da kuma wata jaka mai launi mai haske wadda aka yi mata alama da cewa wannan ta sunaye ce ba.

Maimakon haka kwakwalwarmu an yi ta ne ta yadda ta ke kulla alaka tsakanin bayanai daban-daban. Wannan ne ma ya sa mukan shiga dogon tunani wani lokaci:

Misali ka lura cewa littafin da kake karantawa an buga shi ne a Paris, kuma a Paris hasumiyar Eiffel Tower take, inda 'yar uwarka Mary ta ziyarta a bazarar bara, kuma Mary tana sha'awar askirim din Pistachio (wani dan ita ce kamar kashu).

Sai ka ce, ko ta sha askirim din na Pistachio a lokacin da ta hau hasumiyar ta Eiffel?

Haka za ka yi ta harhada bayanai kowanne ka danganta shi da wani ba da wata dabara ba.

Kawai yadda abubuwan suke dacewa da lokacin faruwar kowanne da wurin, da yadda ka samu bayanin da kuma abin da bayanin yake nufi gare ka.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Muna barin sunaye suna yawo ne a kwakwalwarmu kamar jirgin ruwan da yake watangaririya a teku

Irin wannan alaka ta jerin bayanai na nufin za ka iya tunanin tambayar da za a iya yi daga amsar.

Amsar : ''Hasumiyar Eiffel?'' Tambaya: ''Fitaccen abu a Paris.'' To wannan shi zai sa hadda ta zama mai amfani domin ta ko ina aka bullo maka za ka iya bayar da bayani.

Tambaya kamar, ''menene a cikin akwatin nan ta sama?'' ba wata tambaya ce mai muhimmanci ko sha'awa ba, amma za ta kasance hakan a lokacin da kake son ka ji amsar ''ina mukullayena suke?''.

Saboda haka hadda ana gina ta ne kamar haka a bisa dalili, kuma yanzu za mu iya ganin dalilin da ya sa muke manta sunaye.

Haddarmu tana da ban mamaki, amma kuma tana tasiri ne bisa yawan alakar da muka kulla da wani sabon bayani, amma ba wai bisa yadda muke matukar bukatar mu tuna da abu ba.

Lokacin da ka hadu da wani mutum a karon farko, ka kan san sunansa, amma a wurin kwakwalwarka wannan wani dan bayani ne kawai wanda ba shi da alaka da wani abu da ka sani, kuma ba shi da alaka da duk wani abu kuma da ka sani a gaba game da mutumin.

Bayan hirarka da mutumin, inda watakila ka san aikinsa da abubuwan da yake sha'awa da iyalansa ko wani abu, dukkanin wadannan bayanai sun hade a kwakwalwarka.

Ka dauka kamar kana magana da wani mutum wanda ya sa shudiyar riga, wanda yake sha'awar kamun kifi, kuma aikinsa shi ne sayar da motoci, amma kuma ya gwammace ya daina wannan sana'a domin ya koma sayar da kayan su.

To yanzu idan za ka tuna da magana ko bayani daya (sayar da motoci) za ka iya bin wannan bayanin har ya kai ka zuwa sauran bayanan (sayar da motoci amma kuma yana son ya daina, da yana son ya daina domin ya koma sayar da kayan su da yana son kamun kifi da sauransu).

To matsalar a nan ita ce sunan wannan sabon abokin naka ya bata, ko ba a waiwaye shi ba, saboda dan bayani ne kawai wanda ba ka danganta shi da komai ba na zancenku.

Kuma an dace akwai hanyoyin da za ka karfafa wadannan bayanai ta hanyar sarkafa su da juna.

To ga yadda za ka tuna sunan ta hanyar amfani da wasu kai'doji na hadda ko tuna abu.

Da farko ka maimaita duk sunan da aka gaya maka. Daya daga cikin muhimman ka'idoji ko hanyoyin koyon abu shi ne jarrabawa akai-akai.

Yawan jarrabawarka shi zai sa ka fi haddace abu da kyau, yadda za ka fi saurin tuna shi.

Kari a kan wannan, idan ka yi amfani da sunan mutum, kana alakanta shi ne da kai kanka, a lokacin da kake furta shi, kuma kana alakanta shi da maganar da muke yi a kwakwalwarka, (misali ka ce, ''To James wai me kake gani ne a sana'ar kamun kifi har take ba ka sha'awa sosai?'').

Na biyu kuma shi ne, ka yi kokari ka danganta sunan da ka ji yanzun nan da wani abu wanda daman ka san shi. Ba damuwa ko alakar shirme ce, abin da kawai ake bukata shi ne ka samu wani abu da za ka danganta sunan da shi da zai sa ya zauna a kwakwalwarka.

Misali, watakila sunan wannan mutum shi ne James, kuma sunan abokinka na babbar makaranta shi ma James, kuma ko da yake shi wannan mutumin yana sanye ne da shudiyar riga, abokinka na makarantar shi ba ka taba ganin ya sa shudiyar riga ba sai baka, saboda haka ba zai sa shudiya ba.

Ko da yake za ka ga wannan kulle-kullen kusan shirme ne kawai ko soki-burutsu, amma duk da haka za su iya taimakonka ka tuna.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kana son ka daina kunyata kanka? Ka yi kokari ka danganta sunan da duk wani abu da ka sani game da mutumin, ko da shirme ne, ba za ka manta ba

A karshe kana bukatar ka danganta sunan mutumin da wani abu da ya shafe shi.

Idan ni ne zan kama abu na farko ne kawai da ya zo min a zuciya na danganta sunan da wani abu da na fahimta game da mutumin.

Misali, James suna ne a cikin Baibul (Linjila), kuma bayan wannan ma, ga Baibula na sabon alkawari da ake kira ''King James'', kuma sunan James ya fara ne da harafin J, kamar dai sunan Jonah (Yunus) na cikin Baibul, wanda kifi ya hadiye, sannan kuma shi wannan James din ga shi yana sha'awar su, to amma dai na san cewa ya fi son ya kama kifi ba kifi ya kama shi ba.

Ba wata damuwa idan alakar da ka kulla tsakaninsu tana da ma'ana ko babu. Ba abu ne da za ka gaya wa wani ba.

Kila ma zai fi idan ba ka gaya wa kowa ba, musamman ma sabon abokin naka.

Amma dai alakar da kake kullawa tsakani za ta taimaka wajen dasa sunan a kwakwalwarka, kuma wannan dangantaka za ta taimaka maka ka tuna sunan idan bukatar gaya wa wani shi ta taso.

Kuma idan kana shakku, to gwada wannan 'yar jarrabawar ta sauri.

Na fadi suna ye uku a cikin wannan bayanin. Na san dai za ka tuna James, wanda ba shi ne Jonah ba.

Haka kuma watakila za ka iya tuna 'yar uwarka Mary ( ko kuma akalla irin askirin din da take so).

To amma za ka iya tuna sunan mai karanta kasidun namu, wanda ya aiko da tambayar da ta jawo wannan bayani?

Shi kadai ne na gabatar ba tare da na bayyana wata dangantaka ta sosai da sunan ba, kuma wannan shi ya sa nake ganin shi kadai ne sunan da ka manta.

Idan kana da wata tambaya da ta shafi wani al'amari na tunani ko halayyar dan adam da kake son ganin an yi bayani a kai a wannan shafi, ka tuntubi wannan adireshi (a harshen Ingilishi) @tomstafford a shafin Twitter ko ideas@idiolect.org.uk.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Never have the embarrassment of forgetting a name again