Ko ka san abin da ke cikin dalar Masar?

Yadda suke da dakuna da lunguna da sako da ramuka cikin rami har yanzu ba a san dukkan abubuwan da ke cikin dala-dalar Masar ba- me ya sa abin yake haka?

Chris Baraniuk ya yi mana nazarin yadda abin yake

''Na yi gam-da-katar na gano wani abin mamaki a kwari, wani kabari ne mai ban sha'awa da yake rufe, ba abin da ya taba shi, wanda na gano domin yi maka maraba,'' wannan rubutun da Howard Carter kenan ya yi a gurguje na sakon karfafa wa George Herbert gwiwa domin ya biyo shi yawan bude idanun binciken abubuwa da yake yi.

Wannan a shekara ta 1922 kenan a daidai lokacin da Carter ya yi gamo-da-katar na gano wata kyakkyawar kushewa da aka adana ta sarkin Masar Tutankhamun.

Gano wannan kushewa ta sarki Tutankhamun ke da wuya sai kawai labarin ya dauki hankalin duniya.

Duk da cewa shi wannan sarki ba an birne shi ba ne a wata daga cikin dalar kasar ta Masar, amma sanin cewa wasu sarakunan kasar an birne su ne a wuraren, ya sa mutane da yawa suke tunanin irin abubuwan mamaki da za a iya ganowa a cikin ramukan da ke cikin wadannan dala-dala masu muhimmanci.

Duk da cewa wadannan dala-dala sun yi daruruwan shekaru a hamada, har yanzu ba mu san takamaimai mafi yawan abubuwan da ke can cikinsu ba.

A kwanan nan dan takarar shugabancin Amurka Ben Carson ya yi bayani kan abin da yake gani na cikin dala-dalar, inda ya ce kawai ana amfani da su ne a zamanin da domin adana hatsi, abin da ya ba wa kafafen yada labaran Amurka matukar mamaki.

To wai shin me ya sa har yanzu almara da labaran kanzon kurege da shaci-fadin da ake yi a kan wadannan dala-dala ke ci gaba har zuwa yanzun nan da muke wannan magana? Kuma me ya sa ba mu yi bincike a kan su ba sosai har yanzu?

Image caption Dala-dalar suna da muhimmancin da duk wani tunani na fasa su a shiga domin ganin abin da ke cikin dakuna da lungunan cikinsu za a dauka abu ne na rashin sanin ya kamata

Wani abu dai shi ne, su wadannan dala-dala gini ne na tarihi na ban mamaki masu amfani. Suna da matukar muhimmanci, daga irin tsarin gininsu da zane-zanen ado da ke jikinsu da kuma kayan tarihi da ake ganowa a cikinsu, wanda kuma duk wani yunkuri na fasa su a shiga ramukan da ke can cikinsu zai zama kamar abu ne da bai dace ba kuma na rashin sanin ya kamata.

Hanyoyin zamani na aikin bincike da nazarin kayan tarihi suna ''tabbatar da cewa ba a yi illa ga kayan tarihin da muke kokarin fahimta ba'', kamar yadda Alice Stevenson ta sashen kayan tarihi na Masar a kwalejin jami'ar Landan ta bayyana.

Misali wata kungiyar sa-kai mai suna CyArk, a kwanan nan ta fara amfani da hanyoyi na zamani wajen adana wuraren kayan tarihi sama da 500, kama daga kofar nan ta Berlin a Jamus, Brandenburg Gate zuwa ginin nan na jan bulo na ban mamaki, Ziggurat da ke birnin Ur a Nasiriyah a Iraki.

Fasaharsu za ta dauki hoton wuraren na nau'in taswirar 3D, wato samar da makamancin wannan wuri na zahiri ba tare da ko da taba shi da hannu ba.

Stevenson ta soki maganar cewa manya-manyan wurare ne kawai na adana kayan abinci a zamanin da.

Ta ce, '' a gaskiya masu binciken kayan tarihi na karkashin kasa suna gano rumbunan kayan abinci a Masar abubuwa ne da muka sansu sosai, ba su yi kama da dala ba''. Su ma hukumomin Masar a kwanan nan sun soki ra'ayin na Mista Carson.

Amma duk da haka wannan magana ko tambaya tana nan, ta cewa me muka sani game da abin da ke ciki cikin tarin dalar Masar?

Dauki misali ita kanta babbar dalar ta Masar da ke Giza, wadda aka gina sama da shekaru 3,000 da suka wuce da bulon dutse sama da miliyan biyu, a yau tsawonta ya kai mita 139 (kafa 450), ko da yake tsawon zai dan fi haka a lokacin da aka gina ta.

Wannan ba karamin katafaren gini ba ne. Amma kuma 'yan wasu kadan daga cikin dakunan da ke cikinta muka iya shiga, kamar babban wurin ajiyar kayanta da kuma sashen sarki da na sarauniya.

A kwanan nan wasu masana aikin tsara gine-gine da masana kimiyya sun yi amfani da wata na'ura inda suka gano bambancin yanayi na sanyi da zafi da ba su yi tsammani ba a dutsunan babbar dalar.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hoton alamar zafin da wasu tubalan dalar Masar ke yi

Wannan watakila ya sake tayar da wasu tambayoyin maimakon amsoshi a game da dalar.

Domin a ji dumi a jikin wasu duwatsun a lokacin da rana take fitowa da kuma faduwa za ta iya kasancewa alama ce ta ramuka ko hanyoyin karkashin kasa inda iska ke shiga.

Sai dai ba hanyar da za a iya tantance hakan cikin sauki, domin an yi wa masana kimiyyar da suka gano hakan gargadi mai tsanani kan kada su sake su yi wani rami ko haka.

To amma koma ya lamarin yake, rahoton hukumar kula da harkokin kasa ta Amurka (National Geographic), ya ce hukumomin Masar sun nuna aniyarsu ta bayar da goyon baya ga wani tsari na kasuwanci, inda za a ba wa masu yawan bude idanu damar shiga duk wani daki ko kogo da za a iya ganowa.

Wannan abu ne da za a tsara cikin natsuwa da hankali, amma Stevenson ta fahimci dalilin da watakila ya sa hukumomin na Masar suke da sha'awa a kan shirin.

Ta ce, ''ina ganin abu ne mai muhimmanci ga harkar yawon bude idanu ta Masar,'' inda ta kara da cewa, ''kuma ina jin suna son su yi amfani da yawancin damar da ke tattare da hakan ne, su nuna abubuwan ban mamaki na zamanin da.''

Ga alama na'urorin fasahar daukar hoto da sansano cikin abubuwa su ne manyan kayan aikin da masu binciken dala-dalar za su yi amfani da su a shekarun da ke tafe.

Zuzzurfan nazarin hotunan da aka dauka da tauraron dan adam ya taimaka wajen gano wasu dala-dalar da ke binne a kasa.

Saboda haka akwai misalai da yawa a yanzu kan yadda irin wadannan fasahohi na zamani za su iya bunkasa fahimtarmu ta wadannan manyan abubuwan ban mamaki.

Haka kuma mutum-mutumi na inji (robot) ma zai iya taimaka mana, domin shekaru hudu da suka wuce ta hanyar amfani da na'urori, an samu damar shiga wani kogo ko rami da mutane ba za su iya shiga ba, a cikin babbar dalar.

Wani dan zirin rami ko hanya ce mai ban mamaki, wadda ta tashi daga sashen dakin sarauniya zuwa wani wuri da aka rufe.

Tun a shekara ta 2002 aka gano wurin, lokacin da aka yi amfani da mutum-mutumi mai inji aka huda wata aba mai kama da kofar daki ta dutse aka dauki hoton abin da yake bayanta. Sai dai hotunan ba su nuna wasu bayanai masu yawa ba.

A shekara ta 2011 ne sai kuma aka yi amfani da wasu na'urorin wadanda suka fi kurdawa ciki-ciki aka tura su cikin dakin inda suka dauko hoton wasu zane-zane jajaye masu ban mamaki da sarkakiya, wadanda idanuwan mutum bai gansu ba a shekaru dubbai.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tarin kwararru masu bincike suna jira a wurin dalar Masar da ke Giza

Hatta wannan binciken da aka yi da kwararrun na'urorin zamani dan bayani kadan ko kuma a ce dan dandano kawai suka bayar na tarin abubuwan da ke cikin wannan daki na babbar dalar, wanda ba a san da shi ba ko aka manta da shi dimbin shekaru.

Har sai lokacin da shedun kimiyya suka wayar mana da kai, za mu cigaba da kasancewa cikin duhun jahilici a kan abubuwan da ke ciki ko kuma wadanda babu a cikin sauran dakunan dala-dalar na Masar.

A wurin Stevenson wannan shauki na neman sanin abin da ke boye kuma mai wuyar fahimta abu ne da muke tare shi tsawon lokaci.

Hasali ma wani bangare ne na dangantakarmu da dala-dalar a shekaru daruruwa.

''Sun kasance abubuwan ban mamaki a daruruwan shekaru,'' ta ce. ''Ina ganin yadda manyan abubuwan tarihi daman suke kenan, su ratsa zamani da yawa''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why do we still not know what's inside the pyramids?